Ticker

6/recent/ticker-posts

Turken Tauhidi a Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Turken Tauhidi a Waƙoƙin Amali Sububu

Tauhidi kalma ce ta Larabci da ke nufin kaɗaita Allah[1], A taƙaice tauhidi shi ne tabbatar da cewar babu abin da ya cancanta da bauta sai Allah. kamar yadda Abi Abdurrahman bn Muhammad bn Rislam ya yi bayani a cikin littafinsa mai suna ‘La’ilaha illallah’ Ma’anaha Shuruɗiha Nawaƙibuha Fabluha cewa:

“Tauhidi shi ne ƙuduri da kuma faɗar cewa

Lallai ba bu wanda ya cancanci a bauta masa

sai Allah, da kuma lizimtar hakan tare kuma

da aiki da shi.

 

Haka ma a Muhammad bn Abdulwahab a cikin Littafinsa  Usulus Salasa Wa’adatiha ya kawo ma’anar tauhidi inda yake cewa:  

Tauhidi shi ne tabbatar da cewa ba

wanda ya cancanta a bauta masa bauta ta

gaskiya sai Allah (SWT) Shi kaɗai.

(Muhammad bn abdulwahab: babu shekarar bugawa)

 

Shi kuwa Imamu Ɗahawi a Littafinsa mai suna Al-aƙidatu Ɗahawiya ya yi bayanin tauhidi da cewa:  

Lallai Allah ɗaya ne baya da abokin    

Tarayya. (Ɗahawi: babu shekarar bugawa)

 

Har wa yau Shaikhul Islam Muhammad bn abdulwahab a Littafinsa mai suna ‘Tafsiru Kalimatut Tauhid ya ce:   

Tauhidi shi ne haƙiƙanin tabbatar

da cewa babu wanda ya cancaci a

yi wa ibada sai Allah.

(Muhammad bn abdulwahab: babu shekarar bugawa)

 

Don haka ya  kasa tauhidi kashi uku kamar haka:

Tauhidir Uluhiyya,

Tauhidir rububiyya,

Tauhidi asma’u wa siffa.:

 

Manazarta waƙa kan yi ƙoƙarin fito da abubuwan da suka shafi tauhidi a cikin waƙoƙin da mawaƙa suka yi. Ga misalan wasu wurare da Amali ya kawo wannan turken kamar haka:

 Jagora : Allah ubana,

  : Ubangijina,

  : Uban giji,

: Wanda adda sheɗa[2],

  : Yana gani,

: Ba da ijjiya[3] ba,

  : Shi ne ka ji,

: Ba da kunnuwa ba,

  : Sarkin da ba,

: A kiɗa ma ganga,

  : Sarkin da ba,

: A kiɗa ma kotso,

  : Sarkin da ba,

: A kiɗa ma goge,

  : Sarkin da ba,

: A ganin naɗinai,

  : Sarkin da ba,

: A ganin hitonai,

  : Sarkin da ba,

: A gani da riga,

  : Sarkin da ba,

: A gani da wando,

  : Balle agogo da sa tubarau[4],

  : Ikonka shi,

: Ne abin ruhwanka,

  : In ya yi hannu,

: Yana ƙahwahu,

  : In ya yi hwarutta[5],

: Yana yin akaihu[6],

  : In ya yi hanci,

: Yana idanu,

  : In ya yi hal...,

: She yana haƙora,

  : In banda shi,

: Wa ka yin hakan ga?

’Y/Amshi : Mu san da Allah,

: Mu gyara gobenmu,

  : Kam mu saɓa ma lahirarmu,

  : Ya biya,

: Mai kuɗin manoma,

  : Mu kai dumanmu gidan Nadada.

(Amali  Sububu: Nadada)

 

A wannan ɗan waƙar Amali Sububu ya bayyana sunayen Allah Maɗaukakin sarki da sifofinSa, waɗansu ayyuka waɗanda babu mai iya yin su sai Allah duka sun bayyana a wannan ɗan waƙar. Sifofin Allah kamar ji ba da kunnuwa ba, ko gani ba da ido ba, da halitta mutum da sauran abubuwan halitta tare da suranta su yadda yake so,  daga ƙarshe Amali ya nuna cewa bayan Allah babu mai iya yin waɗannan abubuwa.



[1]  Kamar yadda mai littafin mai suna ‘Tauhidi Li-Safil Suwal As Thani’     shafi na 46  ya yi bayani.

[2]  Numfashi.

[3]  Ido.

[4]  Gilashin Ido.

[5]  Yatsun hannuwa da ƙafafuwa.

[6]  Farce.

Post a Comment

0 Comments