Manyan Turaku A Wakokin Amali Sububu

    Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Manyan Turaku A Waƙoƙin Amali Sububu

    Babban turke shi ne abin da mawaƙi ko marubuci ya sa gaba gadan- gadan domin ya faɗe shi a gane shi sosai[1].

    Galibi[2] shi babban turke mawaƙi ko marubuci ya kan faɗa a cikin waƙarsa ko kuma tun a sunan waƙar ya zan yana tafiya da saƙon wannan waƙar, idan kuma mawaƙi ko marubuci bai faɗa a waƙarsa ba,  kuma ba a gane a sunan waƙar ba, to sai mai nazari ya yi ƙoƙarin yin anfani da kalmomin fannu da aka gina waƙar da su waɗanda za ka samu ƙananan turakun.

     

    Turken Roƙo a Waƙoƙin Amali Sububu

    Roƙo shi ne neman wani abu daga wani mutum domin biyan bukata. Roƙo a cikin waƙoƙin baka na Hausa ya kasu gida biyu ne: akwai roƙo na kaitsaye, akwai kuma na kaikaice. Maroƙi shi ne wanda aikinsa shi ne roƙo, wanda yaki aiwatar da wannan harkarsa a wurare daban-daban a ƙasar Hausa. Hausawa suna kiransa da sunaye daban-daban ko da a ce masa Maroƙi ko Sanƙira ko Ɗan ma’abba ko Roƙo. Haka kuma Arawa suna kiransa Zakara. Maroƙi mutum ne wanda bai jin nauyin roƙo ko’ina ya je, ko ya samu ko kar ya samu.

    Amali Sububu yakan sa roƙo a cikin ɗiyan waƙoƙinsa kuma yana matsayin babban turke a cikin waƙoƙinsa kamar haka:

      Jagora   : Sarkin noman Garin Magaji,

       ’Y/Amshi : Kai muka dubi kamar,

           : Watan sallah[3]in ya hito,

         : Da hanzarin[4]noma nis san ka,

         : Taho gida rana ta hwaɗi,

         : Mu gaida Kartau mai gulbin hura,

              (Amali  Sububu: Sarkin Noman B/Magaji)

    Roƙo ne Amali ya yi a kaikaice a lokacin da yake furta cewa sarkin noman garin magaji kawai suke dubin don su ga yadda zai yi masu kamar dai yadda suke dubin watan sallah a lokacin da ake tsammanin fitowarsa.

       A wata waƙar kuma ya sa roƙon kamar haka:

     

      Jagora : Yanzu kam Mamman,

       : Sai ka hausan[5]ga doki,

       : Wanda  za ni gwada[6] wa,

       : Gida can ga dangi,

       : In yi mai turke[7],

       : Masu sona su duba,

       : Gashi dai nauna ba,

       : Giri babu mashi,

       : Ko na hwan huɗu ne.

        ‘Y/Amshi   : Noma na so ka bani,

       : Ka yi sunan noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Maigidan[8] Nasara,

       : Ɗan da yat tara damma,

        (Amali  Sububu: Maigidan Nasara)

     

    A waɗannan ɗiyan waƙar Amali yana roƙon doki ne daga wanda yake yi wa waƙar, a cikinsu ne ya nuna sha’awarsa da a ba shi kyautar dokin wanda yake son ya kai shi gida don danginsa su ga irin kyautar da aka yi masa. Ya kuma nuna cewa babu matsawa ga sayen dokin ko da zuwa ranar Talata ne wato ranar da kasuwar Mafara ke ci, don a cewarsa akwai dawaki masu kyawo a can.

     

    A wata waƙar kuma Amali yana cewa:

     Jagora : Inda na Cedi nit taho,

      : Yai dokin kiɗi ya ba Mamman, 

     

      ’Y/Amshi  : Yai dokin kiɗi ya ba Mamman

    : Riƙa da gaskiya,

      : Rana ba ta sa ka tasowa,

         : Iro Ɗangado Goga[9] mai kiyo cikin jema.

     (Amali  Sububu: Iro Ɗangado)

     

    Shi ma nan Amali ya roƙi kyautar doki ne, yana fatar ubangidan nasa ya sami wani doki ya ba shi, wato ya nuna kamar saboda shi kawai ya taho ya kawo masa kiɗinsa.

     

     G/Waƙa : Na taho in gaisai ya aika man,

     

        Jagora : Goje raƙumi kaka sai man,

         : Shi nir roƙa,

         ’Y/Amshi : Kai a sai ma doki,

    : Shi ad daidai,

     

        Jagora : Ko ka sai man honda,

        ’Y/Amshi : Shi ma daidai,

     

       Jagora : Ko ka sai man besfa.

        ’Y/Amshi : In hau daidai,

    (Amali  Sububu: Sarkin)



    [1]  Bunza (2009: 63).

    [2]  Mafi-yawa

    [3]  Al’ummar Hausawa kan mayar da hankalinsu ne wajen kallon watan sallah tun daga ranar ashirin da tara ga watan kafin sallah.

    [4]  Sauri

    [5]  Saya masa

    [6]  Nunawa

    [7]  Itace ko ƙarfe ko wani abu da ake kafewa ƙasa don a ɗaure dabba.

    [8]  Miji

    [9]  Babban sa maji ƙarfi.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.