Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Taƙaitaccen Tarihin Amali Sububu
Sunan Amali na asali shi ne Muhahammadu, wannan sunan da ake yi masa laƙabi ne wanda kakarsa Abi
(wato Rabi) ce ta sa masa shi. Wannan ya faru ne kasancewar surukinta wato mahaifin mijinta
shi ma sunansa kenan (Muhammadu), kuma a al’adance matan Hausawa ba su faɗin sunan surukansu wato iyayen mazansu na aure, don haka
bayan haihuwarsa da aka sa masa sunan, sai ta ce an sami amali kenan, daga nan
aka cigaba da kiransa da wannan sunan na Amali. A wani ƙauli kuwa an ce ita kakar tasa ta sa
masa sunan Amali ne saboda irin kazar-kazar da yake da shi wajen gudanar da
harkokinsa, wato shi mutum ne mai zafin nama baya da kasala kamar dai yadda amali
yake. Ana samun amali ne a cikin jinsin dabbobi wato raƙuma, Idan an kira raƙumi amali to ana nufin
wani raƙumi ne wanda ya gawurta wanda yake shugabancin ayarinsu na ‘yan’uwansa raƙuman mazansu da matansu.
1.1 Asalin Amali Sububu
An haifi Amali Sububu a garin Sububu da ke cikin gundumar Ƙaya wadda ke a Arewacin Maradun a ranar Lahadi 11 ga watan biyu 1933, garin Sububu yana ƙarƙashin riƙon ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara. Sunan mahaifinsa Malam Aliyu, mahaifiyarsa kuwa sunanta Ramatu amma an fi saninta da suna Azumi. Ya tashi a garin Sububu wato garin da aka haife shi wanda kuma ake kiran sunansa tare da shi wato Amali Sububu, kodayake bayan wani lokaci malam Aliyu mahaifinsa ya canja gari, ya koma wani gari da zama, shi ma a cikin wannan yankin na Maradun yake wanda ake kira Gidan bisa, mai nisan kimanin kilomita ɗaya rak a tsakaninsu da Sububu.
Amali yana da matan aure guda biyu Hauwa da Jimma, Hauwa
ita ce babbar matarsa, sai Jimma ta zama amaryarsa. Yana da ‘ya’ya tara maza da
mata, maza huɗu mata biyar. Mazan sun haɗa malam Sada da Liman Gado da Hamisu da kuma Murtala. Su
kuma matan sun haɗa da Rabi ana ce mata Sadau da
Wakkala da Tumba da Umaima da kuma Hajiya Mairi.
Ga yadda nasabar Amali take:
Kakan Amali wanda ya haifi Aliyu wato mahaifin Amali ana
ce masa Gona matarsa wato wadda ta haifi Aliyu ita ce Halima. A ɓangaren uwa kuwa wato Azumi mahaifiyar Amali kenan, sunan
mahaifinta shi ne Ummaru, mahaifiyarta kuwa Abi ake kiranta (wato Rabi). Dangin
Amali kuwa su ne Abu Amali da Malka da Sa’a da Ta’olo (Dije) da kuma ƙaunarsu Hure. Amali shi
ne babba a wajen iyayensu, duka sauran ƙannensa ne kuma uwa ɗaya uba ɗaya.
Ga yadda taswirar nasabarsu ta
kasance:
1.2 Wasu Sana’o’in Amali
Amali mutum ne wanda ya tashi da kazar-kazar wajen ganin cewa ya sami na kansa tun yana ƙaraminsa, shi ba ci-ma-kwance ba ne. Ko da ya shahara a kan yi wa wasu manoma waƙoƙin noma yana da wasu sana’o’in da yake yi waɗanda yake samun abubuwan biyan bukatunsa, kuma kowace daga cikinsu Amali ya riƙa ta sosai ba da wargi ba. Ga bayanin sana’o’in kamar haka:
1.2.1 Sana’ar Kanikanci
Kanikanci sana’a ce ta gyaran na’urorin da aka saye domin yin amfani da su na yau da kullum, waɗanda Turawa suka yi kamar su Agogo da rediyo da keke da mashin har mota da jirgi idan sun lalace. Haka kuma akan gyara wasu kayayyakin amfanin waɗanda ba lalle ne Turawa suka yi su ba, kamar galemanin huɗa ko noma da sauransu.
Amali ya ƙware kan sana’ar kanikanci a ƙauyensu musamman kanikancin rediyo. Jama’ar garin Sububu da Gidan bisa da kewaye suna kai wa Amali gyaran rediyoyinsu idan sun lalace, duk yadda rediyo ya rikirkice ya ƙi magana Amali kan gwada sa’arsa don ya sa ya yi magana, ya san yadda ake saitin muryar rediyo da ƙulla zaren gano tasha idan ya tsunke, da sa kwandasta da ƙullawa ko jona waya idan ta katse, ko kuma waldar jikin rediyon idan ya ɓaɓɓalle da sauran matsalolinsa.
Bayan gyaran rediyo Amali ya iya gyaran mashin (wato babur) na hawa, idan kafirata ta lalace yana gyarawa, yana sa fistin da ringi da kuma sabis, yakan duba fitila idan ta ɗauke. Idan an kai masa babur ɗin da ya lalace yakan duba shi sosai har ya tayar da shi don a ci gaba da amfani da shi.
1.2.2 Sana’ar Fawa
Haka kuma kasancewar mahaifinsa mahauci ne, Amali ya iya
fawa kuma yana sana’ar, wato ya yanka dabba ya sayar da namanta ga jama’a,
1.2.3 Ubandawaki
Kafin dai Amali ya kai ga nasa kiɗi ya yi Uban dawakin[1]noma,
wato noma wanda mutun ke yi da hannunsa kuma ya shahara sosai a lokacin don har
wasu makaɗan noma sun riƙa yi masa kiɗa da waƙa saboda irin tasa shaharar, daga cikin makaɗansa akwai Dogo
yana kiɗin ganga da kuma Maigandi duk sun yi
wa Amali waƙoƙin noma.[2]
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.