Ticker

6/recent/ticker-posts

Gabatarwa - Daga littafin Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Gabatarwa

Wannan littafi ya ƙunshi bayanai ne masu inganci dangane da wani shahararren makaɗin noma wanda aka sani da suna Amali  Sububu, littafin zai kawo salsalar mawaƙin ta hanyar kallon tarihinsa da samar da bayanai a kan fara waƙarsa da dangantakarsa da sauran makaɗa musamman na noma. Har ila yau, lattafin zai kawo nau’o’in waƙoƙinsa da waɗanda ya fi raja’a a kansu.

An yi nufin shirya wannan littafi ne domin ya dubi waƙoƙin Amali  Sububu, don su amfanar da jama’a musamman ɗaliban makarantun sakandare da na gaba da sakandaren, har ma da malamansu waɗanda ke son su san wani abu a kan waƙoƙin noma Musamman na Amali  Sububu. An yi la’akari da irin yadda waƙoƙinsa suke bunƙasa a wannan lokaci, suna yaɗuwa a dukan ɓangarorin ƙasar Hausa har da maƙwabtanta.

Makaɗa Amali  Sububu ya yi waƙoƙi da yawa waɗanda suka haɗa da na noma da ma waɗanda ba na noma ba, waɗanda dukansu an fahimci cewa mutane suna da sha’awa da su, to sai aka ga ya dace a tattaro su daidai gwargwado don a alkinta su don jama’a su amfana.     

Mutane kan ji waƙoƙinsa ne su saurare su domin daɗinsu, ko jin kalaman daɗaɗa zukata da mawaƙin ya yi amfani da su, har ma wani lokaci sai mutane su riƙa samun wasu waƙoƙin don wata ƙila su saurara, ko ma wani lokaci su yi kasuwancinsu. Wannan littafin dai zai share hawayen jama’a kan waƙoƙin Amali  Sububu domin sanin yadda ya fayyace su filla-filla.

           

Wannan aikin an gudanar da shi ne a cikin mawuyatan halaye guda biyu; na farko shi ne a lokacin da shi mawaƙin baya a raye (wato ya riga ya rasu) tun kafin a fara aikin, don haka ba a samu waɗansu bayanan da ake buƙata ba daga bakinsa, wanda idan son samu ne hakan ya fi kyawo da inganci. Mawuyacin hali na biyu kuwa shi ne na yanayin tsaro! A lokacin gudanar da wannan aikin ana cikin wani yanayi na rashin tsaro, inda ‘yan ta’adda suke kashe mutane da sace su suna garkuwa da su, abin ya yi tsanani a yankin Sububu har ma garin ya watse babu kowa a ciki! Domin haka sai ma an nemi wanda ake son a sami wani bayani daga gareshi ta waya don a san inda yake! Idan wani lokaci an samu to a tsorace ake haɗuwa babu aminci, kowa yana ɗar-ɗar da kowa. Allah ya sawwaƙe mana, ya nuna mana ƙarshen wannan iftila’in[1] amin.



[1]  Jarrabawar ko faruwar wani mummunan abu. 

Post a Comment

0 Comments