Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Raƙumin Daji
A garin Tsabre yake sunansa Musa mutumen gidan maƙera a ƙaramar
hukumar Sabonbirni ta jihar sakkwato, Musa ya shahara ga noma sosai don haka
Amali ya yi masa waƙarsa.
G/Waƙa : Na taho in gaisai,
: Ya aika man,
: Raƙumin daji,
: Bai zanna ba.
Jagora: Na
taho in gaisai,
: Ya aika man,
: Raƙumin daji,
: Bai zauna ba.
‘Y/Amshi:
Na taho in gaisai,
: Ya aika man,
: Raƙumin daji,
: Bai zanna ba.
Jagora:
Musa ɗan Isah.
‘Y/Amshi: Noma sabo,
Jagora: Ganɗo[1]
mai tsaida ruwa.
‘Y/Amshi:
Ɗanɗan Kande.
Jagora:
Gurbi mai ɗauke ruwa.
‘Y/Amshi:
Ɗanɗan Kande.
Jagora:
A kai ni Tsauren sarki.
‘Y/Amshi:
Musa na can.
Jagora:
A kai ni Tsauren sarki,
‘Y/Amshi:
Musa na can.
Jagora: Gidan maƙera an nan.
‘Y/Amshi:
Ba samnan ɗa.
Jagora: Ina ganin raggon ɗa,
: Nik kauce mai.
‘Y/Amshi:
Saboda na san Allah ya ebe mai.
: In gaisai,
: Ya aika man,
: Raƙumin daji,
: Bai zanna ba.x2
Jagora: Musa ɗan Isah.
‘Y/Amshi:
Noma sabo.
Jagora: Goje raƙumi kaka sai man.
: Shi nir roƙa.
‘Y/Amshi:
Kai a sai ma doki,
: Shi ad daidai.
Jagora: Goje raƙumin yaka sai man,
: Shi nir roƙa.
‘Y/Amshi:
Kai a sai ma doki,
: Shi ad daidai.
Jagora: Ko ya sai man honda[2].
‘Y/Amshi:
In hau rairai[3].
Jagora: Ko ya sai man besfa.
‘Y/Amshi:
In hau da ita,
: In gaisai,
: Ya aika man,
: Raƙumin daji,
: Bai zanna ba.
Jagora: Na
gaida Garba Garba Dauran,
‘Y/Amshi:
Ya aika man,
: Ra ƙumin daji,
: Bai zanna ba.
Jagora: A
kai ni Tsauren Sarki,
‘Y/Amshi:
Musa na can.
Jagora: Isah ka kai ni Sakkwato birni.
‘Y/Amshi:
Domin manzo.
Jagora: Sakkwato birnin Shehu.
‘Y/Amshi:
Lalle[4] Jatau.
Jagora: Gusau ta malan Sambo.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau.
Jagora: Allah kai ni Kaduna.
‘Y/Amshi:
Domin Manzo.
Jagora: Allah kai ni Habuja.
‘Y/Amshi:
Domin Manzo.
Jagora: Yaro man kaza ne.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau[5].
Jagora: Rana ta yi ya narke.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau.
Jagora: Hanƙurin wuta sai ƙarhe.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau.
Jagora: Wata tahiya sai mota.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau.
Jagora: Amali mai ciki cike da kiɗi.
‘Y/Amshi:
Ɗanɗan Dije.
Jagora: Amali mai akwatin waƙa.
‘Y/Amshi:
Ɗanɗan[6]
Dije.
Jagora: Mai cikin da yac cika da kiɗi.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau.
Jagora: Gaban ga duk launi ne.
‘Y/Amshi:
Lallai Jatau.
Jagora: Cikin ga duw waƙa ce.
‘Y/Amshi:
Lallai Jatau.
Jagora: Ka ji abin da ni iya nis saba.
‘Y/Amshi:
Lallai Jatau.
Jagora: Akawai kiɗin a kwai kuma
: waƙa.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau.
Jagora: Noma dai karen gida yas sace.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau.
Jagora:
Ko shi ko muna iyakan namu.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau.
: In gaisai,
: Ya aika man,
: Raƙumin daji,
: Bai zanna ba.
Jagora: A gaida Binta mai kasa marsa[7].
‘Y/Amshi:
Ta kyauta[8]
man.
Jagora: Binta tsohuwa na gode.
‘Y/Amshi:
Ta kyauta man.
Jagora: Bagobira bisije.
‘Y/Amshi:
Ta kyauta man.
Jagora: A’i Buzuwa na gode.
‘Y/Amshi:
Ta kyauta man.
Jagora: Da Shehu baka kwana daji.
‘Y/Amshi:
Ya kyauta man.
Jagora: Da Shehu baka kwana daji.
‘Y/Amshi: Ya kyauta man.
Jagora : Dogo mai ganin ƙulewah[9]
: hanya.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau.
Jagora: Dogo mai ganin iyakah hanya.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau.
Jagora: Inji mutan Shagamu.
‘Y/Amshi:
Lalle Jatau.
: In gaisai,
: Ya aika man,
: Raƙumin daji,
: Bai zanna ba.
Jagora: Ina su mai kasa dawa,
‘Y/Amshi:
Ya gode mai,
: In gaisai,
: Ya aika man,
: Raƙumin daji,
: Bai zanna ba.
Jagora: Musa ɗan isah.
‘Y/Amshi:
Noma sabo.
Jagora: Ganɗo mai tsaida
ruwa.
‘Y/Amshi:
Ɗanɗan kande.
Jagora: Ganɗo mai
tsaida ruwa.
‘Y/Amshi:
Ɗanɗan kande.
: In gaisai,
: Ya aika man,
: Raƙumin daji,
: Bai zanna ba.
[1] Wani abu da ake tare/keɓe ruwa a rafi ko
lambu..
[2] Mashin ne na hawa, wanda ake tafiye-tafiye da
shi.
[3] Yashi.
[4] Haka ne.
[5] Ana yi wa Amali laƙabin Jatau ne
saboda farar fatarsa.
[6] Ɗa
[7] Goro fari, wato tana sayar da goron ne ta hanyar
kasawa ba zaɓi ɗaiɗai ba.
[8] Bayar da kyauta.
[9] Ƙarshe.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.