Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Ɗanja Mai Kwana da Shirin Ma’aikata
Ɗanja
mutumin garin Batamna ne a ƙaramar
hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara. Sunasa Amadu amma an fi saninsa da Ɗanja. Manomi ne na haƙiƙan a ƙauyen nasu kuma koyaushe a shirye yake da ya je gona, wana halayyar tana
burge Amali har ya yi ma mai yinta waƙa.
G/Waƙa : Koma
sakko gona,
: Kar ka tsaya zaman gida,
: Mu gaida Ɗanja,
: Mai kwana da shirin ma’aikata[1].
Jagora: Kuikuyon zaki,
: Mai maida bida kake Ɗanja.
‘Y/Amshi:
Irin gidan Ummaru,
: Ka zan zakaran ɗiya maza,
Jagora
: Kuikuyon[2]
zaki,
: Mai shanye dahi[3]
kake Ɗanja.
‘Y/Amshi: Irin gidan Ummaru.
: Ka zan zakaran ɗiya maza.
Jagora: Ba iyaka ba da kai,
: Ba a biye ka ga noma,
‘Y/Amshi:
Wanda duk ka biye ma,
: Ba ya zuwa gida maza,
: Koma sakko gona,
: Kar ka tsaya zaman gida,
: Mu gaida Ɗanja,
: Mai kwana da shirin ma’aikata.
Jagora: Noma da kai aka sauna,
: Ba a haye maka barde,
: Sallama kada gaba,
: Geme baban yaro,
: Garnaƙaƙi kake ɗan ja,
‘Y/Amshi:
Wanda duk ka haye ma,
: Toggo[4]
yana ganin gida,
: Koma sakko gona,
: Kar ka tsaya zaman gida,
: Mu gaida Ɗanja,
: Mai kwana da shirin ma’aikata.
Jagora: Mata wadda ba a wa iba[5],
‘Y/Amshi: Mik kai ta zuwa masussuki[6],
Jagora: Mata wadda ba mijin kirki,
‘Y/Amshi:
Mik kai ta zuwa masussuki,
Jagora: Duw wadda ba a ba damma.
‘Y/Amshi:
Mik kai ta zuwa masussuki.
Jagora: Wadda ba a wa iba[7].
‘Y/Amshi:
Mik kai ta zuwa masussuki.
Jagora: Wadda ba na albarka.
‘Y/Amshi:
Mik kai ta zuwa masussuki.
Jagora: Macce mai koda.
‘Y/Amshi:
Abu sai mu aje ta tsohuwa.
Jagora: Macce mai koda.
‘Y/Amshi:
Abu sai mu aje ta tsohuwa.
Jagora: Mijinta in Goje ne.
‘Y/Amshi:
Ba ta yini tsakar hwaƙo.
: Koma sakko gona,
: Kar ka tsaya zaman gida,
: Mu gaida Ɗanja,
: Mai kwana da shirin ma’aikata.
Jagora: Abin da ar arne.
‘Y/Amshi:
Gero ya tsaya cikin gida.
Jagora: Abin da ag Goje[8].
‘Y/Amshi:
Gero ya tsaya cikin gida.
Jagora: Ya yi matan tsara,
: Sun isa,
: Ga su hwarhwaru,
: Ga katanbiri,
: Ga hwankeke;
: Ana yi mai ƙawa,
: A shafa gazal,
: A kusanto shi,
: Ana ƙyahwat ƙyahwat,
: A shafa jan baki,
: A dibo shi ana ta washiya,
: Su shahwa kwalli.
‘Y/Amshi:
Ka ga an buɗe ido narau-narau[9],
: Koma sakko gona,
: Kar ka tsaya zaman gida,
: Mu gaida Ɗanja,
: Mai kwana da shirin ma’aikata.
Jagora: Duw wurin da yad duba.
‘Y/Amshi:
Daɗi yaka ji cikin gida.
Jagora: Duw wurin da yad hanga.
‘Y/Amshi:
Daɗi yaka ji cikin gida.
: Koma sakko[10]
gona,
: Kar ka tsaya zaman gida,
: Mu gaida Ɗanja,
: Mai kwana da shirin ma’aikata.
[1] Gona.
[2] Ɗan wata dabba wanda ba a daɗe da haihuwarsa
ba.
[3] Dafi-poision.
[4] Da ƙyar/ ƙila.
[5] Ɗebo hatsi daga cikin
rumbu/rihewa don a sussuka a yi amfani das hi wajen dafa abinci.
[6] Ibda ake sussujar gero ko dawa.
[7] A ɗebo
hatsi daga runbu don a sussuka.
[8] Shahararren manomi.
[9] Hasken ido, fari cikin ido ya yi fari baƙin ɗigon cikin ido ya
yi baƙI
gwanin sha’awa.
[10] Sammako.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.