Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Gidan Nasara (Ta farko)

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Mai Gidan Nasara (Ta farko)

Ana kiransa da suna Muhammadu Sani, wasu suna kiransa Autan Yaya, amma an fi ce masa Noma, saboda shahararsa ga noma. Abokin wasan (taubashin) Amali ne, mutumen garin Kuzi ne da ke cikin mazaɓar Faru da ke cikin ƙaramar hukumar Maradun.

 

 G/Waƙa : Ka yi sunan noma,

   : Mu gaisai da aiki,

   : Mai gidan Nasara,

: Ɗan da yat tara damma.

 

    Jagora: A jinjina[1] a aje,

: Ba shi komi da hwata,x2

   : Tunkuɗa[2] yaro,

: Ba ta komi da dutsi.

 

    ‘Y/Amshi: Noma jan zaki,

   : Mai wa yaro kujera[3].

   : Ka yi sunan noma,

   : Mu gaisai da aiki,

   : Mai gidan Nasara,

: Ɗan da yat tara damma.

 

   Jagora: Gajere abun da yawa,

   : Inda baƙon Habibu,

   : Ina gida wani bin,

: Hankalina ka tashi,

   : Ga ni can wani bin,

: Zuciyata ta yo nan,

   : In biyo hanya,

: In taho in da Mamman,

: Ko da niz zaka.

    ‘Y/Amshi: Sai hankali na ya kwanta,

   : Ka yi sunan noma,

   : Mu gaisai da aiki,

   : Mai gidan Nasara,

: Ɗan da yat tara damma.

 

   Jagora: Sai hankali na ya kwanta,

   : Ka yi sunan noma,

   : Mu gaisai da aiki,

   : Mai gidan Nasara,

: Ɗan da yat tara damma.

 

    Jagora: Dut inda niz zaka[4],

    ‘Y/Amshi: Sai hankali na ya kwanta,

 

   Jagora: Yanzu kam Mamman,

   : Sai ka hausan ga doki,

   : Wanda  za ni gwada[5] wa,

   : Gida can ga dangi,

   : In yi mai turke,

   : Masu sona su duba,

   : Gashi dai nauna ba,

   : Giri babu mashi,

   : Ko na hwan huɗu ne.

     ‘Y/Amshi: Noma na so ka bani,

   : Ka yi sunan noma,

   : Mu gaisai da aiki,

   : Mai gidan Nasara,

   : Ɗan da yat tara damma,

 

   Jagora: Kuma in  akwai hali,

   : Ba matcewa ga dokin,

   : Ko jiran ka nikai,

   : Hak ka dubo Talata,

   : Kasuwam Mahwara.

    ‘Y/Amshi: Mai dawaki da shawa.

: Ka yi sunan noma,

: Mu gaisai da aiki,

: Mai gidan Nasara,

: Ɗan da ya tara damma.

 

   Jagora: Noma wa nane dum,

   : Nu ɗauko ta tushe,

   : Ɗan uwana ne,

   : Wanda yak kai jimilla,

   : Lissahin da nikai,

   : Tamu kaka halima,

   : Mai biɗaj jikan gona.

    ‘Y/Amshi: Ku za ya dibi,

   : Ka yi sunan noma,

   : Mu gaisai da aiki,

   : Mai gidan Nasara,

: Ɗan da yat tara damma,

 

   Jagora: Wanga  ko wajje,

: Noma Jikan Salau ne,

   : Irin gidan Abdu,

: Jan kada dama gurbi[6],

   : Taƙamad da nikai,

     ‘Y/Amshi: Taka ce don kaji ta,

   : Ka yi sunan noma,

   : Mu gaisai da aiki,

   : Mai gidan nasra,

: Ɗan da ya tara damma.

 

    Jagora: Duniya da yawa bani,

   : Roƙon bahili,

   : Ina ganin zaure,

   : Ba ni kwana  ga hanya,

   : Na gano shigihwa,

   : Ba ni kwana ga bukka,

   : Na gano ɗaki,

    ‘Y/Amshi: Ba ni kwana ga zaure,

   : Ka yi sunan noma,

   : Mu gaisai da aiki,

   : Mai gidan Nasara Ɗan da,

   : Ya tara damma,

 

   Jagora: Yawan hwarauta,

: Mai tsunke Gyado[7] ga daji,

   : Shi da ba rame,

: Ba wurin molaƙewa,

   : Sai ya dunga gudu,

   : Har a cimmai akame,

   : Shi na iyaka yi nai,

    ‘Y/Amshi: A ci mai mutunci.

   : Ka yi sunan noma,

   : Mu gaisai da aiki,

   : Mai gidan Nasara,

   : Ɗan da yat tara damma,

 

   Jagora: Mai kwaɗan nama,

   : Sai ya dawo ga tuji,

   : Don ganin suturar,

: Mujiya gat ta jaka,

   : Ina ganin gashin mujiya,

   : Manya-manya,

   : Koda nit tona.

    ‘Y/Amshi: Mujiya babu nama,

 

   Jagora: Amali na gane mujiya,

   ‘Y/Amshi:‘Yak kaɗan ta.

   : Ka yi sunan noma,

   : Mu gaisai da aiki,

   : Mai gidan Nasara,

   : Ɗan da yat tara damma[8].  



[1]  A ɗauki abu don a ji kwatancin nauyinsa.

[2]  Turawa.

[3]  A zaunar da mutum saboda ya kasa ko an tsare masa.

[4]  Zowa/tahowa

[5]  Nunawa

[6]  Inda ruwa ke kwantawa a rafi ko tafki da sauransu.

[7]  Wata dabba mai haƙora gaye-gaye, wanda ke tono rame das u ya shige.

[8]  Ɗaure-ɗauren gero ko dawa ko wani abu.

Post a Comment

0 Comments