Ticker

6/recent/ticker-posts

Mukaddima - Daga littafin Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Muƙaddima

Makaɗan baka na Hausawa kan taka muhimmiyar rawa wajen ba da irin tasu gudummawa ga duk wani abu da ya shafi zamantakewar Hausawa. Wannan gudummuwa tasu bata tsaya ba ne don samar da nishaɗantarwa, a’a har ma wani ƙarin ci gaba ne ga rayar da harshen Hausa. Sauye-sauyen zamani shi ne babban jigon da ke tallafa wa mawaƙa wurin ƙirƙiro fasaharsu.        

Hausawa suna daga cikin mutanen da suka dogara ga ayyukan noma don samun abincinsu.Wannan ne yake sa ake samun makaɗan Hausa masu yi wa manoma da noma waƙoƙi daban-daban don su zaburar  da su wajen jajircewa ga aikin noma  domin samun wadataccen abinci a ƙasar Hausa. Makaɗan noma na daga cikin rukuni na biyu na makaɗa a tsarin makaɗan Hausa da suka biyo bayan makaɗan farauta da na yaƙi.  

Waƙoƙin Amali Sububu sun ƙunshi basira da jayo hankali don sarrafa harshen Hausa. A cikinsu ya kwarzanta manoma, a lokaci guda kuma ya muzanta raggon mutun, wannan ya sa ya zaburar da al’ummarsa da su tashi tsaye haiƙan ga aikin gona, a lokacin guda kuma yake fargar da raggo ya sauya halinsa don ya kama aikin noma.

Duk wani manazarci da mai sha’awar harshen Hausa a gaba ɗaya, ko kuma waƙoƙin Hausa a keɓance, zai gamsu da irin basirar da Allah ya ba Amali Sububu ta yadda ya ƙarfafa manoma da zaburar da su ga ayyukan gona.

Ina yaba wa marubucin wannan littafi da ya taskace waƙoƙin wannan mawaƙi, kan irin ƙoƙari hangen nesansa ta yadda ya fito da wannan shahararren mawaƙin Hausa musamman a fannin noma a fili domin kada irin gudunmuwarsa ta tafi a banza. Ina kira ga ɗalibai a kowane mataki na karatu da ma malamai da su mallaki wannan littafi saboda wani rumbu ne da ke da mahimmanci ga nazarin adabin Hausa.

A ƙarshe ina yi wa mawallafin wannan littafi fatan alheri da kuma roƙon Allah (S.W.T) ya ƙara buɗi da basira ya cigaba da zaƙulo muna ayukka masu muhinmanci da amfani a harshen Hausa.    

Dr. Hamza Ainu
Cibiyar Nazarin Hausa,

Jami’ar Usmanu Ɗan Fodiyo, Sakkwato.

Post a Comment

0 Comments