Ticker

6/recent/ticker-posts

Godiya – Daga littafin Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Godiya

Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki, mai iko a kan  kowa da komai, wanda ya ƙaddara in rubuta wannan littafi na Amali  Sububu. Ina godiya ga iyayena waɗanda suka taimaka mani tun ina ƙarami har kawowa yanzu, suka tarbiyyantar da ni, suka kuma sa ni makarantu daban-daban na karatun addini da na boko. Suka kuma bani ƙwarin guiwar tsayawa in yi karatun. Allah ya saka masu da mafificin alherinsa, amin. 
Ina kuma miƙa godiyata ga Maimartaba Sarkin Fulanin Bunguɗu Alhaji Hassan Attahiru (MFR) bisa goyon bayan da yake bani a kodayaushe ta ɓangarori da dama, Allah ya saka masa da alheri. Dole in gode ma malamina Docta Hamza Ainu wanda ya duba wannan littafi tare da yin gyare-gyare a cikinsa tare da bada shawarwari don ƙara inganta shi ya kasance abin amfani ga al’umma baki-ɗaya, Allah ya biya shi. 
Ina godiya ga Dr. Isah Bala Homawa wanda ya saba bani ƙwarin guiwar tafiyar da harkokina na cigaba, ya kuma saba taya ni bincike na dukkan wani abu da ya ɗaure man kai, Allah ya biya shi. Ba zan manta da Idris Muhammad (Ɗan Asabe) Homawa ba, wanda ya taimaka mani wajen samo man wasu tsofaffin waƙoƙin da ba a samun su a kasuwa na Amali  Sububu, na ji daɗi ƙwarai na kuma gode masa Allah ya saka da alheri. Keɓantacciyar godiya zuwa ga Alhaji Bello Umar Bunguɗu da malam Aliyu Abubakar Kanoma na gidan rediyon jihar Zamfara saboda gudummuwar da suka bani wajen tattara waƙoƙin da gyaggyara su, Ina godiya ga Baba da Baba da abokin Baba wato Dr. Umar Bello da Dr. Abbas Bunza da Malam Salihu Jangebe domin ƙwarin guiwar da suke bani a kan wannan aikin, Allah ya saka masu da alheri. Sai wata gagarumar godiya da zan tura a garin  Sububu, wajen Alhaji Ɗan Idi  Sububu wannan bawan Allah ya taimake ni ya bani bayanai tare da haɗa ni da yaran marigayi Amali  Sububu, daga cikin ‘ya’yansa na sadu da Liman Gado na kuma haɗu da yaronsa mai yi masa amshi Hamidu  Sububu, sun kuma taimaka mani da dukkan bayanan da nike so, na kuma amfana matuƙa, Allah ya saka masu da alheri. 
Ina kuma gode ma abokin aikina wato Abdulmalik Aliyu Maradun wanda ya sada ni da Yusuf Aliyu Maradun (coordinator) jagorana na farko zuwa garin  Sububu, ina godiya Allah ya biya su baki-ɗaya. Su ma abokaina waɗanda suke bani shawarwari a kan rubuce-rubucena ina gode masu, kamar su malam Bashir Aliyu Tsafe da malam Almustafa S/Fulani Bunguɗu da Idris Abubakar Bunguɗu da Abdullahi Abubakar Bunguɗu da malam Ibrahim Ahmadu Ɗan’amarya da dai sauran waɗanda ban samu kawo sunayensu ba. Na gode Allah ya bada lada, amin. 

Post a Comment

0 Comments