Ticker

6/recent/ticker-posts

Kamancen Daidaito a Wakokin Amali

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Kamancen Daidaito a Waƙoƙin Amali

Wannan ita ce kamantawar da mawaƙi kan yi tsakanin abubuwa biyu domin nuna daidaitonsu ga abin da yake nufi. Akwai irin wannan salo da yawa a cikin waƙoƙin Amali  Sububu. Misali:

 

Jagora : Kana yi ma gona kamar gudun ƙato, x2

  : In ya hangi gobara, in ya hangi,

: Gobara, har in yaz zan gidansu tak kama,

  : Ban san mai tare shi ba.

‘Y/Amshi : Rannan ko galbi[1] as saman hanya,

  : Sai dai yai ƙire biyu.

  : Ya riƙa noma da gaskiya,

  : Na Bakwai bai saba ba da zama,

  : Aikau jikan  Tayawo ɗan Mammam,

  : Kunkelen[2] hwashin[3] ƙasa.

    (Amali: Aikau)

 

Haka kuma ya ce:

   Jagora : Sai na taho da mai huskar shanu.

  ’Y/Amshi : Sai na taho da mai huskar shanu,

    : Ga Ma’azu gwauron daji.

         (Amali  Sububu: Gwauro)

 

Ga kuma wani wurin inda ya kamanta

   Jagora : Sullata nome karkara.

 ’Y/Amshi : Tahi duƙe ga daji,

 : Kamar Irin shanun nan farfaru.

   : Da hanzarin noma nis san ka,

   : Taho gida rana ta hwaɗi,

   : Mu gaida Kartau mai gulbin hura,

   : -------------------------------------------

  

Jagora : Dojindo[4] mai dakan ƙasa,

 ’Y/Amshi : Tahi gilme ga daji,

   : Kamar ana tuƙin jirgin ruwa,

   : Da hanzarin noma nis san ka,

   : Taho gida rana ta hwaɗi,

   : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

(Amali  Sububu: Aikau)

 

Ya sake cewa a wani wurin:

  Jagora  : Sarkin noman garin magaji,

 ’Y/Amshi  : Kai muka dubi,

       : Kamar watan sallah in ya hito,

       : Da hanzarin  noma nis san ka,

    : Dawo gida rana ta hwaɗi,

    : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

    (Amali  Sububu: Sarkin Noman garin Magaji).



[1]  Sanke, wani iccen da ake gittawa a garken shanu don ya tare su kar su fita.

[2]  Kato mai ƙarfi

[3]  Fashi, wato a fasa abu Musamman mai ƙarfi.

[4]  Wani suna ne da akan kira mutum mai ƙoƙarin aiki da shi, ina ka fito aiki ina zaka aiki. 

Post a Comment

0 Comments