Ticker

6/recent/ticker-posts

Kambamawa a Wakokin Amali

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Kambamawa a Waƙoƙin Amali

Ita wannan wani lafazi ne ko furuci da mawaƙa kan yi wanda sai a ga abu ne mai wuya haka ta auku, sukan faɗi abin da ba zai yiwu ba, su nuna ya auku ko zai auku: ko kuma su ce in ma ya auku ba zai hana haddasa wani abu ba. Ɗangambo, (2007:43).

 Jagora : Ta tahi ta bag gida da kewa,

     : Ranan ko ka sawo dawo,

  ’Y/Amshi: Damu sai an yi ma,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Dawo gida rana ta hwaɗi,

 : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

 

Ya kuma ce a cikin wata waƙa:

Jagora : Dare da rana yana gona,

  : Hussani zarton hwashin kuyye.

’Y/Amshi : Dare da rana yana gona,

  : Hussani zarton hwashin kuyye,

(Amali  Sububu: Hussaini Zarton).

 

A wani wurin kuma ya ce:

G/Waƙa : Na taho in kai mai dandama[1] garka tai,

  : Buda ko san noma baya hi nai ƙarhi.

(Amali  Sububu: Buda).

 

Ya kuma kambama Alhaji Garba Dauran a wata waƙar kamar haka:

Jagora : Ku gwada mani inda zan iske Garbu, 

  : A gwada mani inda zan iske Garbu,

  : Nik kau tahi nig ga ƙura ga gona,

  : Han na aza guguwa ce ka noma,

  : Kuma nit tuna guguwa bata kuyye,

  : Ko mota ce ka gafcen jigawa,

  : Mota bata yo kamannin mutum ba,

  : Niz zaburara nit tarekke gabanai.

’Y/Amshi : Yac ce gudu mai dume ga a jima.

  : Gona yake baya wargi da noma,

  : Aiki sabon halin Garba Dauran.

(Amali  Sububu: Garba Dauran).



[1]  Kiɗin noma.

Post a Comment

0 Comments