Ticker

6/recent/ticker-posts

Garba Jan Kada Danladi

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Garba Jan Kada Ɗanladi

Sunan garin su Garba Jan kada Indalumu, garin yana ƙarƙashin ƙaramar hukumar mukin Maradun a jihar Zamfara. Garba shahararren manomi ne wanda ya yi tashen noma a Indalumu da kewaye. Sai Amali ya kai masa ziyara har ya yi masa waƙa.

 

    G/Waƙa : Na ji daɗin magana,

: Da Jan kada[1] Ɗan Mamman,

: Garba Allah ya baka,

: Duniya Ɗanladi.

 

Jagora: Na ji daɗin magana,

: Da Jan kada Ɗan Mamman,

: Garbaa Allah ya baka,

: Duniya Ɗanladi.

‘Y/Amshi: Na ji daɗin magana,

: Da Jan kada Ɗan Mamman,

: Garbaa Allah ya baka,

: Duniya Ɗanladi.

Jagora: Amali ya zaka[2] murna,

: Ga an game ma daji,

‘Y/Amshi: Yau ku ka ikon daji,

: Ga masu yi can daji.

 

     Jagora: Ai bara na zaka nan,

: Anka ce awo ya ja mai.

: Na yini na kwana,

: In ga Garba bai dawo ba,

: Yanzu na dawo,

: Anka ce awo ya samai,

: Na yini na kwana,

: In ga Garba bai dawo ba,

‘Y/Amshi: Abin ga in na gudu ne,

: Amali bai dawowa,

: Kai ko biyab bashi ne,

: Abubakar na yahe,

: Abin da ya yi gudu,

: Dub batutuwan banza ne,

: Na ji daɗin magana,

: Da Jan kada Ɗan Mamman,

: Garbaa Allah ya baka,

: Duniya Ɗanladi.

 

Jagora: Abu abin biya.x2

‘Y/Amshi: Garbaa Abubakar,

: Ina gaishe ka.x2

 

Jagora: Abu na Maishanu.x2

‘Y/Amshi: Gareka za ni roƙon honda.x2.

 

     Jagora: Ai ka gani,

‘Y/Amshi: Hondata da kas sani ta kwanta,

 

     Jagora: Ai ka gani,

: Kekena,

: Da kas sani na saida.

‘Y/Amshi: Da kas sani na saida,

    

Jagora: Kuma ka gani,

‘Y/Amshi: Hondata,

: Da kas sani na saida.

 

     Jagora: Dun na taho,

: Na ba Jut[3] bakanike mun canye,

‘Y/Amshi: Na ba Jut bakanike mun canye,

: Na ji daɗin magana,

: Da Jan kada Ɗan Mamman,

: Garbaa Allah ya baka,

: Duniya Ɗanladi.

 

Jagora: Ina maroƙan birni?

: Ina maroƙan ƙauye? X2

‘Y/Amshi: To ku adana kayanku,

: Mai dume ya nisa[4].x2

: Na ji daɗin magana,

: Da Jan kada Ɗan Mamman,

: Garbaa Allah ya baka,

: Duniya Ɗanladi.

 

Jagora: ‘Yab buga sai watarana.x2

‘Y/Amshi: Ga mai dume ya Koma.x2

 

Jagora: Ni Umma na gode.x2

‘Y/Amshi: Ga bisak[5] kiyo ta ba mu.x2

 

     Jagora: Sai godiya Mairi.x2

‘Y/Amshi: Tunda ta yi kyautah hujja.x2

: Na ji daɗin magana,

: Da Jan kada Ɗan Mamman,

: Garbaa Allah ya ba ka,

: Duniya Ɗanladi.

 

 Jagora: Ku masu yi[6] da mutane,

: Amali na kallom ku,

: Ina ganin da kuna yi,

: Da mu kuna nunowa,

 ‘Y/Amshi: Ko arziki baku so ba,

: Batutuwan banza ne, 

 

Jagora: Wane ko na kwan goma,

: Ba ni cin geronka,

: Wane ko na kwan goma,

: Ba ni cin maiwakka,

: Wane ko na kwan goma,

: Ba ni son wakenka,

: Wane ko na kwan goma,

: Ba ni son kuɗɗinka,

: Tunda hak kaɓ ɓace,

: Mu ka sani kah hwara.

‘Y/Amshi: Ai Tunda hak kaɓ ɓace[7],

: Mu ka sani kah hwara.

: Na ji daɗin magana,

: Da Jan kada Ɗan Mamman,

: Garba Allah ya ba ka,

: Duniya Ɗanladi.

 

Jagora: Komai kwaɗai yac cije[8],

: Ni ba ni cin jemagge,

‘Y/Amshi: Da in ci jemagge gwamma,

: In ci ladak kiwo.

: Na ji daɗin magana,

: Da Jan kada Ɗan Mamman,

: Garba Allah ya ba ka,

: Duniya Ɗanladi.



[1]  Jan kada yana daga cikin nau’o’in kadannu, wanda masunta suke danganta shi da girma da ƙarfi da  ƙwazon kiyo fiye da sauran.

[2]  Wannan Kalmar Sakkwatanci ce  wadda take nufin zuwa.

[3]  Wani bakaniken mashin ne da ake ce ma Jute.

[4]  Soma yin waƙa a lokacin.

[5]  Dabbar gida ta kiyo kamar tunkiya ko akuya ko saniya ko kuma raƙumi.

[6]  Gulma/ cin naman mutum.

[7]  Zagi.

[8]  Kamawa.

Post a Comment

0 Comments