Ticker

6/recent/ticker-posts

Iro Dan Gado

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Iro Ɗan Gado

Iro Ɗangado a garin Danau kusa da Janbaƙo yake ta ƙaramar hukumar Maradun. Yana noma sosai don haka Amali ya waƙe shi.

 

     G/Waƙa : Riƙa da gaskiya,

: Rana ba ta sa ka tasowa,

: Iro Ɗangado,

: Goga[1] mai kiyo cikin jema.

 

 Jagora: Riƙa da gaskiya,

: Rana ba ta sa ka tasowa,

: Iro Ɗangado,

: Goga mai kiyo cikin jema.

‘Y/Amshi: Riƙa da gaskiya,

: Rana ba ta sa ka tasowa,

: Iro Ɗangado,

: Goga mai kiyo cikin jema.

 

Jagora  : Yau ga na Cedi nit taho,

: Bari doki yakai ma mai waƙa, 

‘Y/Amshi: Bari doki yakai ma mai waƙa,

: Riƙa da gaskiya,

: Rana ba ta sa ka tasowa,

: Iro Ɗangado,

: Goga mai kiyo cikin jema.

 

     Jagora: Kyan yaro ya sami yarinya,

: Sai ya cakire[2],

: Wani ya auri macce mai zana,

: Ya sa ta tuwo,

: An huta da romuwa,

 ‘Y/Amshi: Duk hwatatta,

: Na cikin talgin,

: Riƙa da gaskiya,

: Rana ba ta sa ka tasowa,

: Iro Ɗangado,

: Goga mai kiyo cikin jema.

 

Jagora: Kyan yaro ya sami yarinya,

: Sai ya cakire,

: Kyan yaro ya auri yarinya,

: Tai a hankali,

: Wani ya auri macce mai zana[3],

: Ya sa ta tuwo,

: An huta da romuwa,

‘Y/Amshi: Duk hwatatta na cikin talgin,

: Riƙa da gaskiya,

: Rana ba ta sa ka tasowa,

: Iro Ɗangado Goga mai kiyo cikin jema.

 

 Jagora: Riƙa da gaskiya,

: Rana ba ta sa ka tasowa,

: Iro Ɗangado,

: Goga mai kiyo cikin jema.

‘Y/Amshi: Riƙa da gaskiya,

: Rana ba ta sa ka tasowa,

: Iro Ɗangado,

: Goga mai kiyo cikin jema.

   

Jagora: Inda na Cedi nit taho,

: Yai dokin kiɗi,

: Ya ba Mamman, 

‘Y/Amshi: Yai dokin kiɗi,

: Ya ba Mamman, 

: Riƙa da gaskiya,

: Rana ba ta sa ka tasowa,

: Iro Ɗangado,

: Goga mai kiyo cikin jema.

 

Jagora: Riƙa da gaskiya,

: Rana ba ta sa ka tasowa,

: Iro Ɗangado,

: Goga mai kiyo cikin jema.

‘Y/Amshi: Riƙa da gaskiya,

: Rana ba ta sa ka tasowa,

: Iro Ɗangado,

: Goga mai kiyo cikin jema.



[1]  Babban sa mai ƙarfi.

[2]  Yin gayu.

[3]  Tashin fata daga jikin mutum.

Post a Comment

0 Comments