Ticker

6/recent/ticker-posts

Bube Mai Gandu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Bube Mai Gandu

Bube mai gandu mutumen Gidan Sani ne ta hanyar Sakkwato ta ɓangaren Isa. Yana noma hatsi sosai a kowace shekara, har wasu suna ci ta bayansa, don haka Amali ya yi masa waƙa.

 

   G/Waƙa : Kwananka lahiya,

: To kuma tashinka lahiya,

: Na tahi roƙon Ubangiji,

: Allah ya cika man da in ga mai gandu.

 

     Jagora: Kwananka lahiya,

: To kuma tashinka lahiya,

: Na tahi roƙon Ubangiji,

: Allah ya cika man da in ga mai gandu.

‘Y/Amshi: Kwananka lahiya,

: To kuma tashinka lahiya,

: Na tahi roƙon Ubangiji,

: Allah ya cika man da in ga mai gandu.

 

     Jagora: Ka zama dutcin tsakar ruwa,

: Ko an yi gumi ba sani yakai ba,

: Tunda wuya ba ta kai ga mai gandu,x2

‘Y/Amshi: Tunda wuya ba ta kai ga mai gandu.x2

: Kwananka lahiya,

: To kuma tashinka lahiya,

: Na tahi roƙon Ubangiji,

: Allah ya cika man da in ga mai gandu.

 

    Jagora: Zamfara an ce ana kira na.

: Na ce kowa ya dakata,

‘Y/Amshi: Sai na yi ziyara ga Garba mai gandu[1],

 

     Jagora: Zamfara an ce ana kira na,

: Na ce su ma su dakata,

‘Y/Amshi: Sai na yi ziyara ga Garna mai gandu.

 

     Jagora: Katsina an ce ana kira na,

: Na ce su ma su dakata man.

‘Y/Amshi: Sai na yi ziyara ga Bube mai gandu.

 

Jagora: Katsina an ce ana kira na,

: Na ce su ma su hanƙura man.

‘Y/Amshi: Sai na yi ziyara ga Bube mai gandu.

 

     Jagora: Gobir an ce ana kira na,

: Na ce su ma su hanƙura manx,2

‘Y/Amshi: Sai na yi ziyara ga Bube mai gandu.x2

 

     Jagora: Sakkwato an ce ana kirana,

: Na ce su ma su hanƙura man,x2

‘Y/Amshi: Sai na yi ziyara ga Bube mai gandu.x2

 

Jagora: Ko kura tah haɗan tana maiso[2] na,

: Ga inda nan nuhwa,

‘Y/Amshi: Sai na haɗa huska da Bube mai gandu,

: Kwananka lahiya,

: To kuma tashinka lahiya,

: Na tahi roƙon Ubangiji,

: Allah ya cika man da in ga mai gandu.

 

Jagora: Ka kwana lahiya,

: In kuma ka tashi lahiya,

: Su kuɗɗi ba ɗumi[3] sukai ba,

: Ko da ka ba ni ba ni son su,

: Sai mani mota da ni da yarana.

‘Y/Amshi: Sai mani mota da ni da yarana.

: Kwananka lahiya,

: To kuma tashinka lahiya,

: Na tahi roƙon Ubangiji,

: Allah ya cika man da in ga mai gandu.

 

 Jagora: Ka tashi lahiya lau,

: Na ga iyalinka lahiya,

: To kuma ni ga ni lahiya lau,

: Su kuɗɗi ba ɗumi sukai ba,

: Ko da ka ba ni ba ni son su,

: Sai mani mota da ni da yarana.

‘Y/Amshi: Sai mani mota da ni da yarana.

 

Jagora: Su kuɗɗi ba ɗumi sukai ba.

: Ko da ka ba ni ba ni son su,

‘Y/Amshi: Sai mani mota da ni da yaranaa,

: Kwananka lahiya,

: To kuma tashinka lahiya,

: Na tahi roƙon Ubangiji,

: Allah ya cika man da in ga mai gandu.

 

 Jagora: Ka zama dutcin[4] tsakar ruwa,

: Ko an yi gumi ba sani yakai ba,

: Tunda wuya ba ta kai ga mai gandu,x2

‘Y/Amshi: Tunda wuya ba ta kai ga mai gandu.x2

: Kwananka lahiya,

: To kuma tashinka lahiya,

: Na tahi roƙon Ubangiji,

: Allah ya cika man da in ga mai gandu,.

 

     Jagora: Allah shi ad da duniyatai,

: To kuma shi ad da lahiratai,

: Ya yi makaho da mai idanu,

: Ya yi guragu da mai ƙahwahu,

: Kowane ya san wurin laɓewa[5] tai,

‘Y/Amshi: Kowane ya san wurin laɓewa tai,  

: Kwananka lahiya,

: To kuma tashinka lahiya,

: Na tahi roƙon Ubangiji,

: Allah ya cika man da in ga mai gandu,

 

Jagora: Ka zama dutcin tsakar ruwa,

: Ko an yi gumi ba sani yakai ba,

‘Y/Amshi: Tunda wuya ba ta kai ga mai gandu.x2

: Kwananka lahiya,

: To kuma tashinka lahiya,

: Na tahi roƙon Ubangiji,

: Allah ya cika man da in ga mai gandu.

 

     Jagora: Ka tashi lahiya lau,

: Bube iyalinka lahiya,

: To kuma ni ga ni lahiya lau,

: Su kuɗɗi ba ɗumi sukai ba,

: Ko da ka ba ni ba ni son su,

‘Y/Amshi: Sai mani mota da ni da yarana.

: Kwananka lahiya,

: To kuma tashinka lahiya,

: Na tahi roƙon Ubangiji,

: Allah ya cika man da in ga mai gandu.



[1]  Babbar gona makekiya.

[2]  Amai.

[3]  Magana.

[4]  Dutsi.

[5]  Inda yake rayuwa da samun abincinsa.

Post a Comment

0 Comments