Dabbantarwa a Wakokin Amali

    Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Waƙoƙin Amali  Sububu

    Dabbantarwa a Waƙoƙin Amali

    Idan mawaƙi ya ɗauki wani halin dabba ya jingina wa mutum shi to ya yi salon dabbantar da shi. Ko kuma ya kira shi da sunan wata dabba kamar Zaki ko giwa ko Raƙumi Amali da sauran irinsu.

     

    Jagora : Yari irin Amina na Maigujiya,

       : Na Shaɗari.

         ’Y/Amshi : Gyado mai kashin marake,

       : Riƙa da gaskiya,

    : Noma ba kashi yakai ba,

    : Yari Ɗan Bagge noma ba ya saka rama.

    (Amali  Sububu: Yarin ɗan Bagge)

     

    A wani ɗan waƙar kuma ya dabbantar kamar haka:

     

    Jagora : A jinjina[1] a aje,

    : Ba shi komi da hwata,x2

       : Tunkuɗa yaro,

    : Ba ta komi da dutsi.

    ’Y/Amshi : Noma jan zaki,

       : Mai wuyar ɗungujewa[2].

       : Ka yi sunan[3] noma,

       : Mu gaisai da aiki,

       : Maigidan[4] Nasara,

    : Ɗan da yat tara damma,

    (Amali  Sububu: Maidubun Nasara)

     

    Haka kuma ya dabbatar a wani wurin:  

    Jagora : Karen ɓuki da biri,

    : Ku dakata dai ku ji ɓannakku,

       : Inda duk ba ka ƙosa ba,

    : Ba ka fatar ka yijayayya.

      ’Y/Amshi : Na zo garkar Magaji,

    : Ya dai isa in san shi,

           : Allah ya ba ka arzikin,

    : Shirya mutanen yau.

    (Amali  Sububu: Magajin Gera).

     

    Ya kuma yi amfani da salon dabbantarwa a wani wurin:

     

         G/Waƙa : Na taho in gaisai ya aika man,

           : Raƙumin daji bai zauna ba.

    Jagora : Musa ɗan isah,

        ‘Y/Amshi : Noma sabo.

     (Amali  Sububu: Raƙumin Daji)

     

    A nan kuma ya dabbantar kamar haka:

    Jagora : Riƙa da gaskiya,

           : Rana ba ta sa ka tasowa,

           : Iro Ɗangado Goga mai kiyo cikin jema,

    ’Y/Amshi : Riƙa da gaskiya,

          : Rana bata sa ka tasowa,

           : Iro Ɗangado Goga mai kiyo cikin jema,

        (Amali  Sububu: Iro Ɗangado)

    Haka kuma ya dabbantar a nan:

     G/Waƙa : Tahi noma  Sa’idu dokin sukan sabra,

       : Tahi gonakka raƙumi mai yini duƙe[5].

          Jagora  : Sai wata rana  Sa’idu zaure masha baƙi,

        (Amali  Sububu: Saidu dokin sukan sabra)

     

    A waɗannan ɗiyan waƙar Amali ya dabbantar da wanda yake yi ma waƙar ta hanyar kiransa da sunan dabbobi kamar “gyado” da kuma “jan zaki” da “Goga” da “Raƙumin daji”. Ya kuma dabbantar da maƙiyan wanda yake yi wa waƙar da karen ɓuki da biri.



    [1]  A ɗauki abu don a ji nauyinsa.

    [2]  Turewa

    [3]  Mutumen day a shahara ga noma kuma sananne.

    [4]  Miji, kamar a ce mijin Nasara.

    [5]  Yana noma.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.