Ticker

6/recent/ticker-posts

Abuntarwa a Wakokin Amali

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Abuntarwa a Waƙoƙin Amali

Salon alamci shi ne inda mawaƙi zai ambaci wani abu da nufin ya wakilci wani abu da bai ambaci sunansa ba.

Jagora : Tanada[1] baƙin ka majiro.

’Y/Amshi : Tahi sake dabara amali,

: Na gumza[2] garkar gida,

: Da hanzarin noma nis san ka,

: Taho gida rana ta hwaɗi,

: Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

         (Amali  Sububu: Aikau)

 

A wani wurin kuma:

Jagora : Magaji harshe zauna,

: Cikin haƙori ka yi wadagi[3],

 : Ana son a taɓa ka,

: Jalla bai bada umurni ba.

 ’Y/Amshi : Na zo garkar Magaji,

: Ya dai isa in san shi,

 : Allah ya ba ka,

: Arzikin shirya mutanen yau.

 

Amali ya abuntar da gwarzon nasa a nan inda yake kiransa da suna harshe, shi kuma harshe wani abu ne ba mutum ba.



[1]  Yin shiri don sallama.

[2]  Rurin ko kiɗa da waƙa

[3]  Gadara, fantamawa

Post a Comment

0 Comments