Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Mutuntarwa a Waƙoƙin Amali
Mutuntarwa tana nufin Mawaƙi ya ɗauki wata halayya ko ɗabi’a ta mutum ya saka wa wani abu da ba mutum ba kamar
dabba ko tsauni ko ƙwaro da sauransu, kuma ya kasance wannan halayyayr ko ɗabi’ar mutum ne kawai aka san shi da ita. To amma wani
lokacin abin yakan zama akasin haka, Ɗangambo,
(2007:45). Misali:
Jagora : Yunwa
‘yar Buhari ce,
’Y/Amshi : Kowa ba bari ta kai
ba.
: Riƙa da gaskiya,
: Noma ba kashi yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya sa ka rama.
Jagora : Yunwa ta game da ‘yan ƙyare,
: Za su unguwa, tac ce ina nuhwa[1]?
: Sun ce za mu
unguwa,
: Bari in ba ku shawara,
: Ku yi wajen gida ku nemi,
: Abincin da kunka ci,
: In ko kun ƙi shawarata,
: Wahala ta na gaba,
: Sai kun kwana ba abinci,
: Kun tashi ba abin.
: Kun ci tuwon da ba miya,
: Sannan sai gudansu yan noce,
: Yay yi
lissahi,
’Y/Amshi : Yac ce gida nikai,
: Ko aikin maraice[2] in
tai.
: Riƙa da gaskiya,
: Noma ba kashi
yakai ba,
: Yari ɗan Bagge,
: Noma ba ya saka
rama.
(Amali: Yari Ɗan Bagge)
A nan mawaƙin ya yi
amfani da salon mutuntar da yunwa don kuwa ita ba mutum ba ce balle ta yi
magana, yin magana ga wani abu wanda ba mutum ba an mutuntar da shi kenan domin
tun asali bai yin magana, balle ma irin wannan ta masu hankali.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.