Ticker

6/recent/ticker-posts

Karamin Turken Zolaya a Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Ƙaramin Turken Zolaya a Waƙoƙin Amali Sububu

Mawaƙin kan zolayi wasu mutane a cikin  waƙarsa. Zolaya ita ce a ambaci mutum da wanu hali maras kyawo wanda kan sa wasu su yi dariya. Ga wasu wurare da Amali ya kawo irin wannan turken kamar haka:

Jagora : Raggo yana ganin  mai kandu na daka,

  : Raggo kana ganin teadadda na daka,

  : Sai ta yi rangaji ta yi yabƙi nan haka,

  : Yabƙi ɗai takai, yanga ɗai takai,

  : Yat tambaye ni,

: Yac ce yabƙin mi takai,

  : Yabƙi takai mijinta,

: Ta dai gane mashi,

: Ta dai sami gaba nai,

: Rana ta dushe,

  : Bakin ƙarhe bakwai,

: Kai wa ƙarhe takwas,

  : Bakin ƙarhe tara.

’Y/Amshi : Kahin a kai ga sha biyu ya sha nakiya,

  : Zahin rana bai tauye ka ba,

  : Sabon Goje Isah Maikware,

Jagora : Ko kahin akai ga sha biyu,

’Y/Amshi : Duh an durmuya[1],

 

Jagora : Raggo yay yi tagumi,

  : Yac ce gaya ma kowa bana aiki nikai,

  : In na yi jijjihi[2] sai rana ta dushe,

  : In nit taho gida in riƙa saƙar kaba,

  : Wannan abin da kowa yaka so in yi shi.

: In ya yi macce ba yada na haushin runguma,

: Ta rungume shi,

     ’Y/Amshi : Ya yi kamay ya tawwaha,

  : Zahin rana bai tauye ka ba,

   : Sabon Goje Isah Maikware,

(Amali  Sububu: Isah Maikware)

 

Ya kuma kawo wannan turken yana cewa:

Jagora : Damana ta dawo,

: Raggo na kuka,

  : Ya zo ya yi noma,

: Rana ta hana,

  : Ya dawo gida,

: Ba tsabad daka,

  : Ba kuɗin awo,

  : Ya koma bara,

  : Mata sun hana,

  : Kowak kirɓa gona za a yi,

  : Tsohon shegen kuka yat tcira,

  : Raggo yac ce,

: Wayyo Allah,

  : Wayyo annabi,

  : Wayyo yinwa wai mi yai maki?

’Y/Amshi : Koko yunwa jimai za ta yi?

  : Zahin rana bai tauyeka ba,

  : Sabon Goje Isah Maikware.

 

Haka kuma wannan turken ya bayyana a wata waƙar inda yake cewa:

Jagora : Mata wadda ba a wa iba[3].

’Y/Amshi :Mik kai ta zuwa masussuki?

 

Jagora : Mata wadda ba mijin kirki,

’Y/Amshi : Mik kai ta zuwa masussuki?

 

Jagora : Duw wadda ba a ba damma,

’Y/Amshi : Mik kai ta zuwa masussuki?

 

Jagora : Wadda ba a wa iba,

’Y/Amshi : Mik kai ta zuwa masussuki?

 

Jagora : Wadda ba na albarka[4],

’Y/Amshi : Mik kai ta zuwa masussuki?

 

Jagora : Macce mai koda,

’Y/Amshi : Abu sai mu aje na tsohuwa,

 

Jagora : Macce mai koda[5],

’Y/Amshi : Abu sai mu aje na tsohuwa.

 

Jagora : Mijinta in Goje ne,

’Y/Amshi : Bata yini tsakah hwaƙo.

: Koma sakko gona kar ka tsaya zaman gida,

: Mutai ga Ɗanja mai kwana da shirin ma’aikata.

     (Amali  Sububu: Ɗanja)



[1]  Soyayya ta yi tsauri har an kai ga saduwa.

[2]  Wajajen lokacin da ake yin sallar asuba, wani lokaci kafin hakan.

[3]  A ɗebo hatsin da aka adana a cikin rumbu domin a sussuka.

[4]  Mijin kirki mai abin hannunsa, wato manomi mai iya noma abin ciyar da iyalinsa.

[5]  Sana’ar yin sussuka. 

Post a Comment

0 Comments