Ticker

6/recent/ticker-posts

Karamin Turken Sana’o’in Hausawa a ‘Yar Yara a Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Ƙaramin Turken Sana’o’in Hausawa a ‘Yar Yara a Waƙoƙin Amali Sububu

Jagora : Ko Hushe mai koko ta sayar,

’Y/Amshi : Ta bam mai na gaskiya,

    : Noma ba kashi yakai ba,  

     : Yan ɗan Bagge,

  : Noma ba ya saka ka rama.

 

Jagora : Masu biredi sun sayat,

 ’Y/Amshi : Sun bam mai na gaske zamne.

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya saka rama.

 

Jagora : Kuma an taho da tsaba,

: Na iske an sayar,

     ‘Y/Amshi : Dud dai mai na gaske na nan,

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya saka rama.

 

Jagora : Hashimu ya taho da rogo,

: Na iske ya shigat[1],

’Y/Amshi : Duddai mai na gaske na nan.

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge, Noma ba ya saka rama.

 

Jagora : Ko ‘Yat tama da adda haki[2],

    : Na ga ta sayar,

’Y/Amshi : Ta bar mai na gaske zanne,   

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama.

 

Jagora : Malan Abdu ya sayar,

’Y/Amshi : Ya bar mai na gaske zanne.

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama.

 

Jagora : Kuci mai yamri[3] ta sayar,

’Y/Amshi : Ta bar mai na gaske zaumne,

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,  

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya saka rama.

 

Jagora : Kuma Dela uwat[4] tuwo,

: Kuma mun iske ta sayas,

’Y/Amshi : Ta bam mai gaske zamne,

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya saka rama,

 

Jagora  : Hassi ta Amali ta bugo hwanke,

: Na ga ta sayas,

’Y/Amshi : Ta bar mai na gaske zamne,

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama, 

 

Jagora : To ƙarya ba na gaske ne ba x2,

’Y/Amshi : To ƙarya ba na gaske ne ba,

: Riƙa da gaskiya,

: Noma ba kashi yakai ba,

: Yari ɗan Bagge,

: Noma ba ya sa ka rama.

 (Amali  Sububu: Yari Ɗan Bagge)

 

Akwai wata ‘yar kasuwa wadda ake taruwa ana saye da sayar da abinci a unguwannin Hausawa wadda aka fi kira da ‘yar yara ko ‘yar kasuwa da sauransu, Amali ya fito da wannan turken inda ya nuna kowa ya fito yana tallar abinci iri daban-daban, ga jama’a na ta sayen wanda suke so don su ci ko su tafi da shi.



[1]  Sayarwa.

[2]  Dafaffen ganye kamar zogale ko tafasa ko rama.

[3]  Dafaffen ganyen dankali.

[4]  Mai sayar da abinci wadda take da yara masu yi mata aikace-aikace.

Post a Comment

0 Comments