Ticker

6/recent/ticker-posts

Karamin Turken Koda kai/Wasa kai a Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Ƙaramin Turken Koɗa kai/Wasa kai a Waƙoƙin Amali Sububu

Koɗa kai ko wasa kai yana nufin mutum ya faɗi wasu kalmomi da ke nuna shahararsa ko ƙasaitarsa ko kuma ɗaukaka da yake ganin yana da ita:

“Wato ambato ne na abubuwan ƙasaita ko burgewa da mutum yake da su ko ko yake aikatawa. Wani bi akan haɗa da wuce gona da iriinda mutum zai bayyana fifikonsa a kan sauran jama’a, ko ya nuna wata zalaƙarsa ko basirarsa kan wasu da sauran hanyoyin fifitawa. A irin wanna hali mutum yakan zuga kansa da kansa ne. Gusau, S.M (2008).

Jagora : Da arziki na irin na yanzu,

  : Da arziki na ina da raina,

  : Ina da ƙanne ina da yannai,

  : Ina da ‘ya’ya irin na kaina,

  : Akwai rikoda[1] ina da keke,

  : Ina da shanu ina da jakkai,

  : Ina da doki ina da mashin,

  : Ina da gero abin dakawa,

  : Akwai tuhwahin da  Za ni sa wa,

  : Ina da kuɗɗi abin kashewa,

’Y/Amshi : Amali sai godiya ga jabbaru,

  : Shi da yac ce hakanga Jatau.

  : Ya biya mai kudin manoma,

  : Mu kai dumanmu gidan Nadada.

(Amali  Sububu: Nadada).  



[1]  Tape recorder

Post a Comment

0 Comments