Ticker

6/recent/ticker-posts

Karamin Turken Yanayin Damina a Wakokin Amali Sububu

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Ƙaramin Turken Yanayin Damina a Waƙoƙin Amali Sububu

Amali  Sububu yana fitar da yanayin damina a cikin waƙoƙinsa waɗanda suke nuna cewa lokacin noma ya yi, don haka kowa ya fuskanci aikin gona, wanda bai iya yi raggo ne.

Jagora : Yaro bai san kahon-kaho ba,

    : Kuma bai san caɓon-caɓo ba,

: Kuma bai san gumin-gumi ba,

: A kai jubuha[1] ba ka da hatsi ci,

: Ba ka da komi cikin rihewa[2],

: Bisa ruwa ƙasa ruwa,

: Sannan ga noma ba ta tashi,

: Sannan ciwon cikin,

: Maza yake,

’Y/Amshi : Sai ka ga ƙato da shi da mai,

: Ɗakinai an yi shu[3],

: Da hanzarin noma nis san ka,

: Taho gida rana ta hwaɗi,

: Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

(Amali  Sububu: Aikau)



[1]  Wata tauraruwa ce a cikin yanayin shekara., wadda a cikinta ake samun yawaitar ruwan sama, mafi yawa cikin watan Ogas a Arewacin Nijeriya.

[2]  Rumbu, inda manoma ke adana hatsin da suka noma.

[3]  Shiru, a zauna ba a magana.

Post a Comment

0 Comments