Ticker

6/recent/ticker-posts

Karamin Turken Raha a Wakokin Amali Sububu

  Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu


Ƙaramin Turken Raha a Waƙoƙin Amali Sububu

Kalmar raha ararriyar kalma ce daga harshen Larabci wadda take nufin tafin hannu, amma takan ɗauki ma’anar lokacin hutawa da nishaɗantuwa[2]. Ga dukkan alama da ma’anarta ta biyu kalmar ta shigo Hausa.

A harshen Hausa kalmar (Raha) tana nufin hirar jin daɗi da sa dariya[3].

Jagora : Yarinya da tag ga Isah,

 : Gona yana ta noma ya sha gangara,

 : Tay yi duƙe tac ce Isa mi a kai?

 : Yaw waiwayo ta yac ce mata aiki ni kai,

 : Ko kana kwaɗaina[4] bana amre akai,

 : Ko baka kwaɗaina bana amre akai,

   : .........................................................

 : Yac ce wuce-wuce,

 : Ga wata can ta wuce,

 : Waccan da ta wuce hakanan,

 : Tac ce mani,

 : Ke ma da kit taho hakanan kic ce mani.

 : Dubu kamak ki sun ce hakanan,

: Sun wuce,

: In na biye ku,

Ɓata biɗata  Za ni yi,

  : Dum mai biye ma macce,

: Shiga kunya ya kai,

: Sai tay yi zanne,

: Tac ce Isan Dukkuma,

: Sabon yaro, mai kyawon shiri,

: Ka yi min gahwara,

: Ka yi min gahwara,

: Isah Ɗan Buwai.

: Ya waiwayo ta,

     ’Y/Amshi : Yac ce ya yahe mata,

 : Zahin rana bai tauye ka ba,

 : Sabon Goje,

  : Isah Maikware.



[1]  Abin da ake ɗorawa wajen gini, kamar ƙungu ko bulo.

[2]  Duba Ƙamusul Muhid na Fairu Zibady da aka duba a adereshin  yanar gizo

[3]  Abubakar (2015:401)

[4]  Son aure.

Post a Comment

0 Comments