Ticker

6/recent/ticker-posts

Kananan Turaku A Wakokin Amali Sububu

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Ƙananan Turaku A Waƙoƙin Amali Sububu

Ƙaramin turke ya saɓa wa babban turke ta kowace fuska. Na farko dai abin da ya kyautu a kula shi ne babban turke ke haifar da shi. Haka kuma ba don ƙananan turaku ba da babban turke bai fito fili sosai aka gan shi ba. Duk wata waƙa da aka gina wani babban turke ɗaya, za a samu wasu ƙananan turaku da yawa da za su mara wa babban turken baya, domin Ƙawata shi da ƙara fayyace shi sosai. Bunza (2009:64).

 

Idan aka ce ƙananan turaku dai nan ana nufin tuballan[1] da suka gina babban turke, su waɗannan tuballan sun danganta daga waƙa zuwa waƙa, ma’ana dai kowace waƙa da irin nata tuballai da suka samar da babban turkenta. A wasu waƙoƙi za ka ji an samar da yabo, kirari, siyasa, aminci, shaida, sha’awa, roƙo, tuba, ilimi da dai sauransu. Misali idan muka ɗauki waƙar Mu’azu Haɗejia ta Yabon Ubangiji za mu ga cewa ƙananan Turakun su ne suka haɗu suka samar da Babban turke. Ga kaɗan daga cikin ƙananan turakun don ganin yadda abin yake.



[1]  Abin da ake ɗorawa wajen gini, kamar ƙungu ko bulo.

[2]  Duba Ƙamusul Muhid na Fairu Zibady da aka duba a adereshin  yanar gizo

[3]  Abubakar (2015:401)

[4]  Son aure.

Post a Comment

0 Comments