Ticker

6/recent/ticker-posts

Karamin Turken Matakan Girkin Fura A Al’adar Hausawa a Wakokin Amali Sububu

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Ƙaramin Turken Matakan Girkin Fura A Al’adar Hausawa a Waƙoƙin Amali Sububu

Amali Sububu ya kawo wannan ƙaramin turke kamar haka:

: Abin da nih hi so in riƙa ƙaton dame,

 : In yo sussuka,

 : In sheƙe da kyau,

 : In auna da kyau,

 : In surhe da kyau,

 : In wanke da kyau,

 : In kirɓe da kyau,

 : In na yi tankaɗe,

 : In aza sanwa[1] dawo.

 : In nig gama daka, in yi zaman tankaɗa.

 : In dunhe da kyau,

 : In kirɓe da kyau,

 : In dame da kyau,

 : Ka zo ka sha hura,

 : Mu yi ta zaman duniya,

  (Amali  Sububu: Isah Maikware)



[1]  Dafuwa/Dafa abinci.

Post a Comment

0 Comments