Ticker

6/recent/ticker-posts

Karamin Turken Raha Tare Da Batsa a Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Ƙaramin Turken Raha Tare Da Batsa a Waƙoƙin Amali Sububu

Shehun malami ya yi bayanin cewa “wannan turke ya ƙunshi shirya kalmomi na raha a gabatar da su ta yadda za su sanya wani karsashi da nishiɗi a cikin zuciya inda wani bi baki yakan bayyana wannan hali a fili ta hanyar yin dariya” (Gusau 2008. Sh 389).

    

Ga misalin wannan turken a cikin waƙar Amali kamar haka:

Jagora : Kui aniya ku saba da ƙwazo,

 : Kun san biɗa ba ta ƙin ku,

 : In ka ga yaro da mata tcadadda,

 : Tana runguma tai,

 : Hannunta na lalaba tai,

: Ya yi baƙi ƙirin da baƙin lalle.

: Abu dai kamaz zai karewa[1],

: Allan ko baran bai karewa,

: Nonnonta na inguza tai,

: Ka tabbatar ya yi gabce,

: Ka san ba ta iske shi kyauta,

’Y/Amshi : Sai an sha wuya za a shan daɗi.

 : Bai san wuyag gargare ba,

: Ga Garba can za mu jiɗa,

: Namijin da noma ka wa haske.

(Amali  Sububu: Garba)

    

A wata waƙa Amali ya fitar da wannan turken

 

Jagora : Kyawon yaro ya auri yarinya,

 : Shi ak kyau hakan na ga dai.

: Kyawon yaro shi auri yarinya,

: Ga kyawonta ga hali.

: Kyawon yaro ya auri yarinya,

: Ga kyawo da natsuwa,

: Kuma dus sanda ya shigo ɗakin,

: Ta zamna mashi gado,

: Kuma dus sadda tag ganai ɗakin,

: Ga shanya[2] tana yi mai,

: Sai ta yi ban hihhike[3],

: Ta kyabta idonta ta ɗauka mashi  gira.

: In wani wayau gare shi ta amshe,

: Rannan ba shi da shiya.

: Sai ka ga yaro shina rawa da haɓa,

: Ta hyaɗa shi ga gado.

: Ba ta bari nai hita cikin ɗakin,

: Sai ta ƙoshi da shiya,

: To ko ta bas shi ya ya hito ɗakin,

: Ba shawad da zai gani.

’Y/Amshi : Ai duw wata shawa tana cikin ɗakin,

 : Dawo wa yakai maza[4].

: Ya riƙa noma da gaskiya,

: Na Bakwai bai saba da zama,

: Aikau jikan  Tayawo ɗan Mamman,

: Kunkelen[5] hwashin ƙasa.

(Amali  Sububu: Aikau)

 

Akwai maganganu a cikin waɗannan ɗiyan waƙar na sama waɗanda suke raha ne kawai, wasu kuma batsa ne mawaƙin yake fitarwa a waƙoƙin nasa, wannan kuma ba sabon abu ba ne ga mawaƙan Hausa, amma ba a son ana faɗarsu kaitsaye a cikin jama’a a al’adance, kuma idan mutum yana da kunya ba zai iya yin irin waɗannan maganganun ba a gaban kowa.



[1]  Karyewa.

[2]  Jan ra’ayin miji don a tayar masa da sha’awar jima’i.

[3]  Sakin wata alama wadda za ta nuna son a sadu (Jima’i), kamar fari da ido da ɗauka gira da wawan zama da sauransu.

[4]  Da sauri ba wani ɓata lokaci

[5]  Mai ƙarfi.

Post a Comment

0 Comments