Ticker

6/recent/ticker-posts

Karamin Turken Kirari a Wakokin Amali Sububu

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Ƙaramin Turken Kirari a Waƙoƙin Amali Sububu

Kirari ya shafi kwarzanta mutum ta hanyar nuna irin bambancinsa da sauran jama’a irinsa. Ana nuna shahararsa da wasu hikimominsa.

Jagora : Noma da kai aka sauna,

: Ba’a haye maka barde,

  : Sallama kada gaba,

  : Geme baban yaro,

  : Garnaƙaƙi kake ɗan ja.

’Y/Amshi : Wanda duk ka haye ma,

  : Toggo[1] yana ganin gida,

: Kom sakko gona kar ka tsaya zaman

: gida,

: Mu tai ga Ɗanja mai kwana da shirin

: ma’aikata.

(Amali  Sububu: Ɗanja).

    

A waɗannan ɗiyan waƙar Amali ya yi kirari ga gwarzon nasa, dubi kalmomin da ya riƙa kawowa a cikin waɗannan ɗiyan waƙar.[1]  Da ƙyar, wato turaddadin faruwa ko rashin faruwar abu.

Post a Comment

0 Comments