Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali Sububu. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
Ƙaramin Turken Kwalliyar Matan Hausawa Ta Al’ada a Waƙoƙin Amali Sububu
Wannan wani ƙaramin
turke ne a waƙoƙin Amali Sububu, inda ya yi nuni zuwa ga yadda matan Hausawa suke yin
kwalliya a al’adar Hausawa. Kwalliya ita ce saka wani abu wanda yake ƙara wa mutun kyau, musamman ga fuska don a ƙawata ta. Dubi yadda yake cewa:
Jagora : Ya yi matan tsara sun isa,
: Gasu hwarhwaru[1],
: Ga katanbiri[2],
: Ga fankeke[3],
: Ana yi mai ƙawa,
: A shafa gazal,
: A kusanto shi,
: Ana ƙyahwat-ƙyahwat[4],
: A shafa jan baki[5] a
dibo shi ana ta washiya,
: Su shahwa kwalli.
/’Y/Amshi : Ka
ga an buɗe ido narau-narau,
: Koma sakko gona kar ka tsaya zaman gida,
: Mutai ga Ɗan ja mai
kwana da shirin
: ma’aikata,
Jagora : Duw wurin da yad duba,
’Y/Amshi : Daɗi yaka ji cikin gida,
(Amali Sububu: Danja)
Haka kuma:
Jagora : Kyan yaro ya sami
yarinya,
: Sai ya cakire[6],
: Wani ya auri
macce mai zana,
: Ya sa ta tuwo,
: An huta da
romuwa,
’Y/Amshi : Duk hwatatta na cikin talgin,
: Riƙa da gaskiya,
: Rana bata sa ka tasowa,
: Iro Ɗangado Goga mai kiyo cikin jema.
(Amali Sububu: Iro Ɗangado)
Idan ake dubi waɗannan ɗiyan waƙar za a ga cewa mawaƙin ya ɓarje gumensa ne cikin kwalliya inda yake nuna irin tasirinta ga rayuwar
maza da mata musamman ma’aurata, domin irin jin daɗin da maza
suke yi idan sun kalli matansu da suka caɓa kwalliya. Mawaƙin ya ambaci kayan kwalliya na gargajiya kamar katanbiri
da janbaki da fankeke da sauransu. Daga ƙarshe ya
nuna irin yadda maras kwalliya take komawa wata irin ƙazama, har jikinta yana yin zana tana faɗawa cikin
tuwonta.
[1] Farare
[2] Wani abin kwalliya ne baƙi-baƙi, mai kama da kwalta,
mai walƙiya.
Matan da ke yin kwalliya da shi sukan yi kwale da shi.
[3] Hoda wadda mata ke shafwa ga fuskarsu idan za
su yi kwalliya.
[4] Ƙyafawar idanu na jan hankali.
[5] Shi ma wani abin kwalliya ne da mata suke
shafawa ga leɓɓansu idan sun yi
kwalliya.
[6] Jin daɗin rayuwa/ gayu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.