Ticker

6/recent/ticker-posts

Marafa

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

Marafa

Ana kiransa Ma’azu a garin  Sububu yake, wato garinsu guda da Amali, yana noma sosai a lokacin rayuwarsa. Yanzu Allah ya yi masa rasuwa. 

 

     G/Waƙa : Mu taso mu taho gaisai,

   : Batunai luguden[1] sabra.

 

 Jagora: Kai dai a gaishe ka da noma,

   ‘Y/Amshi: Mu kau a gaishe mu da garza ka, 

 

 Jagora: Kai dai a gaishe ka a gaisan,

   : Kai dai a gaishe ka da rana. 

‘Y/Amshi: Mu kau a gaishe mu da garza ka,

: Mu taso mu taho gaisai,

   : Batunai luguden sabra.

 

     Jagora: Allah shi ad da abunai,

   : Marafa ku ad da abin kyauta.

‘Y/Amshi: Marafa ku ad da abin kyauta,

: Mu taso mu taho gaisai,

   : Batunai luguden sabra.

 

     Jagora: Ko kaɗan ban yi zato ba, x2

 ‘Y/Amshi: Ashe Mazuru madaƙuƙi[2] ne,x2

   : Mu taso mu taho gaisai,

   : Batunai luguden sabra.

 

     Jagora: Kai dai a gaishe ka a gaisan,

   : Kai dai a gaishe ka da noma,

     ‘Y/Amshi: Mu kau agaishe mu da garza ka,

   : Mu taso mu taho gaisai,

   : Batunai luguden sabra.

 

    Jagora: Allah shi ad da abunai,

‘Y/Amshi: Marafa ku ad da abin kyauta, 

 

     Jagora: Mai sama shi ke da abunai,

 ‘Y/Amshi: Marafa ku ad da abin kyauta,

: Mu taso mu taho gaisai,

   : Batunai luguden sabra.



[1]  Nome ciyawa.

[2]  Marowaci           

Post a Comment

0 Comments