Ticker

6/recent/ticker-posts

MATAN KAUYE KO MAKARANTAR GUDA

Waƙar Dr Mamman Sha Mai amshi kamar haka: 

Sadauki Shehu Magajin Mamman

Kai tsaya guda na Kwaryar Sallah.

Amshi

Garinsu Yanbiyu matar Malam Garba

Amshi

Garin da akai makarantar guda

Amshi

Kasar da akai makarantar guda

Amshi

Kaji wurin da akai makarantar guda

Amshi

Ganin Daura an wata guda duk bata Kai ba ta Kwaryar Sallah

Amshi

Taron daba an wata guda duk bata Kai ba ta Kwaryar Sallah

Amshi

Ganin Daura an wata guda duk bata Kai ba ta Kwaryar Sallah

Amshi

Kai ko Roni garin gina guda duk bata Kai ba ta Kwaryar Sallah

Amshi

Mutanen Barno sukai wata guda duk bata Kai ba ta Kwaryar Sallah.

Ganin Daura an wata guda donma bakin barbarci ne duk bata Kai ba ta Kwaryar Sallah

Amshi

Garin da akai makarantar guda

Amshi

Kasar da akai makarantar guda

Amshi

Zuwa Sallah tariyar Danmusa Yanbiyu kau na yankan dawa

Amshi

Yanbiyu kau na yankan dawa

Amshi

Mamman yai gaba har yai nisa can sai na rankato wata waka Yanbiyu ta sargaho wata guda zaki tun daga kwaryar kaina sai naji har ksramin danyatsa.

Amshi.

Wai sai kaji guda na wani kamshi kamar ka rike ta kasa bakinka.

Amshi

Kaji guda na kamshin dangoma.

Amshi.

Kace mangwaro Dan gegetso.

Amshi.

Kace mangwaro Dan gegetso.

Amshi.

Kace mangwaro Dan gegetso.

Amshi.

Sai Yanbiyu matar Malam Garba.

Amshi.

Yanbiyu matar Malam Garba.

Amshi.

Yanbiyu matar Malam Garba.

Amshi.

Na Amadu dibgau zakin Bello.

Amshi.

Na Amadu dibgau zakin Bello.

Amshi.

A dandalinsu na gindin kanya daidai inda nabar yaran Nan.

Amshi.

A dandalinsu na gindin kanya daidai inda nabar yaran Nan.

Amshi.

Wasu mata su hudu matan kauye.

Amshi.

Sun zo kallon baban Audu.

Amshi.

Shi ko na Amadu yai gaba har yai nisa sun bude bakin kallonshi.

Amshi.

Ni ko nan na iso da Yar Tau motar sun durkusa garin gaisheni.

Amshi.

Ai a rannan ne naga kallon kallo suna kallonmu muna kallonsu.

Amshi.

Matanne su hudu matan kauye.

Amshi.

Wata Yar Fara dab daga gefen hanya ta bude bakin kallonmu.

Amshi.

Sun daura Dan zanensu na kauye.

Amshi.

Sun daura Dan zanensu na kauye.

Amshi.

Dan zanin kikit bai Kai ba a kokon guiwa.

Amshi.

Sai gasu sun durkusa garin gaishemu.

Amshi.

Su sun durkusa garin gaishemu a kas Basu San ba zanin ya balle.

Amshi.

Sai ga Yan kasa na gyaran takalma Yan sama na gyaran likkafa.

Amshi.

Kowane Yana wayonshi na leke....

Amshi.

Lallai abunda kakeji baka ganinshi ka ganshi da rana akwai mamaki.

Amshi.

Alhaji lallai rannan kai mamaki.

Amshi.

Alhaji lallai rannan kai mamaki.

Rubutawa

Hamisu Adamu Ganarali Funtua

Hussaini Dogo

Sarkin Yaki

Post a Comment

0 Comments