Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarkin Noman Garin Magaji

Citation: Bunguɗu, U.H. (2022). Waƙoƙin Amali  SububuAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Waƙoƙin Amali  Sububu

 Sarkin Noman Garin Magaji

Sunan sarkin noman Garin Magaji shi ne Majiro, Garin Magajin wani gari ne a cikin ƙaramar hukumar mulkin Sabon birni ta jihar Sakkwato.    

   

G/Waƙa : Da hanzarin noma nis san ka,

   : Taho gida rana ta hwaɗi,

   : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

 

Jagora : Ban hana yaro ba sai wuya ta,

   : hana mashi,

   : Rana tana da zahi.

’Y/Amshi  : In ba a daure ba ba ka jin,

   : Damma sun zo gida.

   : Da hanzarin[1] noma nis san ka,

   : Taho gida rana ta hwaɗi,

   : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

  

Jagora : Tadana[2] baƙin ka Majiro,

’Y/Amshi : Tahi sake dabara Amali,

   : Na gumza garkar gida,

   : Da hanzarin noma nis san ka,

   : Taho gida rana ta hwaɗi,

   : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

    

 Jagora : Allah ya maida aure aure,

   : Allah ka bar ma kowa ɗa nai,

   : Duɗ ɗan da kag ga an haihwa ma,

: In dai akwai yawancin rai,

: Sai ka ga ɗanai shi zan jiƙan ka.    

’Y/Amshi : Duw wanda kag ga yai jika,

  : Ya Tsuhwa[3] shi.

  : Da hanzarin noma nis san ka,

  : Taho gida rana ta hwaɗi,

  : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

 

 Jagora : Gwazza ku ƙara aure,

 ’Y/Amshi : Kaw wata rana a shirga[4] baƙi,

     : Ba matan tuwo,

        

 Jagora : Lalle gwarza[5] ku ƙara mata,

 ’Y/Amshi : Kaw wata rana a shirga baƙi,

  : Ba matan tuwo,

        

 Jagora : Mai mata guda ina kad darɓe,

  : Kazan kamar abokin gauro,

  : Dur randa ba ta nan,

 ’Y/Amshi : Ko waz zaka shiyak ka,

  : Ba ka cewa ɗebo mai ruwa,

  : Da hanzarin noma nis san ka,

  : Taho gida rana ta hwaɗi,

  : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

 

 Jagora : Ta tahi ta bag gida da kewa,

  : Ranan ko ka sawo dawo,  

’Y/Amshi : Damu sai an yi mai,

  : Da hanzarin noma nis san ka,

     : Taho gida rana ta hwaɗi,

     : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

 

Jagora : Ban hana yaro ba,

      : Sai wuya ta hana mai,

     : Rana tana da zahi,

   ’Y/Amshi : In ba a daure ba,

     : Ba ka jin damma sun zo gida,

         

     Jagora   : Sarkin noman Garin Magaji,

  ’Y/Amshi : Kai muka dubi kamar,

       : Watan sallah in ya hito,

     : Da hanzarin  noma nis san ka,

     : Taho gida rana ta hwaɗi,

     : Mu gaida Kartau mai gulbin hura,

   

Jagora : Ga sarkin noma za shi gona,

      : Ga jakki goma sha biyar ya koro,

      : Duk kowane da taki,

     : Ga kwando ya ciko da taki,

      : Ya ɗauka ya azo ga kainai,

      : Ga kalme ya saɓo da gitta,

    : Ga kwashe ya riƙo ga hannu,

    : Ga juji ya lago gaba nai,

    : Ga juji ya lago ga baya,

    : Ni dai na dabugo[6] gaba nai,

    : Ban san kan inda ya nuhwa ba,

    : Kuma nij jirkito shi baya,

    : Ban san kan inda yan nuhwa ba,

    : Kuma nij jirkito...,

    : Dub bai tanka ba ya yi shu,

    ‘Y/Amshi    : Duk ya cika hanya,

    : Kama da tantebur ta yo hawa.

    : Da hanzarin noma nis san ka,

     : Taho gida rana ta hwaɗi,

            : Mu gaida Kartau[7] mai gulbin hura.

Jagora     : Sullata nome karkara,

 ‘Y/Amshi     : Tahi duƙe ga daji,

    : Irin shanun nan hwarhwaru.

    : Da hanzarin noma nis san ka,

    : Taho gida rana ta hwaɗi,

    : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

 

Jagora      : Dojindo mai dakan ƙasa,

    ’Y/Amshi     : Tahi gilme[8] ga daji,

    : Kamar ana tuƙin jirgin ruwa,

    : Da hanzarin noma nis san ka,

    : Taho gida rana ta hwaɗi,

    : Mu gaida Kartau mai gulbin hura,

 

Jagora : Rana mai sa mutun la’ari gona,

     : Aiki ya barkace mai,

     : Rana mai kai mutun ga saiɓi[9] daji,

     : Har rai shi ɗora gumu,

     : In dai na kai duma ga gona,

     : Gwazza cilas ku sake Hausa,

     : Ina gaba Gwazza suna biya ta,

     : Ka ga ƙato shina jiɓi,

     : Cilas ka ga ƙato yana huka,

     ’Y/Amshi : Cilas ka ga hancin mutum,

  : Da tarsone ya zalzalo,

     : Da hanzarin noma nis san ka,

    : Taho gida rana ta hwaɗi,

    : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

 

Jagora : Ban hana yaro ba,

    : Sai wuya ta hana mai,

    : Rana tana da zahi,

‘Y/Amshi : In ba a daure ba ba ka jin damma,

    : Sun zo gida,

    : Da hanzarin noma nis san ka,

    : Taho gida rana ta hwaɗi,

    : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

 

Jagora : Ɗaukab bashi yana da ciwo,

     : Kuma ganoma[10] na da zahi,

     : Kalmen ga noma tambaɗaɗɗe,

     ‘Y/Amshi  : Kowas saba da shi,

     : Ana raina mai gaskiya,

     : Da hanzarin noma nis san ka,

     : Taho gida rana ta hwaɗi,

     : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

 

Jagora : Noma mun kai cikin gumi nai,

     : Bisa da zahi ƙasa da zahi,

     : Ga yunwa ga jiɓi da rana,

     : Ga Gwazza sun shigo ga gona,

     : Ga mata sun taho suna dubin,

     : Wada ƙatta ka gwabce kuyyai,

     : Abi kuyya a lukkume[11] ta,

     : Abi kuyye a sasume su,

     : A yi kuyye kamar rihewa.

‘Y/Amshi   : Kowace kuyya kamar gadar,

      : Mota an mulmulo,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaɗi,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

   

    Jagora    : Ba wada za kai ka ratsa gona,

      : Kuyye sun zan kama da Juna,

      : Ba wada zaka yi ka ƙetare su,

‘Y/Amshi   : Sai ka bi raɓin su,

      : Ko kana samun kwana gida,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaɗi,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

   

    Jagora    : Ban hana yaro ba,

      : Sai wuya ta hana mai,

      : Rana tana da zahi,

     ‘Y/Amshi    : In ba a daure ba ba ka jin,

      : Damma sun zo gida,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida  rana ta hwaɗi,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura,

  

   Jagora     : Yaro bai san kahon-kaho ba,

      : Kuma bai san caɓon-caɓo ba,

      : Kuma bai san gumin-gumi ba,

      : A kai jubuha[12] ba ka da hatsin ci,

      : Ba kada komi cikin ruhewa[13],

      : Bisa ruwa ƙasa ruwa,

     : Sannan ga noma bata tashi,

      : Sannan ciwon cikin,

      : Maza yake.

    ‘Y/Amshi    : Sai ka ga ƙato da shi da mai,

      : Ɗakinai an yi shu,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaɗi,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

  

   Jagora     : Ban hana yaro ba,

      : Sai wuya ta hana mai,

      : Rana tana da zahi,

    ‘Y/Amshi    : In ba a daure ba ba ka jin,

      : Damma sun zo gida,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaɗi,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

  

    Jagora    : Ba wada za kai ka ratsa gona,

      : Kuyye sun zan kama da juna,

      : Ba wada zakai ka ƙetare su,

    ‘Y/Amshi      : Sai kabi raɓin[14] su,

      : Ko kana samun kwana gida,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaɗi,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

   

    Jagora    : Ban hana yaro ba,

      : Sai wuya[15] ta hana mai,

      : Rana tana da zahi,

     ‘Y/Amshi   : In ba a daure ba ba ka jin,

     : Damma sun zo gida,

   

    Jagora    : Yaro bai san kahon-kaho ba,

      : Kuma bai san caɓon-caɓo ba,

      : Kuma bai san gumi-gumi ba,   

      : A kai jubuha ba ka da hatsin ci,   

      : Ba ka da komi cikin ruhewa,

      : Bisa ruwa ƙasa ruwa,

      : Sannan ga noma bata tashi,

      : Sannan ciwon cikin,

      : Maza ya kai,

   ‘Y/Amshi     : Sai ka ga ƙato da shi da mai,

      : Ɗakinai an yi shu,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaɗi[16],

   : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

   

    Jagora    : Ban hana yaro ba,

      : Sai wuya ta hana mai,

      : Rana tana da zahi,

     ‘Y/Amshi   : In ba a daure ba ba ka jin,

      : Damma sun zo gida,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaɗi,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

  

   Jagora     : Kaya ba ginin la’arin ganwo[17],

      : Zama da macce ba tsabacci,

      : Akwai wuya akwai ban haushi,

      : Ta na yi ma abin ganganci,

      : Ka hanƙure ka mai sai banza,

    : Ka hanƙure takaici,  

      : In ba ka tanka ba ka ji tsoro,

 ‘Y/Amshi : In ka tanka ta ɗora ce ma tsinannen

: maza,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaɗi,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

  

    Jagora    : Matar raggo kina da haushi,

      : Yunwa ta kwalkwale kin rame,  

      : Har kin bak kama da mata,

      : Ɗan kunkurun[18] kamar na mi ya ke?

     ‘Y/Amshi  : Ɗan kunkurun kamar biri na,

      : Tonon gujiya,

      : Da hanzarin noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaɗi,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

  

    Jagora    : Amali kiɗi babu wanda ban yi ba,

      : Bakin cin hwara dukiyata,

      : Na ci awaki da raguna da dawaki,

      : An ba mu dukiyar raƙumma,

      : Am ba mu hadda shanu,

      : Sauran mota a hwara sai man,

      : Komi ka ba ni duk cikin ƙari ne,

     ‘Y/Amshi     : Komi kab bani duk cikin ƙari kay yi

: man,

      : Da hanzarin noma nis san ka.

      : Taho gida rana ta hwaɗi,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

  :Jagora    : Amali zuga ba wadda,

      : Ban yi ba,

      : Bakin dai tamu hwara Hausa,

  : Na sa an ɗauki doguwa ta zanna,

      : Domin a tara gero,

      : Na sa an ɗauki aljana an ƙara,

      : Domin a hau da suna[19],

      : Na sa an ɗauke aljana na kauce,

      : Na bam mutun da kaya,

      : Wani ya ɗauki zakuma[20] ya tushe,

      : Ta zanne zuciya tai,

      : Ni ban ɗauka ba,

     ‘Y/Amshi    : Wanda yaɗ ɗauka shi ac ciki.

      : Da hanzarin[21] noma nis san ka,

      : Taho gida rana ta hwaɗi,

      : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

   Jagora:    : Albarkacin alu mai saje,

     : Albarkacin sahabi,

     : Kartau Allah ya ba ka albarkassu,

     : Mu ma mu samu albarkassu,  

     : Kahin[22] mu cimma albarkakka,

     : Da mu da kai da sauran taro,

     : Allah ka sa muna dacewa,

  ‘Y/Amshi    : Bagudu[23] indai kana da,

     : Alheri sai mun gani,

     : Da hanzarin noma nis san ka,

     : Taho gida rana ta hwaɗi,

     : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.

 

   Jagora     : Mamman Tukur waliyin Allah,

     : Allah shi ba ka albarkatai,

     : Mu ma mu samu albarkatai,

     : Kahin mu cimma albarkakka,

     : Da mu da kai da sauran taro,

     : Allah ka sa muna dacewa,

     : In dai kana da alheri,

    ‘Y/Amshi    : Bagudu in dai kana da,

     : Alheri sai mun gani,

     : Da hanzarin noma nis san ka,

     : Taho gida rana ta hwaɗi,

     : Mu gaida Kartau mai gulbin hura.[1]  Sauri

[2]  Tanada, wato ya yi tanadin wata kyauta da zai ba baƙinsa.

[3]  Tsufa

[4]  Yin abu da yawa, cikawa.

[5]  Manoma

[6]  Dubi na mamaki

[7]  Suna ne na wani mutum wanda wasu suke yi masa idan su ga yana da ƙoƙari wajen noma.

[8]  Karkace

[9]  Yin wasu ‘yan surutai kamar sambatu

[10]  Kodago, yin noma a gonar wani don a biya ka.

[11]  Dunƙulewa, rufewa

[12]  Lokacin yawan ruwan sama kamar watan Ogas.

[13]  Rumbun ajiyar hatsi.

[14]  Gefe

[15]  Zafin rana da wahalar aikin noma.

[16]  Idan rana ta yi Yamma har ta ɓace ba a ganinta.

[17]  Gammo don ɗaukar kaya.

[18]  Ƙugu/kwankwaso.

[19]  Wata tad ace ake yi idan ana son manomi ya yi fice kowa ya san shi ga maganar noma. A taƙaice dai ta zama ya tara kayan gona da yawa waɗanda ya noma.

[20]  Sunan aljana ne.

[21]  Wanda yake noma ba tsayawa ko yawan hutawa har ya yi aiki da yawa.

[22]  Kafin- mawaƙin ya yi amfani ne da Karin harshen Sakkwatanci.

[23]  Wanda bai tsoron wahala.

Post a Comment

0 Comments