Ticker

6/recent/ticker-posts

Rai Dangin Goro: Turken Raha a Wasu Waƙoƙin Noma na Makaɗa Amali Sububu

 Zamfara is located in the north-western part of northern Nigeria. It was one of the Hausa state refered to in history as banza bakwai . Allah in His infinite bounties has blessed Zamfara with vast fertile land suitable for agriculture. This led to the enhancement of the production of food crops like sorghum, millet, maize and cowpea. Cash crops in the form of cotton, calabash and ground nuts are also cultivated in commercial quantity. Zamfara is also endowed with quite a reasonable number of praise singers. Late Makaɗa Salihu Jankiɗi, Alhaji Musa Danƙwairo, Alhaji Sa’idu Faru, Abdun Inka Bakura are clear cut examples of traditional court singers. Zamfara being an agrarian population witnessed a good number of occupational singers who sing in praise of the farmers so as to motivate them to produce more. Makaɗa Amali Sububu stands tall amongts this category of singers. The saying goes, that ‘all works and no play make life dull.’ It is against this backdrop that this paper intends to explore the theme of pleasantries, raha in some of the farming songs of the singer. The methodology to be adhered to is attempts to listen to some of the farming songs with a view to identifying the theme of pleasntries therein and make expositions on it. The paper has come to the conclusion that Amali Sububu is such an endowed singer that uses lots of pleasanatries in the songs he composes for farmers. This he does to arouse amusement in the minds of his heroes so as to ward away fatigue incured after the days’ hard work at the farm.

noma

Rai Dangin Goro: Turken Raha a Wasu Waƙoƙin Noma na Makaɗa Amali Sububu

Dr. MUSA FADAMA GUMMI
Email: gfmusa24@gmail.com
Gsm No.: 07065635983

 

Dr. ABDULLAHI SARKIN GULBI
Email: asgulbi@gmail.com
Gsm. No.: 08089949294

 

Tsakure

 

Zamfara wani yanki ne na ƙasar Hausa da yake shimfiɗe a yankin arewa maso yamma na ƙasar Nijeriya. A wannan yanki ne aka sami daula ta ƙasar Hausa da aka saka a cikin jerin banza kawai. Allah ya albarkaci yankin Zamfara da albarkar ƙasa niimtacciya, wadda ta dace da noman albarkatun gona irin dawa da gero da masara da gyaɗa da auduga da sauransu. Tare da haka yankin ya shahara a ɓangaren samar da shahararru kuma haziƙan makaɗa da mawaƙa na ƙasar Hausa. Marigayi Salihu Jankiɗi da Alhaji Musa Ɗanƙwairo da Alhaji Sa’idu Faru, da Abdun Inka Bakura da sauransu makaɗa ne na fada. Kasancewar Zamfara yankin da noma ne ya sa ake da makaɗa da mawaƙa da suke koɗa manoma domin cusa maso karsashi da himmatuwa ga aikinsu. A rukunin mawaƙan noma na Zamfara Makaɗa Mamman Amali Sububu fitacce ne musamman idan aka yi la’akari da irin fasahar da Allah ya ba shi. Ƙudurin wannan maƙala shi ne ta zaƙulo wasu daga cikin waƙoƙin noma na Makaɗa Amali Sububu da nufin lalubo turken raha a cikinsu musamman da yake Bahaushe na cewa ‘rai dangin goro ne.’ A wannan muƙala, za a saurari kasakasai na waƙoƙin makaɗin da nufin lalubu ko yin duba zuwa ga ƙaramin saƙo na raha da wasu waƙoƙin suka ƙunsa sannan a yi sharhi a kansu. Muƙalar ta gano cewa makaɗa Amali Sububu makaɗi ne da ke yawan saka raha a cikin waƙoƙinsa na noma domin saka nishaɗi da annashuwa sosai a cikinsu ta yadda saƙonsa zai shiga zukatan masu saurarensa cikin sauƙi.

 

1.0 GABATARWA

Waƙa baka aba ce daɗaɗɗiya da ta rayu tun zamani mai nisa da ya shuɗe, take kuma daɗa bunƙasa da cigaba har wannan zamani[1] kuma a bisa hange, za ta cigaba har wani zamani na gaba. Noma daɗaɗɗiyar sana’a ce da Hausawa suka daɗe suna aiwatarwa a matsayin hanyar neman abinci da samun kuɗin shiga don biyan buƙatun yau da kullum. Wannan ne ya sanya Hausawa kan ce ‘na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar. Duba ga irin matsayin wannan sana’a a al’adun Hausawa, ba abin mamaki ba ne idan aka sami wani rukuni na makaɗa da mawaƙan Hausa su karkata ga yin waƙoƙi na noma domin su ƙara wa manoma ƙwarin guiwa, su duƙufa sosai ga sanaarsu,domin a sami bunƙasa ko wadatar abinci da kuma haɓaka tattalin arzikin al’umma. Da haka ne aka sami makaɗan noma na Hausa da misalin ya haɗa da makaɗa Illon Kalgo da makaɗa Abu Ɗankurma Maru da makaɗa Mamman Yaro Horo da makaɗa Daudun Kiɗa Janbaƙo da gwarzon wannan muƙala, makaɗa Mammam Amali Sububu. Aikin noma aba ne mai matuƙar wahala da akan aiwatar yayin da ake duƙe kuma cikin rana, komai zafinta. Laakari da irin wahalar da ke tattare da noma da kuma tarin gajiya da ke tattare ga mai yin sa, a tunanina, ya sa makaɗan noma suke saka raha a cikin waƙoƙinsu domin su saka annashuwa da jin daɗi a zukatan manoma, su shaƙatu, su nishaɗantu, don su manta da wahalar da suke sha a gona. Wannan zai sa zuciyarsu ta huce, su sami ƙwarin guiwa ta yadda idan gari ya waye za su ƙara azama zuwa gonakinsu. Makaɗa da mawaƙan noma galibi suna faɗar maganganu na ban dariya don saka raha a waƙoƙinsu. Irin waɗannan kalamai ne na raha wannan muƙala take son ta lalubo, kamar yadda makaɗa Mamman Amali Sububu ya yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa. Gabanin yin haka, ya dace a kawo ma’anonin tubulan da suka gina taken wannan muƙala.

2.0 Ma’anonin Tubulan Take

 Tubulan take na nufin muhimman kalmomi da aka yi amfani da su wajen gina taken wannan muƙala. Kalmomi muhimmai da suka gina taken muƙalar su ne turke da raha da waƙoƙi. Wannan kalmomin ne za a ɗauka ɗaya bayan ɗaya a kawo ma’anoninsu.

2.1 Turke

Kalmar turke Bahaushiya ce bisa asali. Ma’anarta kamar yadda CNHN, (2006:446) suka faɗa a Ƙamusun Hausa, shi ne guntun ice da ake kafawa don ɗaure dabba a jikinsa. Haka ma yana iya ɗaukar ma’anar wurin yada zangon sojoji ko mayaƙa. A fagen nazarin waƙa kuwa, turke daidai yake da jigo. Kalmar Jigo ana amfani da ita a fagen nazarin waƙa rubutacciya. Turke kuwa, ana amfani da shi a nazarin waƙar baka. Gusau, (2003:28) ya faɗa cewa abin da ake nufi da turke shi ne manufar waƙa. Manufar kuwa shi ne abin da waƙa take magana a kansa. Wannan yakan ratsa waƙar tun daga farkonta har ya zuwa ƙarshenta. La’akari da abin da masanin ya kawo, ana iya cewa turke shi ne saƙon da waƙa take son ta isar zuwa mai sauraro. Akwai babban turke, akwai kuma ƙanana waɗanda mawaƙi yakan kawo domin ya isar da babban saƙo da ke cikin waƙa.

 

2.2 Raha

Bisa asali, kalmar raha an aro ta ne daga harshen Larabci. A cikin Larabcin, kalmar na nufin tafin hannu. Haka ma takan ɗauki ma’anar lokacin hutawa da nishaɗantuwa.[2] Ga dukkan alama, da ma’anarta ta biyu kalmar ta shigo Hausa. Abubakar (2015: 401) ya faɗa cewa a Hausa kalmar tana nufin hirar jin daɗi da sa dariya. CNHN, (2006:364) a Ƙamusun Hausa cewa suka yi raha na nufin walwala ko faraa. A haka, ana iya cewa raha kalma ce da take nufin hira ko kalamai da ke sa jin daɗi da fara’a a zukata, da ka iya saka mutum walwala, har ya yi dariya da annashuwa.

2.3 Waƙa

Waƙoƙi kalmar jami ce wadda tilonta ita ce waƙa. Waƙa kuwa a Hausa nau’i biyu ce. Akwai rubutacciyar waƙa da kuma waƙar baka. Wannan muƙala ta karkata kan waƙar baka don haka ita za a bayyana. Bisa ma’ana Yahya (1997)[3] yana kallon waƙa a matsayin tsararriyar maganar hikima da ta ƙunshi saƙo cikin zaɓaɓɓun kalmomi da aka auna domin maganar ta reru ba faɗuwa kurum ba. Masanin ya ce ita waƙar baka ana rera magana ne tare da amfani da kayan kiɗa bayan zaɓen kalmomi da tsara su .A wurin Gusau (2003)[4] waƙar baka wani zance ne shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ka’idojin tsari da daidatawa a rere cikin sautin murya da amsa-amon kari da kiɗa da ‘Yan amshi. Idan aka yi la’akari da abin da masana suka faɗa dangane da abin da suke ganin ake kira waƙar baka, to ana iya cewa waƙar baka wani zance ne na hikima ko magana wadda aka shirya ta hanyar tsara kalmomi zaɓaɓɓu kuma zaunannu, a rera su gutsure-gutsure cikin azanci da salon armashi, tare da yin kiɗa, da ‘Yan amshi, da nufin isar da saƙo.

3.0 Taƙaiatccen Tarihin Mawaƙi

An haifi makaɗa Mammam Amali a ƙauyen Sububu wadda take cikin gundumar Ƙaya a masarautar Maradun da ke cikin jihar Zamfara. An haife shi ne a wajajen shekara ta 1945.[5] Sunan mahaifinsa Malam Aliyu, mahaifiyarsa kuwa ita ce Ramatu. Dukkan mahaifan makaɗa Amali Zamfarawa ne. Mammam Amali, ya sami sunan Amali ne daga wurin gwaggonsa. Hakan kuwa ya faru ne a lokacin da aka je sanar da ita cewa matar ƙanenta ta haifi ɗa namiji. Nan take sai ta ce “an sami Amali”[6] Wannan sunan ne ya kasance kaƙabin Amali, baya ga sunansa na yanka, wato Muhammadu. Makaɗa Mamman Amali ya yi karatun allo wajen malaminsa mai suna malam Muhammadu Dodo. Bai sami damar yin karatun boko ba saboda a wannan lokaci babu makarantar boko a ƙauyensu, ga kuma ƙyamar da mutane suke yi wa boko a wannan lokaci. Sana’ar da mahaifinsa yake aiwatarwa ita ce sana’ar noma. Baya ga sana’ar noma, Malam Aliyu yana kuma yin sana’ar sassaƙa. Ya ƙware sosai wajen sassaƙa ƙotoci daban-daban na kayan aikin gona. Makaɗa Amali Sububu ya buɗe ido ne da sana’ar noma wadda ita ce mahaifinsa ya fi yi. Amali ya yi fice a cikin sana’ar ta noma musamman a tsakanin tsararsa. A duk lokacin da ake noman gayya, Amali na daga cikin waɗanda suka fi fice. Makaɗa Mamman Amali bai gadi kiɗa daga wajen mahaifinsa ba. Ya gadi kiɗa ne a wajen kakansa ta gefen uwa, wanda ake kira Narini. Narini kuwa makaɗin ganga ne ba duma ba wanda shi ne kayan kiɗan Amali. Mamman Amali mutum ne da Allah ya yi wa baiwa t3a sarrafa kalmomi cikin waƙa. Amali ya tashi da wannan baiwar tun yana ɗan shekara goma sha ɗaya zuwa sha biyu[7] Wannan baiwar ce ta sa makaɗa Amali bai yi barantaka wajen kowane makaɗi ba, ballantana ya koya wurin wani.

Gabanin shigar makaɗa Mamman Amali ga lamarin waƙa gadan-gadan, ya ƙware wajen lamarin kirarin noma irin wanda aka fi sani da tama. Wannan ne ya taimaka masa wajen yin wasu ‘yan waƙoƙi na yarinta. Hannun wannan bincike bai kai ga waɗannan waƙoƙi na yarinta da makaɗa Mamman Amali ya yi ba don haka ba za a sami damar ba da misalansu ba.

Makaɗa Mammam Amali ya fara sha’anin waƙa ne gadan-gadan ta hanyar yi wa gwagware waƙa. Ya kuwa fara ne da yi wa wani gwauro, Bafulatani[8] waƙa. Sunansa shi ne Dudu. Gindin waƙar shi ne:

 Ni na ka yi ma,

 Gwabro barka da wulaƙanci.

 (Makaɗa Mamman Amali Sububu: Waƙar gwauro.)

 

Makaɗa Mamman Amali dai makaɗin duma ne. Yana da yaransa waɗanda su ke kaɗa duma su kuma yi masa amshi. Daga cikin yaran akwai Abu Amali wanda ƙane ne a wajen makaɗin. Labaran yaronsa ne mai amshin waƙa, haka ma Usman da Sada suna daga cikin yaransa. Makwashe kuwa shi ne sanƙira ko ɗan mu’abban makaɗa Amali. A hirar da na yi da Muhammadu Naharɗo Sububu ya nuna man cewa Amali ya rasu ne gabanin ƙirƙiri jihar zamfara. Ibrahim Ahmad Isa, ya tabbatar da wannan zance cewa, Amali ya rasu ne shekara biyu gabanin ƙirƙiro jihar Zamfara. Wannan yana daidai da 1994 domin an ƙirƙiro jihar Zamfara ne a 1996. Makaɗa Mamman Amali ya rasu a ranar Alhamis, uku ga watan Nuwamba, shekara ta 1994 (03/11/1994) sakamakon faɗowa da ya yi daga cikin mota yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida, bayan kammala ziyarar kiɗa a garin Gangara.[9]

 

4.0 Turken Raha A Wasu Waƙoƙin Noma Na Amali

Raha ita ce hira ko faɗar kalamai masu sa jin daɗi da fara’a a zukata, wanda ka iya saka mutum ya yi walwala da annashuwa har ma da sa dariya. A nan, za a shiga ne a cikin waƙoƙin noma na makaɗa Mamman Amali Sububu da nufin fito da turken raha a cikinsu. Abin nufi shi ne za a kalli ɗiyan waƙa da suke ba da nishaɗi da ban dariya a cikin waƙoƙin nasa. Hakan zai zo ta hanyar la’akari da batutuwa daban-daban waɗanda makɗin ya tsara hikimominsa a cikin raha. Akwai kalamai na raha da suka jiɓinci rago (malalaci) da kuma raha da ta jiɓinci tagomashi da manoma suke da shi ga mata da yadda makaɗa ya saka batun rashi ko talauci a cikin raha wasu ɗiya waƙa tasa. Baya ga haka, makaɗa Mamman Amali Sububu ya baje koyin hikimarsa ta saka zancen aure a cikin raha a wasu ɗiya da dama na waƙoƙiinsa. Duka waɗannan za a zaƙulo su a cikin waƙoƙimsa na noma.

 

4.1. Raha A Kan Rago (malalaci)

Rago shi ne malalaci ko mutum marar kuzari (CNHN, 2006:364). Aikin noma aba ne mai matuƙar wahala da a bisa alada akan aiwatar da shi ne a duƙe kuma cikin rana. Wannan ne ya sanya Hausawa suke yi masa kirari da “Na duƙe tsohon ciniki...... Rashin juriya da shan wannan wahala ta noma ko rashin kuzari da azma ga aikin shi ke sa a gano rago ko malalaci ga sha’anin noma. Ɗabiar raganci ko lalaci abar ƙyama ce a tsakanin Hausawa don haka ɗabi’a ce da ba a son mai yin ta.[10] Duba da irin matsayin lalaci da ragonci ke da ita a tsakanin al’umma ne ya sa makaɗa Mamman Amali ya saka yadda rayuwar rago kan kasance sakamakon rashin juriyarsa ga aikoi gona.

Na farko za a duba waƙar Isah Maikware, inda makaɗin ya kawo dogon zance cikin azanci a daidai ɗiyan waƙa da yake cewa:

             Jagora: Raggo yana ganin Mai kandu na daka,

 Raggo yana ganin tcadadda na daka,

 Sai ta yi rangaji ta yi yabƙi nan haka,

 Yabƙi ɗai takai,

 Yanga ɗai takai,

 Yat tambaye ni yac ce yabƙin mi takai,

 Yabƙi takai mijinta ta dai gane mashi,

 Ta dai sami gabanai rana ta dushe,

 Bakin ƙarhe bakwai,

 Kai wa ƙarhe takwas,

 Bakin ƙarhe tara,

 ‘Yan Amshi: Kahin a kai ga sha biyu,

 Ya sha nakiya.

 Gindin Waƙa: Zahin rana bai tauye ka ba,

 Sabon goje,

 Isa Mai Kware.

 Jagora: Ko kahin a kai ga sha biyu,

 Duk an durmuya.

 ‘Y/amshi: Ko kahin a kai ga sha biyu,

 Hay ya sa giya.

 

A waɗannan ɗiyan waƙa da aka kawo, makaɗa Amali, cikin nishaɗi da ban dariya, yana jawo hankalin mutane ne da su tashi tsaye, su zage dantse, su duƙufa ga aikin noma idan dai suna son su sami cikakken tagomashi daga wajen matansu. Sha’awa tana zuwa ne bayan ƙoshi, don haka lallai ne mutane su samar wa iyali cimaka, idan suna son su yi shauƙinsu ko su kwaɗaito da kusantarsu da nuna masu matuƙar soyayya. Ganin wannan halayya da matar manomi ta nuna a cikin ɗiyan waƙa da suka gabata, sai rago ya ɗauki alwashi na yin aiki tuƙuru kamar yadda Amali ya faɗa cewa:

 Jagora: Raggo yay yi tagumi,

 Ya zura hwarce baka,

 Yac ce gaya wa kowa,

 Bana aiki nikai,

 In na yi jijjihi sai rana ta dushe,

 In nit taho gida in riƙa saƙak kaba,

 Wannan abin da kowa yaka so in yi shi

 In ya yi macce ba shi da haushin runguma,

 ‘Y/amshi: Dut ta rungume shi,

 Ya yi kamay ya tauwaha.

 Gindin waƙa: Zahin rana bai tauye ka ba,

 Sabon goje Isa Mai Kware

 Takidi: Dut ta adana shi,

 Ya yi kamad dai bai da rai.

 Gindin waƙa: Zahin rana bai tauye ka ba,

 Sabon goje Isa Mai Kware.

A nan za a ga makaɗa Amali Sububu ya ja hankalin rago da sakin jiki, ya duƙufa wajen aikin noma yadda zai sami cikakkiyar kulawa da nuna ƙauna daga wajen iyali. Rago kuwa a cikin hoton bayani, ya sha alwashin ba za a bar sa a baya ba. Makaɗin ya kawo zancen ne domin ya saka nishaɗi mai yawa a zukatan masu saurarensa. A ƙoƙarinsa na cigaba da saka nishaɗi da annushuwa a zukata da fuskokin masu saurarensa, Amali ya ci gaba da faɗa a wani ɗa na waƙar cewa:

 Jagora: Damana ta dawo,

 Raggo na kuka,

 Ya zo shi yi noma

 Rana ta hana,

 Ya dawo gida,

 Ba tsabad daka,

 Ba kuɗɗin awo,

 Ya koma bara,

 Mata sun hana,

 Kowak kirɓa,

 Gona za a yi,

 Tsohon shegen,

 Kuka yac tcira,

 Raggo ya ce,

 Wayyo Allah,

 Wayyo Annabi,

 Wayyo yunwa,

 Wai mi yai maki

 ‘Y/amshi: Koko yunwa ji mai za ta yi.

 Gindin waƙa: Zahin rana bai tauye ka ba,

 Sabon goje Isa Mai Kware.

 

A nishaɗance, makaɗa Mamman Amali ya nuna yadda zafin rana ya hana rago samun sukuni a aikin noma duk da kuwa alwashin da ya ɗauka na yin aiki tuƙuru. Haka ma ya kawo illa ko sakamakon rashin dagewa a nemi na kai, wanda ka iya kai mutum ga shiga matsanancin hali na rashi. Irin wannan ɗabi’a ta ragonci kan haifar da mutuwar zuciya da ke kai mutum ga bara. Bara kuwa ba ta da tabbas domin ba dole ba ne cewa sai mutum ya sami biyan buƙata. Dubi yadda Amali ya fito ƙarara da irin yadda rago ya yi raki sakamakon shiga halin yunwa. A cikin nishaɗi, an faɗakar da al’umma abin da za a iya fuskanta idan aka kasa jure wahalar noma, domin sai an sha wuya akan sha daɗi, a sami abinci ya wadata. Sakamakon rashin yinsa kuwa shi ne yunwa da talauci.

Duk dai domin makaɗa ya yi wa gwarazansa nuni cikin nishaɗi, a ɗa na waƙar, ya shammaci matar rago da cewa:

 Jagora: Matar raggo kina da haushi,

 Yunwa ta ƙwaƙule ki ke rame,

 Hak ke bak kama da mata,

 Ɗan kunkurun kaman nami yake,

 Ɗan kunkuru kamab biri na tonon gujjiya.

 

A nan, makaɗa Amali kashedi yake yi wa mata da kada su auri mutum rago, wanda bai iya taɓuka komai domin ya nemi na kansa. Dalilinsa kuwa shi ne matar rago cike take da haushi. Duk mai jin yunwa koyaushe cikin rafin rai yake[11]. Sakamakon rashin ƙoshi zai saka rama a jikin matar rago har ya kasance ta fita kamannunta. Wannan zai sa ta lalace, ta bushe har a daina shawarta.

 

4.2 Raha A Kan Tagomashin Manoma

Noma sana’a ce da take samar da abinci da kuma kuɗaɗen shiga ga masu aiwatar da ita. Wannan ne ya sanya Hausawa suke yi masa da kirari “Noma yanke talauci “. Manoma waɗanda suka shahara za a tarar su ne suke da wadata ta abinci da dabbobi da kuɗaɗe na biyan buƙatun yau da kullum. Wannan wadatar abinci da suke da ita shi ya sanya suke da tagomashi a wajen mata. Kowace mace in dai son ranta ne tana son ta auri manomin kirki domin ko ba komai zai iya ɗaukar ɗawainiyarta da lalurorinta. Irin wannan tagomashi da manoman suke da shi ne musamman a karkara, makaɗa Mamman Amali Sububu ya kawo a cikin raha.

Makaɗa Mamman Amali ya zayyana irin tagomashin da gwarazan noma suke samu a wajen mata. Gurin kowace ‘ya mace ne ta sami mijin da zai kula da ita ta hanyar kiyaye buƙatunta na ci da sha da sauran buƙatu na rayuwa. Wannan ne ya sanya mata har ɗoki su ke yi su ga sun sami namijin da zai iya yi masu haka. Cikin raha da nishaɗi, Amali ya kawo wannan a ɗan waƙa na gaba da ke cewa:

 Jagora: Yarinya da tag ga Isa gona,

 Yana ta noma ya sha gangara,

 Tay yi duƙe tac ce Isa mi akai,

 Yaw waiwayo ta yac ce mata aiki mu kai,

 Ko kana kwaɗaina bana amre mukai,

 Ko ba ka kwaɗaina kuma shi za a yi,

 Abin da nih hi so in riƙa ƙaton dami,

 In yo sussuka in sheƙe da kyau,

 In auna da kyau in surhe da kyau,

 In wanke da kyau in ribɗe da kyau, , Sai na yi tankaɗe in aza sanwad dawo,

 In nig gamo daka in yi zaman tankaɗa,

 In dunhe da kyau in kirɓe da kyau,

 In dame da kyau in nid dame da kyau,

 Ka zo ka sha hura mu yi ta zaman duniya,

 Yac ce wuce-wuce ga wata can ta wuce,

 Waccan da wuce haka nan tac ce mani,

 Ke ma da kit taho haka nan kic ce mani,

 Dubu kamak ki sun ce haka nan sun wuce,

 In na biye ku ɓata biɗata za ni yi,

 Dum mai biye ma macce shiga kunya ya kai,

 Sai tay yi zamne tac ce Isan Dukkuma,

 Sabon yaro mai kyawon shiri,

 Ka yi min gahwara,x2

 Isa ɗan Buwai.

 ‘Y/amshi: Yaw waiwayo ta yac ce ya yahe mata

 Gindin waƙa: Zahin rana bai tauye ka ba,

 Sabon goje Isa Mai Kware.

 

Amali ya zayyana hoto cikin bayani yadda mata suke kwaɗaituwa ga auren gwarazan da suka himmatu wajen aikin noma suka kuma tara hatsi a rumbunansu. Ko baya ga wannan, dubi yadda ya tsara yadda mata suke sarrafa gero, su yi fura, wani nau’in abincin gargajiya da ake sha.

Kamar yadda muka gani a wannan waƙa ta Isa Mai Kware, makaɗa Amali ya nuna ƙwarewa ta hanyar zayyanawa a cikin raha da nishaɗi yadda manoma suke da tagomashi ga mata. Ba wannan waƙa kaɗai ke ƙunshe da irin wannan turke na raha ba. A cikin waƙar Sarkin noma Majiro na Garin Magaji, ƙaramar hukumar mulki ta Sabon Birni a jihar Sakkwato, Amali ya yi amfani da turken raha domin isar da saƙonsa cikin nishaɗi. A wani ɗa na wannan waƙar, Amali na cewa:

 

 Jagora: Gwaraza ku ƙara arme,

 Lallai gwaraza ku ƙara mata,

 Mai mata guda ina kad darɓe,

 Ka zan kama da gwabro,

 Dur rad da ba ta nan,

 Ba ka cewa ɗebo mai ruwa.

 Gindin waƙa: Da hanzarin noma nis san shi,

 Taho gida rana ta hwaɗi,

 Mu gai da kartau mai gulbin hura.

Makaɗa Amali shawara ya ba gwarazan noma da su ƙara mata domin mai mata guda abokin gwauro ne. Don shawarar tasa ta karɓu, a nishaɗance ya nuna illar zama da mata ɗaya. Duk ranar da ta yi tafiya, to mutum ya zama gwauro.

 

4.3 Raha A Kan Rashi ko Talauci

Talauci hali ne na rashin wadata. Hali ne na ƙarancin abinci da ƙarancin kuɗi da zai sa mutum ya kasa aiwatar da buƙatunsa na yau da kullum. Irin wannan yanayi abu ne da ya shafi alummomui daban-daban musamman idan aka sami wani lokaci da ruwan sama ya yi ƙaranci sosai ta yadda ba a sami damar noma abinci sosai ba. A irin wannan yanayi, idan aka kai wajajen watan Agusta na shekarar nasara, rayuwa kan shiga halin wahala sakamakon ƙarewar hatsin da aka noma bara, ga kuma wanda aka shuka a shekarar bana bai nuna ba. Irin wannan yanayi ne makaɗa Mamman Amali ya kawo hotonsa a cikin raha.

A ƙoƙarin bayyana mawuyacin hali a akan shiga, Amali a wani ɗa na wannan waƙa ya faɗa:

 

 Jagora: Yaro bai san kahwan kaho ba,

 Kuma bai san caɓon caɓo ba,

 Kuma bai san gumin gumi ba,

 A kai jubuha ba ka da hatcin ci,

 Ba ka da komi cikin ruhewa,

 Bisa ruwa ƙasa ruwa,

 Sannan ga- noma ba ya tashi,

 Sannan ciwon cikin maza yake.

 ‘Yan amshi: Sai ka ga ƙato da shi da mai ɗaki,

 Duk an yi shu.

 Gindin waƙa: Da hanzarin noma nis san shi,

 Taho gida rana ta hwaɗi,

 Mu gai da kartau mai gulbin hura.

 

Amali a cikin raha ya kawo hoton wani yanayi na halin talauci da ake shiga musamman a lokacin marka. Hatsin da yake rumbu ya ƙare, wanda aka shuka a gona kuma bai nuna ba. Sanaar da aikin ƙwadago na aikin gona kuma ya kwanta domin kusan an gama nome-nome sai jiran nunar amfanin gona. A yanayin irin wannan, duk manomin da bai ajiye cimaka a rumbu ba, yana cikin muwuyacin halin ƙaƙa-ni-ka-yi. Duk da kasancewar yanayin ba mai daɗi ba ne, kawo sa a cikin waƙa yana tunatar da manoma cikin raha cewa, su yi kyakkyawan tanadi domin irin haka. A wani ɗa na waƙa, Amali ya sake kawo hali da maras abinci ke shiga dangane da zamantakewarsa da iyali. Amali yana cewa:

 

 Jagora: Kaya sa ganin la’arin ganwo,

 Zama da macce ba tsabac ci,

 Akwai wuya akwai ban haushi,

 Tana yi ma abin ganganci,

 Ka hanƙure ka maisai banza,

 Ka hanƙure takaici,

 In ba ka tanka ba ka yi tsoro,

 In ka tanka ta ɗora ce ma tcinannen maza.

 Gindin waƙa: Da hanzarin noma nis san shi,

 Taho gida rana ta hwaɗi,

 Mu gai da kartau mai gulbin hura.

 

Makaɗa ya faɗakar da manoma cewa zama da mace ba tare da an mallaki abin saka wa baki ba, yana jawo raini tsakanin maigida da matarsa. Domin guje wa fuskantar ganganci da raini, lallai ne maza su tashi tsayin daka su noma abinci domin kore wa bakunansu ƙuda.

 

4.4 Raha A Kan Aure

Aure muhimmiyar al’ada ce ta Hausawa tun gabanin su haɗu da wasu al’adu ko dai na gabas ko na yammacin duniya. A Bahaushiyae al’ada, ba a aminta da zamantakewa tsakanin namiji da mace wacce za ta kai ga saduwa face akwai aure tsakanin. Aure dangantaka ce tsakanin namiji da mace ta hanyar shari’a. (CNHN, 2006:22)

A cikin waƙar da makaɗa Amali ya yi wa Aikau Sububu, ya yi amfani da raha domin isar da saƙonsa cikin nishaɗi wato abin da Bahaushe ke cewa nuni cikin nishaɗi. A ciki, Amali na cewa:

 

 Jogora: Kyawon yaro shi armi yarinya,

 Shi ak kyau hakan ga dai,

 Kyawon yaro shi armi yarinya,

 Ga kyawonta ga hali,

 Kyawon yaro ya armi yarinya,

 Ga kyawo da natsuwa,

 Kuma dus sad da ya shigo ɗaki,

 Ta zamna mashi gado,

 Kuma dus sad da tag ga nai ɗakin,

 Ga shanya tana yi mai,

 Sai ta yi ban hihhiki,

 Ta kyafta idonta ta ɗauka masa gira,

 In wani wayo gare shi ta amshe,

 Rannan ba shi da shiya,

 Sai ka ga yaro shina rawa da haɓa,

 Ta hyaɗa shi ga gado,

 Ba ta bari nai hita cikin ɗaki,

 Sai ta ƙoshi da shiya,

 To ko ta bas shi ya hito ɗaki,

 Ba shawad da zai gani.

 ‘Y/amshi: Ai duw wata shawa tana cikin ɗakin,

 Dawowa yakai ciki.

 Gindinwaƙa: Ya riƙa noma da gaskiya Na bakwai,

 Bai saba ba da zama,

 Aikau jikan Tayawa ɗan Mamman,

 Kunkelin fashin fasa.

 

A nan, Amali yana tsokaci ne kan cewa aba ne kyau saurayi ya auri budurwa kyakkywa wadda take hali na kirki. A haka, sai a sami cikakkiyar soyayya da za ta haifar da zamantakewa mai kyau. Wannan ya zo ne a cikin waƙar domin a ƙara wa hira kauri, a sami zuzzurfan nishaɗi da zai sa a manta da wahalar da aka sha a gona. Domin makaɗa Amali ya ƙara wa yammacin armashi da annashuwa, ya kawo a wani ɗa na waƙar cewa:

 Jagora: Kyawon yaro ya armi yarinya,

 Shi ak kyau hakan ga dai,

 Baran wani ya kwashi raƙumad daji,

 Ta canye masa hatci,

 Ba ta da kyau ta kare ga kunkuru,

 Ga ƙaton ciki kuma,

 Ga ta da ɗan kai kamar na buzuzu,

 Ga hanci da majina,

 Wannan ko shan dakanta cuta ne,

 Balle rungumar dare.

 Gindin waƙa: Ya riƙa noma da gaskiya Na bakwai,

 Bai saba ba da zama,

 Aikau jikan Tayawa ɗan Mamman,

 Kunkelin fashin ƙasa.

 

Amali shawara yake ba manoma da duk masu saurarensa idan za su yi aure, su darje su zaɓi kyakkyawar mace mai tsafta kuma ga halin kirki. Wannan ne zai sa zamantakewa tsakaninsu ta yi armashi.

 

5.0 Sakamakon Bincike

 Zamfara wani yanki na ƙasar Hausa da ake samun makaɗan baka, musamman na gargajiya masu tarin yawa. Daga cikinsu akwai makaɗan noma daban-daban. Makaɗa Mamman Amali Sububu yana ɗaya daga cikin mawaƙan noma da suka fito daga Zamfara. Makaɗa Amali a nasa zamani, ya ɗaukaka game da waƙar noma duk da cewa wasu ba su tantance da shi ba sai bayan ya ƙaura. Amali makaɗi ne mai fasaha wanda Allah ya ba hikimar shiryawa da tsara kalmomi su reru, cikin armashi, ba faɗa kawai ba. Makaɗi ne da ya shahara wajen amfani da raha wajen isar da saƙonsa ga waɗanda yake yi wa waƙa, har da sauran jamaa masu saurarensa.

 

Yawan saka raha da yake yi a waƙoƙinsa na noma ba ya rasa nasaba da kasancewar noma aiki mai matuƙar wahala da tattara wa mai yin sa gajiya da kasala mai yawa bayan an dawo gida da yamma. Da yake galibi makaɗa sun fi kai hirar kiɗa da dare a gidajen manoma, akwai buƙatar a saka nishaɗi a cikin zukatan manoman ta hanyar saka maganganu masu ban dariya a cikin waƙoƙin. Yin haka, zai rage masu gajiyar da suka kwaso a gona, ya sa su manta da wahalar da suka sha. Hakan zai sa gobe su tashi da azma, da shauƙin komawa wajen aikisu. Ko baya ga haka, ɗaya daga cikin muhimmancin waƙoƙin noma shi ne zuga manoma da tsima su domin su duƙufa ga aikinsu na noma.

 

Saka raha a cikin waƙoƙin noma na da matuƙar faida wajen sanya manoma su duƙufa ga aikinsu. Haka zai sa ƙasa ta wadatu da abinci, a kore yunwa da talauci. Amfani da salon ‘nuni cikin nishaɗi’ wata dabara ce da makaɗa Amali Sububu yake amfani da ita wajen farkar da manoma, ya ingiza su, su himmatu ga sana’arsu. Wannan babbar dabara ce ta miƙa saƙo cikin sauƙi, ya kuma yi saurin ratsawa da shiga zukatan mai sauraro. Baya ga haka, saka raha a cikin waƙa musamman ta noma na ƙara wa waƙar armashi. A tunanin wannan muƙala, waɗannan wasu muhimman dalilai ne da ke sa a saka raha a cikin waƙoƙin noma kamar yadda makaɗa Mamman Amali ya yi a cikin waƙoƙinsa na noma.

 

A akasarin misalan raha da aka kawo a cikin waƙoƙin Mamman Amali, za a ga kalaman na raha an ɗora su ne a kan rayuwar mutanen karkara musamman batun zamantakewar aure. Wannan ya kasance haka ne domin kaso mai yawa na manoma suna zaune ne a karkara kuma rayuwarsu irin ta mazauna karkara ce. A karkara ba a faye samun abubuwan da ke kawo nishaɗi ba kamar yadda ake samu a birane. Lura da irin muhimmin matsayin da aure yake da shi a tsakanin al’ummar Hausawa da irin haƙin da alada da addinin Bahaushe suka ɗora a kan ma’aurata, ya sanya makaɗin a cikin raha yake jan hankalin manoma su tsare haƙin iyalansu na ciyarwa da biyan sauran buƙatu. Da haka ne za su sami tagomashi a wajen iyalansu. Wannan ne yasa makaɗin ya fi karkata ga sha’anin aure wajen nishaɗantar da mutane a cikin waƙoƙinsa.

 

Kammalawa

Wannan muƙala kamar yadda aka faɗa a baya kaɗan, wani yunƙuri ne na lalubu yadda Makaɗa Mamman Amali yake amfani da turken raha a cikin waƙoƙinsa na noma. Domin samun nasarar yin haka, an tattara kasakasai na waƙoƙin noma waɗanda makaɗin ya yi wa gwarazansa. Abin da muƙalar ta gano ya tabbatar da faɗar da Hauasawa da ke cewa, ‘rai dangin goro ruwa ake ba shi.’ Kamar yadda aka gani a waɗannan ɗiyan waƙa da aka kawo daga cikin wasu waƙoƙin noma na makaɗa Mamman Amali, rayuwa na buƙatar sakewa ta fuskar nishaɗi da annashuwa. Duba ga irin wahalar da ke tattare da aikin noma, akwai buƙatar idan aka dawo daga gona a sami wata kafa ta samun nishaɗi. Waƙoƙin noma daban-daban na makaɗa Mamman Amali cike suke da kalamai da zantutuka cikin azanci. Haƙiƙa sauraren irin waɗannan kalamai na saka jin daɗi da raha da annashuwa har ta kai mutum ya yi dariya da ƙyalƙatawa. Wannan zai sa cikin sauƙi da hanzari, gajiyar da aka kwaso daga gona ta huce. Da haka sai a sami ƙwarin guiwa da karsashi na yin sammako da sassafe domin a noce a yi ta aiki. Yawaita ƙwazon manoma kuwa, yana taimakawa ainun wajen wadata ƙasa da abinci da samun kuɗaɗe domin biyan buƙatun manoman na yau da kullum. Ko baya ga wannan, muƙalar ta yi tsokaci kan cewa, wani muhimmin dalili na saka turken raha a cikin waƙoƙin noma shi ne yana samar da salo ko kafa ta samun damar miƙa saƙo kai tsaye, ya kuma sa sakon ya karɓu nan take cikin hanzari. Haƙiƙa, makaɗa Mamman Amali shahararre ne a fagen amfani da raha domin isar da saƙo a cikin waƙoƙinsa na noma.

 

 

Manazarta

 

Tuntuɓi mai takarda.



[1] Gusau, S.M. (2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Benchmark Publishers Limited, Kano. Shafi na xi.

[2] Duba Ƙamusul Muhiɗ na Fairu Zibady da aka duba a adireshin intanet http://ar.m.wikipedia.org

[3] Duba Yahya, A.B. (1997) Jigon Nazarin Waƙa Kaduna: Fisbas Media Services. Shafi na 5.

[4] A duba Gusau, S.M. (2003) Jagoran Nazarin Waƙar Baka Kano: Benchmark Publishers Ltd. Shafi na 63

 

[5] A hirar da malam Ibrahim Ahmad Isa ya yi da shi a shirin ‘Daga Bakin Mai Ita’ a Rima Rediyo, a shekara ta 1994, mako biyu zuwa uku gabanin ya rasu, Amali ya faɗa cewa a wannan lokaci yana da shera hamsin ba ɗaya (49). Idan aka cire 49 daga 1994, za a sami 1945. Wannan ne zai kasance shekarar da aka haife shi.

[6] Mamman Amali da kansa ya kawo wannan zance a wata hira da Ibrahim Ahmad Isa na Rima Rediyo, Sokoto ya yi da shi a shirin ‘Daga Bakin Mai Ita’ a shekara ta 1994.

[7] Daidai da Tushen bayani na bakwai. Amali ya faɗa a cikin wannan hira cewa ko da yana koyon magana kusan da waƙa ya tashi a bakinsa kuma da ita yake magana.

[8] Amali ne da kansa ya kawo wannan zance a hirar da Ibrahim Ahmad Isa ya yi da shi a shirin Rima Rediyo Sakkwato mai suna ‘Daga Bakin Mai Ita’. An yi hirar ne a shekara ta 1994.

[9] Hira da Alh. Ibrahim Ahmad Isah, ma’aikacin Rima Radiyo Sakkwato wanda ya yi hira da makaɗa Amali Sububu a shirin ‘Daga Bakin Mai Ita’ na Rima Radiyo.

[10] Makaɗa Muhammadu Bawa Ɗan’anace a wani ɗan waƙa tasa yana cewa:

 Jagora: Damina ta dimdinta a yi ta noma

 ‘Y/Amshi: A kashe raggo mu sha jini nai.

 Jagora: Har abada ban shiri da raggo

 ‘Y/Amshi: Na ce jar ƙaniyar uwatai.

Gindin waƙa: Ɗanbandodo Ubandawaki

 : Yaro ya doke ‘yan banawa

 (Waƙar Ubandawaki Ɗanbandodo, cikin Gusau, (2009:434)

[11] Makaɗa Sani Ɗan’aino Gyalenge ya tabbatar da haka a wani ɗan waƙarsa da ya ce:

 Jagora: Hunger is very danger,

 If you are feeling hunger,

 It will make you anger.

 ‘Y/amshi: Wai yunwa bala’I

 In yaz zan kana jin ta,

 Zahin rai take sa wa

 (Makaɗa Sani Ɗan’aino Gyalenge, Waƙar Ƙwazo Gayari.)

Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.