Ruwa a tunanin Sarkawa shi ne rayuwa kuma abokan aiki ne da muhimmancinsa a rayuwar Ɗan’adam ba ya misaltuwa. A cikin ruwa, Allah Ya rayar da wasu halittu waɗanda mutane ke kamawa domin samun abinci da kuma sarrafa su don wasu buƙatu na al’ada kamar yin magani ko mahaɗin magani. Akwai wani rukuni na al’ummar Hausawa da suka shahara wajen kamun kifi da sauran halittun ruwa. Waɗannan mutane su ne Sarkawa. Sun shahara matuƙa wajen sha’anin ruwa. Tun da haka ne, ashe ba wanda ya cancanta a tuntuɓa dangane da lamarin ruwa idan ba su ba. A kan haka ne wannan muƙala za ta kalli tunani da kuma yadda Sarkawa suke ɗaukar ruwa, musamman irin matsayin da suke ganin ruwa yana da shi a rayuwar al’umma.
Ruwa a
Idon Sarkawa
DR. MUSA
FADAMA GUMMI
Email: gfmusa24@gmail.com
Phone No.: 07065635983
1.0 Gabatarwa
Allah a cikin ikonsa da buwayarsa ya yi
halittu daban-daban kuma daga cikin halittun nasa, akwai ruwa. Ruwa kuwa akwai
wanda yake kwance a kan doron ƙasa, akwai kuma wanda yake ƙarƙashin ƙasa. Misalin ruwan da
yake kan doron ƙasa ya haɗa da na teku da kogi da gulbi da ƙoramu da tafkuna. Na ƙarƙashin ƙasa kuwa shi ne ruwan
rijiya. Masana kimiyya sun yi hasashen cewa ruwa ne yake mamaye da kimanin kashi
saba’in (70%) cikin ɗari na doron ƙasar da ke duniyar
nan.[1]
Daga cikin ruwan da ke shimfiɗe a doron ƙasa, akwai wanda ɗanɗanonsa gishiri ne.
Akwai ruwan da nasa ɗanɗanon mai zartsi ne.
Wani ruwan kuma yana da ɗanɗano mai ɗaɗi.[2]
Ruwa muhalli ne da wasu halittu kan rayu a
cikinsa. Halittun kan haɗa da dabbobi da kuma
ciyayi A cikin ruwa ana samun kifi da kada da dorina da ayyu, da karen ruwa da
kunkuru da tsari da sauransu. Misalin tsuntaye masu rayuwa ko neman abinci a
ruwa ya haɗa da ƙirinjijiya da dunya
da kazar ruwa da takau da zalɓi da sauransu. Ta fuskar ciyayi kuwa, akwai burugu da
bado da shalla da kainuwa da sauransu.
Sakamakon waɗannan albarkatu da Allah Ya rayar a
ruwa, wani rukuni na al’ummar Hausawa sun rungumi sana’a wadda ta danganci
shiga ruwa domin kambaɗar kifi da kuma wasu
halittu na ruwa. Wannan ne hanyarsu ta neman abinci da biyan buƙatun rayuwa. Waɗannan mutane ba wasu
ba ne face Sarkawa. Mutane ne da suka shahara kan sha’anin ruwa. Mutane ne da
ke iya sarrafa ruwa da kuma halittun da ke cikinsa. Masana ne kan lamarin ruwa,
da irin cututukan da ake iya ɗauka sakamakon yawaita shiga ruwa. Ƙwararri ne wajen ba
da magani na cututukan ruwa kuma sun shahara matuƙa wajen bayar da
agaji ga haɗurran da ake iya samu
a ruwa.
Gargajiyance, a idon Bahaushe, babu wani
masanin ruwa da ya wuce Basarke. Dalilin haka, ba ya rasa nasaba da irin sabo
na yau da gobe da Sarkawa suka yi da ruwa. Don haka ne wannan muƙala ta ƙuduri ƙyallaro yadda tunanin
Sarkawa yake dangane da ruwa. Yadda suka ɗauki ruwa, yadda suke kallonsa da irin
matsayin da suka ba shi, wato yadda falsafar su take dangane da ruwa. Wannan
shi ne abin da muƙalar ta ƙuduri yin nutso a cikinsa domin lalubo
bakin zaren ta yadda ko da za a kawo ganga, batun zai fita sarari yadda kowa
zai iya ganinsa. Ko banza Bahaushe na cewa, Ko me ya nutse, a tarbai ganga.
Gabanin duƙufa wajen bayanin, ya dace a duba ma’anar ruwa da kuma
wane ne Basarke?
1.2 Mene ne ruwa?
Ruwa wani abu ne mai danshi da ni’ima da yake saukowa
daga giragizai wanda yake haɗuwa ya samar da ƙoramu da gulabe da
tafukka da teku. Wannan abu mai dausayi shi ne abin da ya fi kowane yawa daga
cikin abubuwan da kowace halitta ta ƙunsa. Idan ba a
gauraya shi da komai ba, wannan abin ba ya da ƙanshi ko wari da kuma
ɗanɗano.[3]
Aljuhari, (2009) ya faɗa cewa ruwa shi ne
abin da ake sha.[4]
Ibn Manzur (1997) ya ruwaito cewa, Imam Jauhari ya ce “ruwa shi ne abin da ake
sha.”[5]
A wani ƙauli kuwa, cewa aka
yi ruwa abu ne da kan kasance ba shi da launi, ɗanɗano da ƙanshi ko wari kuma
shi ne tushen rayuwa.[6]
Ƙamusun Hausa cewa ya
yi ruwa abu ne garai-garai marar launi ko ƙanshi wanda ake sha
don kashe ƙishi, kuma ana wanka da wanki da dafa abinci da
wanke-wanke da makamantansu da shi.[7]
A nawa tunani, gani nake cewa ruwa abu ne
sakakke mai shiga kowane irin jiki da bin iska da tafiya mai nisa da ƙarfin gaske, wanda
yake ɓuɓɓuga a ƙasa da sama. Halitta ne
na Ubangiji wanda tsurarsa ba ya da ɗanɗano ko wari ko ƙanshi da launi.
Wannan halittar kan sauko daga sama domin raya ƙasa ta ɗanyace, ta fitar da
tsirrai. Idan ya sauko sosai daga sama, yakan taru a koguna da gulabe da ƙoramu da tafukka. Shi
ake ɗiba a sha domin a
rayu, a kuma yi wasu ayyuka na musamman da rayuwa ba ta yi sai da su. Ana shigarsa
domin a kama waɗansu halittu da ke
rayuwa a ciki a kuma yi amfani da shi a matsayin wata hanya ta sufuri. Idan ya
yi ƙaranci,
rayuwar kowace halitta da ke doron ƙasa kan takura, ta
lalace, wani lokaci idan abin ya yi tsanani, rayuwar ta salwanta.
1.3 Matsayin Ruwa A
Rayuwa
Ruwa abu ne mai muhimmancin gaske ga rayuwar
kowace halitta da ke doron ƙasa. Ruwan da yake kwance a ƙasa kamar na teku da
koguna da gulabe da ƙoramu har da tafukka, na da tasiri ga rayuwar halittu,
dabbobi da tsirrai. Masana kimiyya sun haƙiƙance cewa, tururi da
ake samu daga ruwan da yake kwance a bisa doron ƙasa da kuma wanda ake
samu daga bishiyoyi ne yake haifar da ruwan sama. Ruwan sama yana taimakawa
wajen fitar tsirrai daban-daban waɗanda ake nomawa domin abinci. Haka sauran
tsirrai da kan fita, su ƙawata muhalli, ya koma kore shar. Wasu daga cikin waɗannan tsirrai kan
taimaka wa Ɗan’adam wajen samar masa da sinadarai waɗanda yake amfani da
su don magance wasu cututuka. Wasu tsirran kamar itatuwa, ana amfani da su
wajen samun makamashi na yin girki da ɗumama jiki da muhalli (gidaje).Muhimmancin ruwa
na gama-gari ya haɗa da yadda ake amfani
da shi a rayuwar yau da gobe. Ruwa ake sha domin magance ƙishirwa. Da ruwa ake
girke-girke, a kuma tsabtace jiki ta hanyar wanka da wanki da kuma tsabtace
muhalli. Haka ana amfani da ruwa a lamurra da suka shafi ibadodi na addinai
daban-daban. Da ruwa ake yin alwala da wanka na ibada kamar wankan janaba da na
haila da makamantansu, waɗanda suka keɓanta ga musulmai.
Mabiya addinin Yesu Almasihu, wato Kiristoci, suna amfani da ruwa musamman na
gulbi wajen yi wa mabiya baptisma.
Akwai alfanu mai yawan gaske da ruwa yake da
shi wanda kuma ya keɓanta ga waɗanda suka ƙware ga sha’anin
ruwa. A nan ina magana ne kan Sarkawa waɗanda galibi hanyar neman abincinsu ta shafi
ruwa. A kowane yanayi Basarke ba ya tada ko ƙyamar shiga. Lokacin
bazara ne, hunturu ko kuwa damina, Sarkawa duk shiga ruwa suke yi domin aiwatar
da sana’ar su ta kamun kifi da kuma kambaɗar wasu halittu na ruwa kamar kada da ayyu da
dorina. Baya ga haka, Sarkawa suna amfani da jirage a cikin ruwa wajen ɗibar mutane da kaya
domin tsallakar da su daga wannan wuri zuwa wancan. A nan ina nufin aikin fito
daga wannan mashaya zuwa waccan. Idan aka yi la’akari da tarin alfanu da ruwa
yake da shi, sai a ga cewa ruwa shi ne rayuwa, idan babu ruwa, babu rayuwa.[8]
1.4 Wane ne Basarke?
Bisa asali, kalmar Basarke an samo ta ne daga
kalmar Sarkanci. Asalin kalmar kuwa ba Bahaushiya ba ce. Tushen kalmar daga
‘Sorko’ ne, wata al’umma ta daular Sanwai (Songhai). Al’ummar Sorko mutane ne
da suka shahara matuƙa ga sha’anin su a kogin Kwara wanda ya ratso ƙasashe da dama na
yammacin Afirka. Sana’ar su ce ta kawo wannan al’umma ta Sorko a daular Kabi.
Sannu a hankali suka saje da al’ummar da suka tarar a Kabi.[9]
Domin a Hausantar da wannan kalma ta ‘Sorko’
an yi mata kwaskwarima ta hanyar cire wasalin /o/ a gaɓar farko aka musanya
shi da wasalin /a/, wataƙila domin a sami sauƙin furuci. Haka ma an
yi mata ƙarin ɗafa goshi na ‘ba’ ta yadda za a sami sunan wanda ya fito
daga wannan al’umma ta ‘Sorko’, kafin daga baya ma’anar ta sauya zuwa ga duk
wani mai gudanar da sana’ar. An kuma cire wasalin /o/ na ƙarshe, aka musanya
shi da wasalin /e/, aka sami “Basarke”. Dangane da suna na sana’ar kuwa tushen
kalmar ne na Ɗsarkɗ aka yi wa ƙarin ɗafa ƙeya na ‘nci’ aka sami
kalmar ‘Sarkanci.’[10]
Bisa ma’ana, masana sun tofa albarkacin
bakinsu dangane da abin da suke ganin ake kira Basarke. Bargery, (1933:92) a ƙamusunsa ya bayyana
wanda ake kira Basarke. A cewarsa,
Basarke
shi ne masunci ko mai fito da kwale-kwale.[11]
Wani sashe na wannan zance na Bargery yana da
rauni domin aikin jirgi (kwalekwale) domin aikin fito da su ba shi ke sa mutum
ya zama Basarke ba duk da cewa akasarin Sarkawa suna amfani da jiragen ruwa a
wajen aiwatar da sana’arsu. Basarke ba shi ne kawai masunci ko mai fito ba.
Wannan ma’ana tana da naƙasu domin kuwa aikin Basarke bai tsaya ga su ba kawai. Basarke
baya ga kamun kifi, yana kuma ba da magani na iskokin ruwa, da cizo ko sukar
wata dabba ta ruwa da ma sauran cututuka na ruwa. Ba wannan kaɗai ba, Basarke shi ne
wanda ya gadi sana’ar Sarkanci ya kuma ba ta muhimmanci fiye da kowace irin
sana’a, rani da damina. Tare da haka, ga kuma zancen ƙwarewa kan sana’ar.
Alkali,
(196930) ya bayyana abin da yake gani ake kira Sarkanci a inda yake cewa
Tun
farkon ƙarni na goma sha tara (19) kalmar sarkanci ta ɗauki
ma’anar ƙwarewa kan sana’ar
su, don haka duk Bakaben da ke
yin wannan sana’a ake kiransa Basarke.
Wannan ma’ana da Alkali ya kawo ta yi daidai
don kuwa ba kowane masunci ne ake kira Basarke ba. Basarke masunci ne ƙwararre, wanda ba ya
da wata sana’a da ta shige ta su, rani da damina. Irin wannan masunci ne za a
tarar yana iya sarrafa ruwa da ma halittun da ke cikinsa ta duk yadda yake so.
Ta fuskar ba da magani kuwa, Basarke ba kanwar lasa ba ne kuma ƙwararre ne, masani ga
sha’anin ruwa. Yana iya hana shan ruwa, ko ya sa ruwa ya kasa dafa kifi, wato
kifi ya kasa dafuwa. Yana iya sa ƙayar kifi ta laƙe wa wani idan aka
takale shi. Yana kuma iya hana a kama kifi a wani ruwa idan aka ɓata masa. Basarke
masanin asirai ne na ruwa matuƙa.
2.0 Karatun Ruwa A
Bakin Sarkawa
Sarkawa mutane da suka saba da ruwa saboda
yawan shigarsa da suke yi don neman abinci. Wannan sabo da suka yi da ruwa ya
sanya suka kasance malamai kuma masana ƙwararri dangane da
asirin ruwa. Dalilin sabo na yau da gobe da kuma kaifin tunani da hikamarsu,
Sarkawa suna da fahimta sosai, da sani mai yawan gaske dangane da lamarin ruwa.
Don haka ne suke yi wa ruwa wani kallo na musamman. Suka ba shi (ruwa) wani
matsayi a rayuwa ta hanyar kare matsayin da hujjoji ƙwarara, waɗanda suka lura da su
tsawon lokaci da suka ɗauka suna mu’amala da
ruwa. Irin wannan kallo ko ɗauka da suka yi wa ruwa ake son a yi tsokaci a kan su.
Wannan kuma shi ne falsafar Sarkawa game da ruwa.
2.1 Halitta Daga Ruwa
Ne
Sarkawa sun ɗauka cewa ruwa rayuwa ne domin ba wata
halitta da za ta iya rayuwa a bisa doron ƙasa idan babu ruwa.
Ruwa yana ɗaukar kaso mai yawa a
cikin jiki na halittu da dama[12] Don
haka ne Sarkawa suke ɗauka cewa ruwa shi ne
rayuwa kuma ruwa yana taka muhimmiyar rawa wajen halitta.[13]
Wannan ne ya sa a cikin kalamansu da maganganunsu na yau da kullum, za a ji
wannan falsafar tana fita a fili. Sau da yawa a kalamai na Sarkawa da ma wasu
da ba su ba, za a ji zance inda suke amfani da kalmar ruwa da nufin kamannu na
halitta. Sukan faɗi zance kamar:
‘Ruwan gidan wane na gani.’
Ma’anar wannan kalami
shi ne wanda ake zance kansa ya yi kama da wani wanda aka sani. Kamar kuwa ta
halitta ake nufi, wato akwai kamanni na halitta tsakanin wanda ake magana kansa
da kuma wani wanda aka sani.
Haka a maganganu na
Sarkawa da kuma wasu da suke makusantansu, za a ji suna amfani da kalmar ‘ruwa’
da ma’anar kamanni na mutanen wani gari ko wata ƙabila. Da irin
lafazin za a riƙa jin suna cewa:
‘Ya yi mini kamar ruwan Yarbawa’.
Kalami irin wannan
yana nufin cewa duk da kasancewar wanda ake magana kansa ba Bayarabe ba ne, ya
yi kama da Yarbawa ta fuskar halitta. Wato yana da siffa irin ta Yarbawa. Ƙwayoyin halitta daga
maniyi suke kuma ana ɗaukar maniyi a
matsayin ruwa. Saboda wannan ne ake ɗaukar kamanni da halitta a matsayin ‘ruwa’.
A tunanin Sarkawa, tun da halitta duka mai rai
daga ruwa take, duk lokacin da ake son a kamanta wani abu da wani, ana amfani
da kalmar ruwa. Dubi yadda ake amfani da kalmar ruwa wajen nuna kamannin launin
wani abu. Idan abu yana da launi shigen na madara, akan ce ‘ruwan madara ne’.
Haka ma akwai ‘ruwan ɗorawa’ idan launin
abu ya yi kama da na ɗorawa. wasu kuwa kan
kira shi ruwan ƙwai. Abin da launinsa mai ƙyalƙyali da ɗaukar ido ne, sai a
ce yana da ‘ruwan zinari’ don kuwa launi nasa tamkar zinari ne. Launuka da dama
akan nuna alamarsu ga wani abu da ya yi kama da su ta hanyar amfani da kalmar
ruwa. Baya ga haka, sakamakon ɗaukar da Sarkawa suka yi na kasancewar halitta daga ruwa,
ana amfani da kalmar ruwa domin nuna kamanni ko siffa ko ɗabi’a ta mutane.
Misali idan mutum ya yi kama da wawaye akan ce “ yana da ruwan wawaye.” Haka ma
idan ya yi kama da masu wayo akan ce yana da ‘ruwan wayo’. Idan kuwa mutum
matsoraci ne sai a ce ‘ya faye ruwan ciki’. Idan kuwa inda-inda, wanda ba ya
kai tsaye zaɓar abu ɗaya nan take, akan ce
‘ya faye ruwan ido.’
2.2 Ruwa Rayuwa ne
A basarken tunani, ruwa rayuwa ne. Ba kawai
kasancewar halitta daga ruwa ba, rayuwa kowace iri ce tana buƙatar ruwa. A tunanin
Sarkawa rayuwa ba ta salwanta sai ruwanta ya ƙare. Idan halitta ba
ta da sauran shan ruwa a gaba, sai ta mutu. Idan kuwa da sauran ruwa, sai dai
ta galabaita ko ta rayu a wahalce, na wani lokaci, bakin iya adadin ruwan da
aka ƙaddara mata,[14]
Bahaushe idan ya ce, “wane ya sha ruwa” to
yana nufin wane ya yi rayuwa mai jinkri, wato ya yi tsawon rayuwa. Idan ya ce
“shan ruwa ya ƙare”, abin nufi shi ne mutuwa ta zo wa rayuwa.
Ɗaukar da Sarkawa suka
yi cewa, ruwa shi ne rayuwa ya sanya Bahaushe a wata Karin magana yana cewa:
‘Rai dangin goro ne ruwa aka ba shi.’
Goro ‘ya’ya ne na
bishiya wadda ba ta iya rayuwa sai da ruwa. Haka ma ‘ya’yan idan ana buƙatar su daɗe ba tare da sun
bushe ba, ana ɗan yayyafa masu ruwa
akai-akai. Rayuwa ma haka take, tana buƙatar ruwa domin ta
rayu, ta kyautatu, ta kuma ni’imtu. Ba wai abinci kaɗai rayuwa take buƙata ba, ruwa ma
muhimmi ne. Rayuwa ba ta saurin salwanta sakamakon rashin abinci kamar yadda
take yi idan babu ruwa. A bisa al’ada idan mutum ya suma, ruwa ake fara zuba
masa domin a farfaɗo da shi. Ko haɗari aka yi, masu ceto
suka hango wani ya suma, ba abin da suke cewa sai ‘a kawo ruwa’. Ruwan ne za a
yayyafa wa wanda ya suma don ya farfaɗo. Wannan gajeren labari da ya auku a zahiri
zai tabbatar da haka.
A shakara1985, sa’ilin watan azumi kan kama
cikin tsakiyar bazara. Ranar wata Lahadi, a kasuwar Jabo, ƙaramar hukumar
Tambawal, jihar Sakkwato, wata tsohuwa ta faɗi ta suma sakamakon matsanancin zafi da kuma ƙishirwar azumi.
Mutane da suka kawo mata ɗauki sai suka yayyafa
mata ruwa. Da ta ɗan farfaɗo, sai suka ba ta
ruwa mai sanyi ta sha. Tana shan ruwan sai ta ƙara dawowa cikin
hayyacinta. Ga fura an kawo, sai mutane suka ce, “a ba ta fura”. Tsohuwar da ta
ji abin da mutane suka faɗa na a ba ta fura,
sai ta ce, “kada ku ba ni fura azumi ni kai!” Abin mamaki, kuma abin ban
tausayi, tsohuwar ba ta san lokacin da aka ba ta ruwa ta kwankwaɗa ba. Amma ta ji
lokacin da ake cewa a ba ta fura, don haka ta ce azumi take yi, kada a ba ta.
Haka ya taɓa faruwa da wani wai
shi Ɓaruje wanda ya sha ruwa a yayin da yake azumi sakamakon
galabaita da ya yi. Da aka ce a kawo masa fura cewa ya yi, “Wallahi sai na kai
shi.” Tirƙashi! Wani abu sai ruwa! Wannan labari ya nuna cewa, ruwa
shi ne rayuwa idan babu shi, rayuwa sai ta salwanta.[15]
2.3 Barkwancin Ruwa
Duk da cewa daga cikin fahimtar da Sarkawa
suke da ita game da ruwa akwai danganta rayuwa da ruwa, ruwa a falsafar Sarkawa
yakan yi barkwanci. Ma’anar barkwanci a nan shi ne samun tangarɗa a wani sha’ani da
aka gwanance kan sa. Sarkawa sun ɗauka cewa komai iya ruwan mutum, wata rana zai
iya samun tangarɗa ko matsala a
cikinsa. Don haka ne ake son a riƙa hattara da
kaffa-kaffa ga sha’anin ruwa. Akan yi hattara ne kuwa domin kaucewa barkwanci
irin wanda aka san ruwa da shi. Ɗaukar da Sarkawa suka
yi wa ruwa na kasancewarsa aba mai iya yin barkwaanci, ya sanya suka fito da
karin magana mai cewa:
Gwanin ruwa, shi ruwa kan ci.
Wanda ya saba da
ruwa, ya iya iyo sosai kuma ba ya razana ko tsorata komai yawan ruwa ko
zurfinsa, shiga yake yi. Irin wannan shi ruwa kan ci. Wanda ke jin tsoron ruwa
kuma ba ya shigarsa, mawuyacin abu ne ruwa ci shi.[16]
Basarke saboda irin fahimtar da yi wa ruwa na
abu mai iya yi wa gwaninsa barkwanci, ya fito da karin magana mai nuna irin
wannan halayya ta ruwa. Bahaushe na cewa:
Ruwa ya ƙare wa ɗan kada, bai gama wanka
ba.
Kada halitta ce da
take rayuwa a cikin ruwa. Abincinta da mazauninta duk a ruwa yake. Basarke yana
sane da cewa, kada yana da waibuwa mai yawa. Saboda wannan waibuwa tasa, sai
Basarken da ya isa zai iya farautarsa. Duk da irin wannan waibuwa tasa da kuma
kasancewar yana rayuwa a ruwa, bai hana ruwa ya yi wa kada halinsa na barkwanci
ba. Ma’anar wannan karin magana shi ne mutum ya riƙa hattara da
taka-tsantsan ga lamurran duniya domin zare na iya tsinkewa a lokacin da ba a
shirya wa haka ba.
La’akari da halin
ruwa na yin barkwanci, ya sanya idan gwanin yin wani abu ya sami kuskure yayin
aiwatar da abin nan, akan ce:
“Abin ya ba shi ruwa”.
Ma’ana, duk da cewa akwai
gwaninta da ƙwarewa ga wannan lamarin, to yau da gobe ta yi halinta.
Kasawa ta Ɗan’adam ta bayyana domin mutum duka ɗan tara ne.
Baya ga haka, tunanin cewa, ruwa yana da
halayya na barkwanci, idan Basarke ko wani Bahaushe ya dafa wake, aka sami waɗansu ‘yan ƙwarori na waken ya
kasa dafuwa, ana kiransa ‘ruwan gawa’. Wato waken da ya yi barkwanci, ya kasa
nuna sa’ilin da aka dafa shi. Sauran waken da ya nuna ya zama gawa amma wanda
ya kasa nuna ya zama ruwa don ya yi barkwancin kasa dafuwa.
Tare da haka, a duk
lokacin da mutum ya ɗauko ɗaki ta fuskar yin
abin da ya fi ƙarfinsa, ba tare da ya yi hattara da kaffa-kaffa a rayuwa
ba, akan ce:
“Ya sha ta fi cikinsa.”
Ma’anar wannan shi ne
mutum ya yi abin da ya zarce zarafinsa.
Idan ruwa ya yi
barkwanci rayuwa na iya salwanta ko ta shiga wani hali na wahala. Da haka a
wurin Sarkawa da wasu makusantansu, duk lokacin da rayuwa ta shiga cikin ƙunci, matsaloli suka
tattaru, suka dabaibaye rayuwa, lamurra suka dagule, akan kwatanta shi da:
‘ruwa ya kai ga wuya’ [17]
Ƙari bisa wannan
zance, sakamakon fahimtar da Sarkawa suke da ita kan ruwa, na kasancewarsa mai
barkwanci, ruwa yana da tsoratarwa don kuwa ko gwaninsa bai tsira daga samun
tangarɗa a cikinsa ba.
Wannan ne ya sanya Sarkawa suke faɗar wani zance na cewa:
‘ruwa ba ka da gwani.’
Komai ƙwarewar mutum da iya
ruwa, yana iya samun matsala a cikin sa, idan dai har yana shigarsa yau da
gobe.
Ba wannan kaɗai ba, dalilin barkwancin ruwa da
Sarkawa suka tabbatar, mutane suna jin tsoronsa musamman ruwan gulbi ko ƙorama ko tafki, wanda
yake da yawa da zurfi. Kan tsoron da ake yi wa ruwa
domin barkwancinsa ya sanya idan mutum ya razana ko ya tsorata da wani lamari
akan ce:
‘Cikinsa ya ɗuri ruwa’
Ma’ana shi ne wanda
duk cikinsa ya ɗuri ruwa, haƙiƙa ya tsorata matuƙa.
2.4 Ruwa Ma’auni Ne
Ruwa yana da ƙima sosai don haka
auna shi sai an yi amfani da wani mazubi. Sarkawa suna amfani da ruwa domin ya
kasance ma’auni na ƙimanta abubuwa ko auna su. A nawa hasashe, sakamakon ƙima da kuma daraja da
Sarkawa suke ganin ruwa yana da shi ya sanya a karin harshen Sakkwatanci wanda
ake amfani da shi a Argungu, cibiyar Sarkawa da Sarkanci a wannan ƙasa, ya sanya ruwa
yake ɗaukar lamirin jam’i,
saɓanin karin Hausar
gabas da ke ba wa kalmar ruwa lamiri na tilo. Misali a Sakkwatanci ana cewa
‘ruwa sun ƙare’, yayin da a Hausar gabas ake cewa ‘ruwa ya ƙare’.
Dalilin kasancewar Sarkawa suna ɗaukar ruwa matsayin
ma’auni na ƙimanta abubuwa ya sanya duk wanda aka ba shi damar zaɓen abu ɗaya daga cikin
abubuwa da yawa, ya kasa ɗauka ko yin zaɓen kai tsaye, ya
tsaya yana inda-inda, akan ce masa yana da ‘ruwan ido’. Wannan ɗabi’a ce take sa a
ce, ‘wane yana da ruwan ido’.
Haka kuma Sarkawa da
ma sauran masu magana da harshen Hausa, suna amfani da kalmar ruwa domin auna
abu musamman idan ana son a nuna yawa ko girman wani abu da mutane ke yin ado
da shi kamar zobe ko sutura. Idan misali mutum ya saka zobe a yatsarsa, ya
kasance zoben bai kama ta ba domin ya yi wa yatsar yawa, ana cewa, ‘zoben ya yi
ruwa’. Riga ko wando idan suka yi wa wanda ya saka su a jikinsa yawa, akan ce
‘sun yi masa ruwa’, wato yawan suturar ta rinjayi jikin wanda ya saka ta.
Akwai karin maganar
da ke nuna ruwa ma’auni ne. Karin maganar na cewa:
‘Ruwan da ya isa kurma, da shigarsa ana
ganewa.’
Ma’anar wannan shi ne
idan ana son a san ƙimar abu, musamman yawansa ko rashin yawansa, akwai buƙatar auna shi ko da
kuwa ba da mudu ba. Ko da ta hanyar taɓawa ko shiga cikinsa ne
Sarkawa sakamakon
sabo da shiga ruwa na yau da kullum, sun gano cewa ruwan da yake a faƙo galibi ba ya da
zurfi amma kuma idan aka kalli ruwan a kwance, sai a yi zaton mai yawan gaske
ne amma ina! Shirim ne ba ci ba. Wannan ya sa ake kwatanta abun da ake zaton
mai yawa ne amma a zahiri ɗan kaɗan ne da ‘ruwan faƙo’ Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun wanda
ya san yanayin fadamar nan da ta raɓi gulbin Sakkwato a nan ƙasar Maradun, wadda
yanzu take cikin madatsar ruwa ta Bakalori yake cewa a wani ɗan waƙa tasa:
Gidin Waƙa: Mai Maradun
baban Baraya
Jikan Moyi, Iro ɗan Mamman tura haushi
Jagora: Allah waddan ruwan hwaƙo
Na hange su zay yawa
‘Yan Anshi: Na zaton da zurhi
(Gusau, 2009:132)
Ana kuma amfani da
ruwa domin auna ƙanƙantar lokaci da aka ɗauka na yin wata tafiya ko ziyara ko wani
aiki. Gano abu ƙanƙani ne ko babba ne ko mai yawa ne duk ya shafi ma’auni.
Domin zance makamancin wannan, ana amfani da kalmar ruwa. Bahaushe na cewa:
‘Shan ruwan tsuntsaye’
Duk abin da aka yi wa
shan ruwan tsuntsaye kuwa, an yi shi ne kai tsaye, ba tare da ɓata wani lokaci ba ko
wata tsaitsayawa. Sarkawa suke zaune a fadama rani da damina, su kuma suka san
abin da yake faruwa a fadama da halittun da ke rayuwa a ciki da kewayenta
musamman ɗabi’unsu don haka su
ne malamai, masana sha’aninta. Su suka san yadda tsuntsu yake shan ruwa suka
kuma kwatanta ma’auni na ƙanƙancin lokaci.
2.5 Ruwa Siyasa ne
Ruwa aba ne mai muhimmancin gaske, wanda
kowace rayuwa da halitta na buƙatuwa da shi. Ruwa da albarkatunsa na
da ƙima
sosai a wurin kowace al’umma. Duk da haka, duniya na fuskantar ƙarancinsa. Ƙarancin ruwa da
albarkatun da ke cikinsa, da kuma yawan buƙatarsa da al’ummomi
daban-daban suke da shi, kan haddasa siyasa dangane da mallaka ko dama ta tatsarsa
da kuma albarkatun cikinsa. Wannan ne kan haddasa tashin-tashina, rigingimu,
wani lokaci har da faɗace-faɗace tsakanin
al’ummomi. Waɗansu gulabe da
tafukka kan ratsa ƙasashe daban-daban. Wannan ne ya sanya akan yi amfani da
su a matsayin alamomin iyakoki na dindindin tsakanin ƙasashe, jihohi ko
yankuna.
Sarkawa saboda fahimtar ruwa da suka yi sosai
da sosai ya sanya sun ɗauka cewa, ruwa
siyasa ne ko wani fage na siyasar al’umma. Wannan ne ya sanya albarkatun
tafukka, gulabe da ƙoramu waɗanda Allah a cikin ikonSa Ya shimfiɗa a duk faɗin gundumar Sakkawato
suna ƙarƙashin kulawar wasu shugabanni na al’umma. A kan haka,
saboda siyasar ruwa masunci ba ya shiga kowane ruwa ya yi su kai tsaye sai tare
da izni na waɗanda ke kula da
ruwan. Misali a Argungu, gulbin Matan Fada, inda ake aiwatar da shahararren
bukin kamun kifin nan na ƙasa da ƙasa yana ƙarƙashin kulawar
Makwashi ne kuma Shugaban ƙasar Nijeriya ne yake bayar da izni na
yin su a cikin wannan ruwan. Gulbin Mala da wasu tafukka kuwa suna ƙarƙashin kulawar Sarkin
Kabin Argungu ne don haka shi kaɗai ne zai iya bayar da iznin kama kifi a
ciki.[18]
Yadda wannan al’amari yake a Argungu dangane da siyasar ruwa, haka abin yake
har a wasu masarautu na gundumar Sakkwato. A bisa siyasar ruwa, masunta ba su
da ikon fasa kowane tafki sai da izinin Sarkin Ruwa. Idan kuwa aka kuskura aka
yi haka, Sarkin Ruwa na da waibuwar da zai iya sa kifi ya kasa kamuwa ga kowa.
A shiga ruwa, a yi su har a take ba tare da an kama ko da ƙwaguwa ba. Wani
sa’ili kuma sukan saki matsanancin sanyi a ruwa ta yadda da mutum ya shiga, ba
zai iya jure wa sanyin ba.
Siyasar ruwa kan sa Sarkawa su mallaki asirai
daban-daban kamar asirin kashe ruwa da sa tafki ya ƙafe, ya daina ajiye
ruwa ko kuma ma a hana ruwa tsayuwa ko tattaruwa a wani gurbi na gulbi. Jayayya
tsakanin mallakar ruwa kan sa aiwatar da waɗannan sihirce-sihirce a tsakanin Sarkawa.
Bisa al’ada, Sarkawa kan yi shinge na kamun
kifi a gulabe da tafukka. Misalin shingen ya haɗa da tashi, da ganuwa, da saba da
sankiya da dumba. A bisa siyasar ruwa ta yankunan da ake yin shinge a ruwa, ba
kowane masunci ne yake yin shinge a duk tafki ko gulbin da ya ga dama ba a
lokacin da zuciyarsa ta muradi yin haka. Galibi wajajen da ake yin shinge na
kamun kifi gadon su ake yi kaka da kakanni. Duk wanda bai gada ba, ba ya da
ikon da zai shiga gulbi ko tafki ya kafa shinge.
Baya ga haka, wani abu da ya ba Sarkawa haske
dangane da ɗaukar da suka yi cewa
ruwa siyasa ne ba ya rasa nasaba da dubin yadda gulbi ɗaya kan ratso yankuna
da dama daban-daban, daga tushensa har zuwa maƙurarsa, inda yake
kwarara ruwan duk da ya kwaso. A wani yanki, wannan gulbi zai sami wani suna
daban da yadda ake kiransa a wani yankin. Misali, gulbin Sakkwato da aka ce
tushensa na can yankin Katsina laka, ya kwararo a Zamfara har ya isa Sakkwato,
ana kiransa da suna gulbin Sakkwato. A tunani na, saboda siyasa, da gulbin ya
ratsa yankin Argungu da Birnin Kabi har zuwa inda ya haɗu da kogin Kwara, ana
kiransa gulbin Kabi domin siyasa ta rashin jituwa da ta wakana tsakanin daular
Sakkwato da kuma daular Kabi gabanin shigowar Turawan mulkin mallaka.
3.0 Sakamakon Bincike
Wannan bincike ya
tabbatar da cewa Sarkawa sun taimaka matuƙa wajen samar da wasu
Karin Maganganu da salo tare da kalamai na hikima da ake amfani da su a harshen
Hausa. Wannan kuwa ya samu ne sakamakon irin falsafarsu dangane da ruwa dalilin
tarin sani ko ilimin ruwa da suka mallaka don su ne malaman ruwa. Haka ma
rayuwar komai ta ta’allaƙa ne ga ruwa domin ko na’urori kamar mota da jirgin sama
da Babura ba su tafiya sai an saka masu ruwan.. Yunwa ba ta saurin yi wa rayuwa
illa kamar yadda ƙamfar ruwa ko rashinsa yake yi wa rayuwa kisa, domin
rayuwa kowace iri ce ba ta yi sai da ruwa.
Kammalawa
Ruwa aba ne mai muhimmancin gaske da rayuwa
kowace iri ce ba ta walwala sai da shi. Baya ga amfani da ake yi da shi na
al’ada da addini wanda ya jiɓinci sha da wanka da wanki, ruwa yana da amfani
kasancewarsa maraya ta waɗansu halittu da ake
kamawa domin a ci ko sarrafa a matsayin magani ko mahaɗi na wasu magungunan
gargajiya.
Sarkawa mutane ne da suka ƙware, suka kuma
shahara wajen kamun kifi da kambaɗar wasu halittun ruwa kamar kada da dorina da
ayyu da sauransu. Da yake aikinsu ya jiɓinci shiga ruwa a kullum da safe ko da yamma
ko ma da dare. A lokacin damina da bazara ko lokacin hunturu, ba sa’ar da
Sarkawa ba sa shiga ruwa. Don haka ne suke iya sarrafa ruwa da kuma halittun da
suke cikinsa. Dalilin ƙwarewar da suke da ita kan lamarin ruwa, Sarkawa su ne
malamai masana ruwa. Da yake Bahaushe yana cewa ‘kome ya nutse a tarbai ganga’
ashe idan ana son ƙwaƙƙwaran sahihin bayani game da ruwa dole sai a
nemi Sarkawa don kuwa su ne malaman ruwa. Tunanin da suke da shi, da irin ɗaukar da suka yi wa
ruwa, ya samu ne sakamakon tarin sanin da suka mallaka game da ruwa. Wannan
kuwa shi ne falsafarsu game da ruwa.
Sarkawa suna kallon ruwa a matsayin rayuwa
kuma rai kowane iri ne, dangin goro ce, ba ya yi sai da ruwa. Wannan ne ya
sanya aka fahimci cewa idan kana son labari daga wurin baƙo, to ba shi ruwa don
ana ba baƙo ruwa a sha labari. Ruwa shi ke ɗaukar kaso mafi
rinjaye daga cikin jikin halittu. Don haka ruwa shi ne sinadarin kowace halitta
ta Ɗan’adam
saboda da ruwa na maniyi aka halicce shi. Ruwa duk da muhimmancinsa ga rayuwa
aba ne mai yawan barkwanci don kuwa sau da yawa ruwa gwaninsa yake ci. Wannan
ne ya sa ruwa yake abin da ban tsoro don kuwa sau da yawa cikin mutum kan ‘ɗuri ruwa’ idan
hankalinsa ya tashi, ya kuma tsorata. Basarke ya ɗauka cewa ruwa ma’auni ne don kuwa mai
‘ruwan ido’ yakan kasa zaɓe nan take. Akan yi
wa abu ‘shan ruwan tsuntsaye’ a ma’aunin lokaci ƙanƙane sannan kome ya
nutse akan tarbe shi ne a ganga don kuwa ba a tababata nutse a ruwa. A wurin
Basarke, ruwa koyaushe hanyarsa yake bi don haka yadda aka al’adantu da gudanar
da abu, haka ya kamata a riƙa yin sa.
MANAZARTA
Tuntuɓi mai takarda.
[1]
Wannan magana tana cikin kundin sani na intanet da ake kira Wikipedia. Ana
samun bayanin a adireshi http// www. en. Wikipedia.org/water.
[2]
Wannan nau’ukan ruwa ana kiran su da Ingilishi marine water da brakish water da
kuma fresh water.
[3]
Fassarar abin da Ƙamusun
Ingilishi na Merrian-Webster ya kawo dangane da ma’anar ruwa. A cikin Ingilishi
cewa aka yi: “ The liquid that decends from clouds as rain, forms streams,
lakes and seas and is a major constituent of all living matter and that when
pure it is odourless and tasteless.” Merrian-Webster Incorporation (2002) Merrian-
Webster Collegiate Dictionary. Tenth Edition. Shafi Na 1330.
[4]
Duba Aljuhari A.I. (2009) Assihahu: Tajul luggati Wa Sihahul Arabiyah. Al-Azhar,
Cairo. Shafi na 1105.
[5]
Ibn Manzur (1997) Lisanul Arab Vol. vi. Darul Sadir Beirut, Lebanon.
Shafi Na 112-113.
[6]
A duba bayanin ‘Al ma’u’ a Wikipedia a adireshin intanet http//www.ar.m.
Wikipedia .org
[7]
Duba CNHN (2006) Ƙamusun Hausa Na Jami’ar
Bayero. Cibiyar Nazarin harsunan Nijeriya, Bayero University, Kano. Shafi na
377.
[8]
Bature ma cewa ya yi
“Water is life.” ma’ana ruwa shi ne rayuwa.
[9]
Duba Alkali,M.B.(1969)” A Hausa Community in Crisis: Kebbi in the Nineteenth
Century.” M.A. Thesis, ABU Zaria. Shafi na 29-30.
[10]
A duba Abubakar, A. (2001) An
Introductory Hausa Morphology. Faculty of Arts, University
of Maiduguri, Nigeria. Shafi na 23 – 27.
[11]
Bargery, G.P. (1934) A Hausa-English Dictionary And English Hausa
Vocabulary. Oxford University Press, London. Shafi na 92.
[12]
Ruwa ya kai kimanin kaso 60 daga cikin ɗari na abin da jikin ɗan’adam ya ƙunsa.
Don ƙarin bayani, a duba intanet a
adireshi, water.usgs.gov/edu/propertyyou.html da kuma
en.wikipedia.org/wiki/Body-Water
[13]
Wannan falsafa ta Sarkawa game da ruwa ta yi daidai da abin da Allah Maɗaukaki ya faɗa
a cikin Alƙur’ani
mai tsarki, sura 21:30. Allah yana cewa:
“Shin kuma waɗanda
suka kafirta ba su gani cewa lalle sammai da ƙasa sun kasance ɗinke,
sai Muka buɗe su, kuma Muka sanya
dukan kome mai rai daga ruwa? Shin ba za su yi imani ba.”
(Alƙur’ani
Mai tsarki: Fassarar Abubakar Mahmud Gummi.)
Haka
ma Bature a cikin harshen Ingilishi yana cewa, “Water is life” wato ruwa shi ne
rayuwa.
[14]
Dubi abin da sha’iri
Aliyu Aƙilu
yake cewa, a ɗango na bakwai na waƙarsa ‘Cuta Ba Mutuwa Ba’
cikin Aliyu Aƙilu
(1980) Fasaha Aƙiliya
Northern
Nigeria Publishing Company, Zaria. Shafi na 39.
Ubangiji ya
yarda Da rayuwa mai tsada
Gare ni, tsara
takarda Da shan ruwa na randa,
Na ci gaban amfani
[15]
Dubi yadda mutanen Nijer ‘yan ci-rani fiye da mutum tamanin da bakwai (87) suka
mutu sakamakon ƙisa, bayan da motarsu ta lalace, yayin da suke tsallaka hamadar
Sahara kan hanyarsu zuwa Algeria, cikin watan Satumba na 2013. Don ƙarin
bayani kan wannan labari, a duba jaridar Daily Trus’ ta harshen
Ingilishi, Vol.33, No 35 ta ta fito ranar Jumu’a, 01/11/2013. Shafi na 25 labari
mai taken “87 Niger Migrants’ Bodies Found Near Algerian border”
[16]
Wannan dalili ne ya sanya makaɗa Ibrahim Narambaɗa
a waƙarsa ta ‘Alƙali Abu ‘ ya faɗa a wani ɗan waƙa cewa:
Gindin
Waƙa: Ya ɗau girma ya ɗau
yabo
Mu zo mu ga Alƙali Abu
Jagora:
Kul ka ishe gulbi ya cike
Im ba kowa ko ka iya,
Koma ka tsaya ganga ka kwan
Haka
Alhaji Mamman Shata a waƙar
da ya yi Sarkin Daura Muhammadu Bashar, ya faɗa
a wani ɗan waƙa cewa:
Gindin Waƙa:
Kwana lafiya mai Daura
Jikan Abdu gwauron giwa.
Jagora: Mamman baƙon ruwa ɗan Ummaru
Ka ci gwani uban ɗan Yayya.
[17]
Makaɗa Ɗan’anace
a wata waƙarsa
ta noma wadda ya yi wa Garba Nagodi yana cewa a wani ɗa na waƙar:
Gindin
Waƙa: Mai gida gona
Gamdaren Ali fama Garba Nagodi
Jagora: Agaza mani Garba Nagodi
‘Y/Amshi: Yau hwa ruwa sun kai ga wuyana.
[18] Domin
cikakken bayani kan gulabe da tafukkan Argungu da kuma masu kulawa da su, ya
dace a duba Argungu, Ibrahim Abubakar “Samuwar Waƙa Da Kirari A Bukin Kamun
Kifi Na Argungu.” Kundin Dgiri na Biyu (M.A.Hausa) Sashen Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato. Shafi na 17-21.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.