Citation: Maimota, A.S & Danbappa, H. R. (2024). Bangwayen Ƙagaggun Labaran Intanet: Ƙwai Daban Abin Cikin Ƙwan Daban. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies. Vol. 17, No. 1, December, 2024. Pg. 116-124
BANGWAYEN ƘAGAGGUN LABARAN
INTANET: ƘWAI DABAN ABIN CIKIN ƘWAN DABAN
Na
Aishatu
Shehu Maimota (Ph.D)
2348066054705
maimotaaisha@gmail.com
da
Jamilu
Kabir
2347067708766
jkabir@fudutsinma.edu.ng
Tsakure
Ƙarni na 21, ƙarni ne da yake ɗauke
da abubuwan cigaba mabambanta da suka shafi rayuwar al’umma a ko ina a faɗin duniya, musamman abin da ya shafi ƙere-ƙere
da fasahohi, uwa uba da ɓullowar hanyoyin sadarwa na zamanima da ake kira shafukan intanet. Samuwar kafafen
intanet ya buɗe sabon shafin samuwar marubuta labaran zube na Hausa da aka fi sani da “Marubutan Shoshiyal midiya ko marubuta Onlayin wato “Online Writers” a Turance. Manufar wannan bincike shi ne yin tsokaci dangane da ƙunshiyar
wasu labarai na intanet tare da yin tsokaci dangane da alaƙar labaran da hoton jikin bangwayensu. Domin sauke haƙƙin
wannan bincike an yi amfani da hanyoyi, da dabaru da suka dace da binciken don
tattare bayanai da suka hada karantawa da nazartar littattafan da suke lungu da
saƙo na ƙwaryar intanet da suka haɗa da Fesbuk wassaf da Watfad da Instagram. Sannan an ɗora wannan bincike a kan Ra’in maida
jawabin mai karatu wato (Reader Response Criticism Theory). An tattara
bayanai ta hanyar karanta wasu labaran sannan an tattaunawa da masu karatu don
jin fahimtarsu dangane da alaƙar da ke akwai tsakanin labaran da suke karantawa da hotunan da
ake liƙawa a bangon. A ɓangare ɗaya an tattauna da wasu
marubuta labaran don jin hikimar da ke tattare da sanya waɗannan
hotuna.. Binciken ya gano abin da mawalafan ke liƙa wa a bangon littatfin
ya yi hannun riga da ƙunshiyar labarin, a taƙaice dai “ƙwan da ban abin cikin ƙwan da ban.” Haka zalika an
gano yadda tasirin kallon fina-finai ƙasashen ƙetare ya taimaka wajen
haskawa marubutan hanyar yin amfani da hotunan Indiyawa da Turawa da sauran
al’umomin labaran. Haka zalika kafafen intanet musamman rumbun adana hotuna na zamani (Instagram) ya zama hanya ma fi sauƙi da samuwar hotunan jaruman fina-finai maza da mata na ƙasashen ƙetare.
1.1 Gabatarwa
Bangon littafi na da tasiri ƙwarai a fagen rubuta ƙagaggen labari da ma
ilmi bakiɗaya, domin a mafi
yawancin lokuta yakan haska ƙunshiyar abin da
littafi ya ƙunsa ne, musamman
abin da ya shafi taurarin labari ko manufarsa ko kuma yanayin wurin da aka
gabatar da labari. A taƙaice bangon littafi
kamar yana tattare labari ne a cikin hoto. Alal misali, da an ga hoton saurayi
da budurwa mai karatu zai yi hasashen wannan labari na soyayya ne Haka idan an
ga hoto da makami da manyan barade a jiki za a ɗauka wannan labari ya
shafi yaƙe-yaƙe, haka zalika idan hoton aljanu aka kawo
tabbas labarin zai shafi aljanu. Wannan misalai da aka kawo ya sa wannan
takarda bibiyar ire-iren bangwayen da ake liƙawa a labaran shafukan intanet, don a gano shin waɗannan hotuna na jikin
banƙwan sun yi daidai da
manufar labarin?. Domin a fayyace haka wannan bincike ya bibiyi wasu bangwaye
littattafan da aka saka a labaran baya musamman na farko da tsakiyar ƙarni na 20, kana aka kawo waɗanda suke na ƙarni na 21, musamman na jikin labaran
shafukan intanet.
Masana da manazarta sun gudanar da bincike kan abin da ya shafi Hausa a kafafen intanet, kamar Diso, (2016) da Yakasai, (2018) da Shehu da Rambo (2019) da Maimota, (2021) da Kabir, (2022) da Maimota (2023) da kuma Yakasai, (2024). Wannan takarda ma ta yi bincike ne kan abin da ya shafi Hausa a kafar intanet, wato adabin Hausa a shafukan intanet, sai da a wannan takarda an bibiyi yadda marubuta labaran Hausa na intanet suke tsara bangwayen labaransu da wasu hotuna na wasu al’umomi na ƙasashen waje, a wasu lokuta da yanayi na ƙasashen. Maƙalar ta bayyana mene ne bangon littafi da tsarinsa da ma’aunin da ya dace a tsara bangon littafi. An kuma bibiyi tarihin samuwar labaran Hausa na Soshiyal Midiya, kana aka yi tsokaci kan manufar wasu labaran soshiyal midiya da taurarin labaran, tare da hasko hoton bangwayensu. Haka zalika an yi tsokaci kan dalilan da ke sa marubutan saka hotunan wasu da ba Hausawa ba a jikin labaran Hausa. A ƙarshe an kawo rataye na samfuran bangwayen labaran soshiyal mediya.
1.1.1 Bangon Littafi
Bangon Littafi shi ne rigar da littafi ke
sanye da ita, wadda ta lulluɓe gangar jikin
littafin, wato shafukan littafi (Kabir 2022) bangon littafi tamkar wani jagora
ne ga mai shirin yin karatu domin kuwa yana ɗauke da wani muhimmin dunƙulallen saƙo da zai haskawa mai karatu abin da wannan littafi ya ƙunsa a taƙaice, musamman abin
da ya shafi surar littafi da kuma hoto, ko surar da ke jikin bangon littafin.
Waɗannan muhimman abubuwa galibi suna yin ishara
ne zuwa labarin da ke ƙunshe a cikin
littafin.
1.1.2 Tsarin Bangon Littafi
Haƙiƙa kowane abu akwai tsarin da ake gina shi a ɗabi’a, wanda yin hakan shi ne dacewa. Bangon littafi yana da tsari, wanda a
kansa ne ake tsara bangon. A tsarin bangon littafi yakan ƙunshi ɗayan abu biyu, wato
ko dai ya kasance zane ne na surar abin da ake so wanda yake nuni da labarin.
Zanen na iya kasancewa zanen sura ta mutum ko aljani (a hasashe) ko dabba ko
bishiya ko tsirrai ko ƙwari ko wani abu
marar rai kamar dutse ko gida ko mota. Hoton kuma yakan iya kasancewa hoto ne
na zahiri ko haƙiƙa (real picture) ko ƙirƙirarren hoto (animated picture).
1.1.3 Ma’aunin Da
ya Dace a Tsara Bangon Littafi
Kamar yadda aka ambata a baya, bangon littafi
wani taƙaitaccen saƙo ne, amma mai faɗi da yake marabtar
mai karatu cikin sauƙi zuwa ga labarin da
zai karanta da ke cikin littafin, wanda daga bangon ne ake iya fahimtar ko
hasashen abin da aka ƙunshe ko lulluɓe a cikin littafin. Misali idan littafi
ya ƙunshi labarin zube kan abin da ya shafi
Bahaushe ko Bahaushiya ko Hausawa, ana sa ran a jikin bango a ga abin da ke
nuni da haka. Idan labarin ya shafi soyayya ta Hausawa ana tsammanin hoton ko
zanen zai nuna budurwa Bahaushiya da irin shiga ta al’adar Hausawa ko a da ko a
yanzu. Idan labarin ya shafi sarauta wajibi ne a jikin bangon littafin a ga
haka, wato abin da ya shafi shiga ta gidan sarauta ko fada ko wani abu da ke
nuna sha’anin sarauta.
Hoton ko zanen ana iya samar da shi kan wani bigire ko yanayi ko muhalli ko wani abu da ya faru a cikin labarin. Idan kuwa littafin kan wani fanni ne na ilimi ana iya amfani da wata alama wadda da an gani take yanke ana iya fahimtar littafin ko a wane fanni yake magana ko a kan me yake ishara. Ga misalai nan daga wasu hotunan bangayen littattafai:
Shafin
sada zumunta wanda da Turanci ake kira Social Media, fasahar
adarwa ce ta zamani da jama’a ke sada zumunci tsakaninsu daga
sassan duniya daban-daban, ta hanyar amfani da cibiyar sadarwa ta zamani da aka
fi kira da netiwak wanda ake aiki da intanet. Jama’a daga sassan duniya suna
samun damar sada zumunci ta hanyar tattaunawa, wato, ta hanyar yin Magana ko
kiran bidiyo (Ɓideo Call) ko kuma tattaunawa ta
hanyar musayar saƙo, wato, chats (Maimota,
2021: 121-122)
2.1 Ƙagaggun Labaran Hausa na Shafukan Sada Zumunta na Intanet
Ƙagaggun Labaran Hausa
na shafukan sada zumunta, waɗanda da Turanci ake kira Online Hausa Noɓels, ƙagaggun labarai ne da ake rubutawa a
shafukan sada zumunta na zamani. ana rubuta su yawanci a wayoyin hannu tare da
amfani da Cibiyar sadarwa wadda take amfani da intanet. Bayan an rubuta,
marubutan na watsawa a ƙananan shafukansu ko su tura a ƙungiyoyi na Fezbuk a Waz’Af da sauransu (Maimota, 2021)
2.2 Samuwar Ƙagaggun Labaran Hausa a Shafukan Intanet
Ana iya cewa an fara samun labaran zuben
Hausa a farfajiyar Intanet a tsakanin shekarar 2003 a majalisar marubuta ta
Intanet, wato yahoo group wanda Farfesa Abdalla Uba Adamu ya
buɗe wanda ya kasance wani zaure da ya tattara
marubuta na Adabin Kasuwar Kano, domin tattaunawa da gyara da kawo duk wasu
hanyoyi da za su ciyar da rubutu da marubuta gaba. A wannan zaure a karon farko
aka fara samun rubuce-rubuce na Hausa a Intanet, har aka kai ga fara samun ‘yan
gajerun labaran zube na Hausa wanda da haka ne ake alaƙanta samuwar rubutun zuben Hausa a Intanet da majalisar marubuta ta intanet
(Kabir 2022).
Labaran zuben Hausa a farfajiyar Intanet da
ake kira littattafan “soshiyal midiya” ko
littattafan “intanet” waɗanda tauraruwarsu ta fara haskawa tsakanin
shekara ta 2013-2014. Hakan ya biyo bayan sallacewar da ake ganin Adabin
Kasuwar Kano ya fara yi musamman daga tsakanin shekarun 2008-2018
(Sabe, 2019:419-420) Maimota (2021:121) ta tabbatar da haka in da ta ce “…
karance-karance ta Intanet ya karaɗe duniya baki ɗaya. Wannan na daga cikin dalilan da suka sa
aka sami koma-baya ƙwarai a harkar rubutu da karatun littattafan ƙagaggun labarain Hausa. …”
Dangane
da samuwa da yawaitar labaran Hausa a kafar intanet Maimota (2021) da Kabir,
(2022) sun tabbatar an fara samun wannan nau’in adabi da marubutansa a shekarar
2013.
2.3 Marubutan Soshiyal Midiya
Marubutan intanet ko onlayin ko soshiyal
midiya, marubuta ne da ke sharafinsu na rubutu a farfajiyar intanet,
galibinsu matasa ne da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 30. Sannan mata sun fi yawa
duk da cewa akwai maza amma idan aka haɗa su da yawan marubuta mata, haƙiƙa mazan ‘yan ƙalilan za a kira su.
Yawancin lokuta ba a lokaci ɗaya suke yin rubutunsu ba, suna yi ne kaɗan-kaɗan suna saki a kafofin sadarwa da suke amfani da su domin makarantansu su
karanta, irin su Fesbuk, Wassaf, Watfad, Telegiram, Manhajar Bakandamiya. Wasu
labaran na kyauta ne, yayin da wasu kuma na kuɗi ne, amma ko na kuɗin wani lokaci sukan
ba da ɗanɗanon wasu shafuka na labarin kyauta ga
makarantan, abin da suke kira (free pages).
Sannan galibi ba su sanya sunayensu na ainahi
a labaran, sai dai su saka wasu sunaye na daban da ke nuni da inkiya ko alkunya ko kyankyanta.
Ga yadda wasu daga cikin sunayen suke da littattafan da suka rubuta:
· Benazir Omar - Ke Ce Gudaliya
· Umm Jeddah - Laifi
· Asisi B. Aliyu - Fulanin Birni
· Umm Asgar - Maryamu
· Maman Haneef - Mai Gaskiya
· Haupha - Muguwar Yaudara
· Maman Nusaiba - Hafsat
· Zulaiheart Rano - Sargarta
· Nabiya Sani - Ɗan Kidnapping
· Mai Dambu - Baƙin Haure
· Ummu Nasmah - Jalala
· Ɗeyyersherthul Humaerath - Ɓiɗeen
· Momyn Ahlan - Colonel Ubaidullah
· Umma Muhammad - Wutar Kara
· Yareema Saheed - Zanen Ruwa
· Autar Mama - Dr Yasmeen
· Maman NurulHuda - A Kan Matata
· Aunty A’isha JB - Amnoor
· Fatey Zahraah - Hooriyah
· Princess Amrah - Dare Dubu (Ibrahim 2019, Maimota, 2021, Kabir 2022, Indabo 2024).
2.4 Bangwayen Labaran Intanet da abin da suka ƙunsa
A wannan ɓangaren an kawo nau’ukan wasu labaran zuben Hausa na Intanet da suka samu a ƙarni na 21, an kuma bayyana yadda manufar labaran ke yin hannun riga da hoton jikin bangon.
a. Littafin Mamana ce na Hauwa’u Salisu (Haupha)
Labarin wata yarinya ce mai suna Halimatu
Aliyu da aka fi sani da (Amrah), Halimatu ta kasance ɗiya ga mutum biyu masu matsala ta musamman, domin mahaifiyarta mahaukaciya
ce, mahaifinta kuma kurma ne, sannan gurgu ne.
A gefe ɗaya kuma akwai wani ɗan sarki mai gadara
marar tausayi, da hanya ta biyo da shi ta ƙauyen su Halimatu abin tsautsayi mahaifiyar Halimatu ta gitto masa a titi
shi kuwa ya mareta. Ita kuma Halimatu ta sha alwashin sai ta rama wa
mahaifiyarta marin komai daren daɗewa.
b. Littafin Hafsat na Sarat Alƙasum
(Maman Nusaiba)
Yana ɗauke ne da labarin tsantsar soyayya da Hafsat ta yi, duk da tsananin son
masoyinta da take a ƙarshe ba ta aure shi
ba, sai dai ta auri wani daban, shi kuwa ya yi ta azabtar da ita har sai da ta
gwammace kiɗa da karatu.
c. Littafin Sangarta na Zulaiheart Rano
Labari ne a kan wata sangantacciyar budurwa
mai suna Ameesha wadda mahaifinta ya shagwaɓata gaya, babu abin da mahaifinata bai iya yi a kanta ya zaɓi ran kowa ya ɓaci har da mahaifiyarta matuƙar dai ita za ta yi
farin ciki. Ganin tsananin so da mahaifinta ke mata, wanda har ya kai ta
sangarce ya sa abokin mahaifinta ya sa aka kaɗe ta da mota, wanda sanadin haka ta gamu da ciwon mantuwa, wato,
(Loose of Memory).
d. Littafin Ɗan
Kidnapping na Nabiya Sani
Labarin wani mutum ne mai garkuwa da mutane
da ya kasance yana da fuska biyu, wato a cikin al’ummar gari da ‘yan uwan shi.
Amma a baɗini ƙasurgumin mai laifi ne wanda ke aikata ta’addancin garkuwa da mutane da
sauran ayyuka na ɓir.
e. Littafin Toufeeƙ na
Hafsat A. Garkuwa (Momyn Seeyamah)
Labari ne da ake gina shi kan soyayya a
gefe ɗaya kuwa shi masoyin
wato Taufeeƙ ya jarabtu da tsananin shan taba
sigari, wanda ta kai har idan bai sha sigari b aba ya samun nutsuwa. Lamarin da
a ƙarshe sigarin ta illata mashi lafiyarsa abin
da ya yi sanadiyyar zama ajalinsa. Sai dai a jikin bangon sai aka sanya wani jarumin fim ɗin Indiya da yake
fitowa a fina-finai masu dogon zango kuma a bangon yana cikin walwalarsa.
Labari ne na wasu masoya guda biyu wato
Falmata da masoyinta kuma mijinta Doctor Hassan wanda suke matuƙar son juna kamar su mutu, sakamakon amincewa da suka yi da juna, hakan ya
samo asali ne sanadiyyar tsananin ƙiyayyar
duk ‘yan uwanta a kan Hassan domin kuwa babu mai ƙaunarsa, ita ce dai ta kafe sai ta aure shi, kuma ta samu nasarar cikar
burinta, sai dai katsam da rana tsaka mahaifin Hassan ya yi ɓatan dabo, yayin da shi kuma Hassan ya mayar
da akalar zargin ɓacewar mahaifinsa kan
mahaifan Falmata, abin da ya ɗaure mata kai matuƙa, kuma a ƙarshe ya rusa zaman
jindaɗin da suke yi na
masoya, zuwa tsantsar ƙiyayya.
Shi ma a bangon wannan littafi hoton wani
jarumin Indiya ne aka sanya a matsayin likita Hassan wato Doctor Hassan, maimak a ga hoton
Bahaushe.
f. Littafin Matar Police na Aisha Sani Abdullahi (Ɗeyyersherthul – Humaerath).
Labari ne da aka gina kan tsantsar soyayya da
yarinta ta matar wani ɗan sanda
sakamakon ƙuruciya da ana iya
kiranta barkwanci zalla.
g. Littafin Baƙin Haure na Ramlat Manga (Mai Dambu)
h. Littafin Gawurtaccen Soja ko Colonel Ubaidullahi
i. Littafin Ƙaddarata ce na Fatima Bello Bala (Zahrah BB)
Labari ne a kan auren Bazawara, ya shafi irin
tataɓurzar da ake yi da wasu iyayen waɗanda ke hana ‘ya’yansu su auri matar da ta taɓa yin aure a yayin da za su auren farko. Haka
zalika yadda wasu matasan su ma ba su iya auren Bazawara, wato abin ya shi
fifita matsayar al’ada sama da halascin abun a addini.
Amma a jikin bango sai aka saka hoton
wata Baturiya tsaye a cikin fulawoyi da furanni ta rufe fuskarta da hula malfa.
Idan aka yi duba a tsanaki dangane da bangwayen
littattafan labaran zuben Hausa na intanet a ƙarni na 21, za a ga cewa galibi bangwayen littattafan daban, haka alƙiblar labaran daban, domin a yawancin lokuta babu dangantaka kowace iri
tsakanin abin da ke jikin bango ko bangayen littattafan da kuma labaran.
Sanya hotuna na wasu al’umomi da ba Hausawa
ba na iya zama ƙalubale ga karɓuwar labari musamman ga wanda bai waye da
yaya hakan ke faruwa ba. Domin za a iya tsammanin labarai ne aka yi da Hausa, amma ba a kan Hausawa ko ƙasar Hausa aka gina shi ba. Wato kamar an
rubuta labaran ne kaɗai da harshen Hausa,
amma ba labarai ba ne da suka shafi Hausawa ko waɗanda aka gina kan al’ummar Hausawa ba. A ɓangare ɗaya wannan nazari ya fahimci akwai tasirin wasu al’ummomi da ba
Hausawa ba a labaran musamman yadda galibin labaran suke yin
hannun riga da tarbiyya da al’ada da tsarin zamantakewar Bahaushe. Haka ne ya
sanya ake ganin bangayen littattafan daban, labaran littattafan daban. Wasu
kuma labaran fassararru da baddalallun labaran da littattafan ƙasashen ƙetare ne musamman
Indiya da Amurka da Turkiyya da Sin sai ɗauki al’adun waɗannan al’ummu a
jingina a ba wa Hausawa. Wasu mawallafan kuwa son kwalliya ko sha’awar sanya
hoto mai kyau ne yake sanya wa suke ɗaukar hoton jarumai mata da maza na Indiyawa ko Larabawa ko Amurkawa su
sanya shi a bangon littafinsu, alhali labarin an gina shi ne kacokan kan
Bahaushiyar al’ada. Wasu ma ba su san ko hoton waye ba, kawai dai za su sanya
mai aikin na’ura mai ƙwaƙwalwa su ce a yi masu bangon littafi mai kyau. Wani lokaci ma akan sake
tsara hoton ta yadda akan sanya wa jaruman kayan da nufin su ne taurarin da ke
cikin labarin Hausawa, wani lokaci kuma akan bar Jaruman da kaya ko shigar da
suke yi a wani fim. Misali a littafin “Abba Ne” na Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba) jarumin Indiya ne Allu Arjun a matsayin Abba a hoton
bangon littafin, sai hoton wata jinjira da aka nuna
yana ɗauke da ita.
Haka a littafin Hauwa’u Salisu (Haupha) a
bangon littafin hotunan jaruman Indiyawa ne mata da yawa, aka sanya wato yadda
suka fito a wani fim.
Haka a littafin Momyn Ahlan wato DSP Aliyu Haidar hoton jarumin Indiya ne mai suna Ɓijaya Hoon Surya hoton jarumin Indiya ne da irin shigar da ya yi ta Ɗan Sanda inda motarsa a cikin fim ɗin Main Hoon Surya ko (Narasinham\Singam 2)
Kammalawa
Wannan bincike an gudanar da shi domin
a haska yadda mawallafa labaran Hausa na shafukan intanet ke sanya hotunan
bangwan labarai da ba su yi daidai da ƙunshiyar labarin da suka kawo ba. Wannan dalili ya sa aka kira
takardar da sunan “Ƙwai Daban Abin
Cikin Ƙwan Daban.” An kuma yi
tsokaci kan yadda a duniyar ilmi tsarin bangon littafi yake, wato ana sa ran
hoton da aka gani ya zama ya haska labarin da za a tarar.
Wannan bincike ya gano cewa marubutan
soshiyal mediya un fi mayar da hankali wajen sanya kyawawan hotunan jaruman
finafinan ƙasashen ƙetare da wasu hotuna da suke samu a rumbunan samar da hotuna a kafafen
intanet. Binciken ya fahimci ko da yanayin ƙasa ne sun fi sanya ƙasashen waje waɗanda ba su yi kama da ƙasar Hausa ba. Domin a fahimci yaya abin yake takardar ta waiwayi ayyuka da
aka yin a ilmi da suka shafi shafukan sada zumunta na intanet an kuma bayyana
ma’anar labaran shafukan sada zumunta da taƙaitaccen tarihin samuwarsu da marubuta wannan, adabi. A yayin tsokaci an kawo
misalan labarn da ke ɗauke da matsalar da wannan bincike ya tattauna. Wato an
bayyana ƙunshiyar labaran an
kuma kawo hotunan bangon kowanne. Daga ƙarshe aka kawo rataye na samfuran waɗannan bangwaye.
Manazarta
Abu
Sabe, B. (2019) “Adabin Kasuwar Kano” Samuwa da Jigogi da Siffofi, Cikin Labarn
Hausa A Rubuce 1927-2018. Shf 396-432 Edita, Malumfashi, I. Zaria: Ahmadu
Bello University Press and
Publishers.
Diso,
A. I. (2016) “Hanyoyin Tallata Ayyukan Marubuta a Yanar Gizo-Gizo.” Takarda da
aka Gabatar a Taron Ranar Marubuta ta Duniya. 26 ga Maris, Kano: Gidan Mambayya.
Ibrahim,
B. (2019) “Mata Marubuta a Ƙasar Hausa.” Cikin Labarin Hausa A Rubuce 1927-2018. Shf
na 452-480. Edita Malumfashi, I. Zaria: Ahmadu Bello University Press and Publishers.
Ibrahim, B. (2009) “Gudummuwar Mata Ga Haɓaka Rubutaccen Adabin Hausa” Kundin Digiri Na
Uku:Sashen Harsunan Nijeriya Sokoto Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Kabir, J. (2022) “Adabin Bariki Tsokaci Kan
Sabon Rubutun Zuben Hausa a Ƙarni na 21.”Kundin
Digiri Na Biyu.Sashen Harsunan Nijeriya Da Kimiyyar Harshe:Kaduna Jami’ar Jihar
Kaduna
Maimota,
A. S. (2023) Ƙagaggun Labaran Hausa a Ƙarni na Ashirin da Ɗaya (Tare da Hanyoyin Nazarinsu). Kano: Gidan
Dabino.
Maimota,
A. S. (2021)”Kwatanta Wasu Littattafan Ƙagaggun Labaran Hausa Da Wasu Ƙagaggun
Labaran Hausa Na Shafukan Sada Zumunta Na Intanet” Kundin Digiri Na Uku
Sashen Harsunan Nijeriya: Kano, Jami’ar Bayero.
Shehu,
M. da Rambo, R. A (2019) “Shafin Sada Zumunta na Was’Af (WhatsApp)”Tasirinsa ga
Lalacewar Tarbiyyar ‘yayan Hausawa.” Journal of Humanities and Cultural
Studies. Vol 1, Issue 6. Kenya: East African Scholars.
Yakasai,
S. A. (2018) “Alaƙar Mawaƙi da Al’umma: Tsokaci Cikin Shafukan
Zumunta a Kafar Sadarwa ta Intanet.” Maƙala da aka Gabatar a Taron Dangin Juna Masoya Ala Faundation.
Asabar, 23 ga Yuni, 2018. Kano: Gidan Mambayya.
Yakasai,
S. A. (2024) “Digital Electronic Deɓices, Growing Dominance of Writing and the Preserɓation of Language and
Culture in Hausa Society.” 47th Inaugural Lecture. 18th July,
2024, Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Tattaunawa da marubuciya Aysha JB ta kafar
WhatsApp a ranar 1/03/2024
Tattaunawa da marubuciya Zahra Abdul (Momyn
Ahlan) ta kafar Wassaf a ranar 03/03/2024
Tattaunawa da marubuciya Aisha A. Garkuwa ta
kafar Wassaf a ranar 04/03/2024
Tattaunawa da marubuciya Hauwa’u Salisu
(Haupha) ta kafar Wassaf a ranar 05/03/2024
Tattaunawa da marubuciya Fatima Bello Bala ta
kafar Wassaf a ranar 12/03/2024
Tattaunawa da marubuciya Nadiya Sani ta kafar
Wassaf a ranar 12/03/2024
Tattaunawa da marubuciya Rasheeda Usman (Ummu
Nasrah) ta kafar Wassaf a ranar 15/03/2024
Tattaunawa da marubuciya Aisha Sani Abdullahi
ta kafar Wassaf a ranar 16/03/2024
Tattaunawa da marubuci/ɗanjarida Adamu Yusuf Inabo ta kafar Wassaf a ranar 17/03/2024 – 20/03/24.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.