Ticker

6/recent/ticker-posts

Farauta da Wasu Al’adunta a Gundumar Sakkwato

 Farauta wata daɗaɗɗiyar hanya ce da ɗan’adam yake bi domin ya nemi abinci. Masana sun haƙiƙance cewa ita ce sana’a ta farko da aka fara aiwatarwa kafin a gano dabarar noma. Wannan hanya ta neman abinci, cike take da al’adu waɗanda masu yin ta suke bi yayin gudanar da ita. Wannan sana’a a halin yanzu ja baya take yi domin wahala, da kuma rashin tabbas da ke tattare da aiwatar da ita, ga kuma yawan salwantar dazuzzuka da ake samu sakamakon sare itatuwa barkatai don makamashi, da kuma faɗaɗa gonakin noma wanda kan haifar da ƙarancin dabbobin dawa. Da wannan dalili, yanzu al’adun da ke cikin farautar sai ja da baya suke yi, suna raguwa, waɗansu ma suna ɓacewa gaba ɗaya. Da wannan dalili ne nazarin ya yi amfani da ra’in ‘Adana al’adu’. Tunanin ra’in ya tafi a kan cewa al’ummar da take son cigaba, to lalle ne ta kyautata hanyoyin da za ta adana al’adunta domin guje wa salwantarsu. Wannan dalili ne ya sa wannan muƙala ta yi ƙoƙarin nazarin waɗannan al’adu, ganin cewa a inda aka fito, ba a yi wani bincike mai zurfi ba dangane da al’adun. Wannan yunƙuri zai taimaka wajen rage salwantar al’adun, don kuwa za a adana su a rubuce. Binciken ya ziyarci mafarauta a garuruwa daban-daban domin samun muhimman bayanai game da sana’ar. Amfani da dabarar samun bayanai daga masu abin ya zama wajibi ganin cewa su ne malaman dawa, waɗanda kuma ke aiwatar da sana’ar. Binciken ya gano cewa haƙiƙa wannan sanaa a yanzu tana fuskantar barazana gushewa domin masu aiwatar da ita sun ƙaranta. Yawan faɗaɗa gonakin noma da saran itatuwa barkatai domin makashi da kasawar sana’ar wajen biyan ɗimbin buƙatun mutane na daga cikin dalilan da suka sanaar take ja da baya.

farauta

Farauta da Wasu Al’adunta a Gundumar Sakkwato

DR. MUSA FADAMA GUMMI

Email: gfmusa24@gmail.com

Phone No.: 07065635983

1.0 Gabatarwa

Gundumar Sakkwato tana nan shimfiɗe a yankin Arewa maso yamma na Arewacin ƙasar Nijeriya. A cikin gundumar ne ake samun tsofaffin daulolin nan na ƙasar Hausa, wato daular Zamfara, da Gobir , da Kabi. A wannan yanki ne kuma ake samun cibiyar shahararriyar daular nan da ta wanzu a ƙarni na 19, wato daular Sakkwato wadda Shehu Usmanu ɗanfodiyo ya jagoranta. Gunduma kalma ce ta Hausa da nufin wani yanki na ƙasa. Daidai yake da a ce lardi wanda kalma ce ta Larabci da take nufin ƙasa. Gundumau Sakkwato a wannan muƙala na nufin lardin Sakkwato wanda ya haɗa da Kabi da Zamfara.[1] Gundumar ta faɗo ne a Sabana ta Sudan da kuma Sahel a wani sashe. Duk da cewa wannan gunduma takan yi fama da ƙaranci ruwan sama daga lokaci zuwa lokaci, akwai wadatar ruwan sama gwargwado ko da yake ba yakan wuce santimita ɗari ba a shekara, sai dai ƙasa da haka. Saboda albarkar ruwa da kuma dazuzzuka da Allah cikin nasa iko ya saka a yankin, ana samun dabbobi na dawa waɗanda suke rayuwa a cikin dazuzzukan yankin waɗanda misalinsu ya haɗa da Gundumi, da dajin Rugu da sauransu.

Dabbobin da ke rayuwa a cikin dazuzzukan wannan gunduma ta Sakkwato sun haɗa da giwa da zaki da gwanki da barewa da gada da ɓauna da batsiya da maje da zomo da sauransu. Ta fuskar tsuntsayen dawa da ake samu a dazuzzukan da ke faɗin gundumar sun haɗa da Tuji da jimina da zabo da fakara da badara da gaba da sauransu, waɗanda ake samu a tudu; da kuma ƙirinjijiya da takau da taka-bado da balbela da zalɓi da dunya da sauran ire-iren su waɗanda ake samu a fadama.

Dubin albarkar dabbobi da tsuntsaye da Allah Ya ajiye a duk faɗin wannan gunduma, ba abin mamaki ba ne idan aka ce akwai mutane da dama waɗanda suka duƙufa wajen aiwatar da sana’ar farauta a wannan gunduma. Farauta sana’a ce da ke samar da abinci ga masu aiwatar da ita da kuma sinadarai na haɗa magungunan gargajiya ta fuskar kitse, fata, gashi, da sauran abubuwan dabbobi da ake amfani da su wajen haɗa magunguna.

Lura da muhimmancin wannan sana’a ga al’umma, masana da dama sun yi rubuce- rubuce a kan farauta. Daga ciki akwai Rimmer, da wasu (1966), da Alhassan, da wasu (1982), da Madabo, (1979), da Garba, (1991). Idan aka dubi waɗannan ayyuka, za a fahimci cewa ba su yi bayani mai zurfi ba dangane da al’adun da ke cikin wannan sana’a ta farauta.Wannan kuwa giɓi ne mai zurfi da ya kamata a cike, idan aka yi la’akari da yadda farauta da masu aiwatar da ita suke raguwa. Wannan muƙala ta yanzu, wani yunƙuri na cike wannan giɓin.

2.0 Ma’anar Farauta

Farauta sana’a ce wadda ta daɗe ƙwarai ana aiwatar da ita domin neman abinci. Hasali masana suna da ra’ayin cewa farauta ita ce sana’ar farko da ɗan’adam ya fara yi a doron ƙasa domin neman abinci (Alhassan, da wasu (1982:39). Ta fuskar ma’ana kuwa masana da dama sun faɗi ra’ayoyi da dama dangane da abin da ake kira farauta. Alhassan, da wasu (1982:39) suna ganin cewa farauta ita ce sana’ar kambaɗar naman daji don ƙarin abinci, da kariya. Garba, (1990:49) kuwa a Ƙamus na Hausa cewa ya yi farauta kalmar suna ce a rukunin ta mace wadda take nufin shiga daji neman dabbobi a kashe don nama. A Ƙamusun Hausa kuwa cewa aka yi farauta ita ce yawon harbi ko kama neman naman daji.[2]

Idan aka yi la’akari da abin da masana suka kawo, ana iya cewa farauta tana nufin kambaɗar naman daji, dabba ko tsuntsu domin kama shi ta hanyar amfani da dabbar farauta wato kare ko ta hanyar yin amfani da makami kamar bindiga, da kwari da baka, da kokara da dai duk wani makami, ko ta hanyar amfani da tarko, domin a ci ko a sayar ko a sarrafa a matsayin magani.

3.0 Ire-Iren Farauta

Alhassan, da Wasu (1982:40) sun kawo hanyoyin gudanar da farauta da suka ce ire-ire ne. Akan sami mafarauci guda daga shi sai karensa su fita farauta. Mafarauta da dama ko masu yawa na iya fita farauta bayan sun gangami da yekuwa na inda za a tafi, da lokacin da za a fita. Ana kuma samun mafarauta yara su yi ƙungiya, su fita domin kama ɓeraye da bushiyoyi da zomaye.

Duba ga irin bayanan da aka tattara daga malaman farauta na yankin gundumar Sakkwato, wato mafarauta. Wannan bincike bisa nazari ya fahinci cewa, ana iya kasa nau’ukan farauta zuwa manyan rukuna guda biyu wato farauta wadda ake aiwatarwa a tudu da kuma wadda ake yi a fadama.Binciken ya duba wannan rabe-raben kamar haka:

3.1 Farautar Tudu

Irin wannan farauta kamar yadda sunanta ya nuna, nau’i ce ta farauta wadda ake aiwatarwa lokacin rani, sa’ilin da babu sauran aikace-aikace na gona. Akan tafi jeji ne domin neman dabba ko tsuntsun da za a kama. Farautar tudu a bisa faifan wannan nazari, tana da nata nau’uka kamar haka:

3.2 Babbar Farauta

Farauta ce gagaruma wadda ake shiryawa ta hanyar gayyatar mafaruta daga wurare daban-daban domin su halarta. Misali Maidaji na shiyoyi ko yankunan wannan gunduma suke shirya irin wannan farauta sai a aika goron gayyata zuwa wurare daban-daban. Wani lokaci irin wannan gayyatar takan haɗa har da maƙwabta wannan yanki. Mafarauta daga irin Ƙwanni, da Gaya, da Maraɗi na jamhuriyar Nijar duk akan gayyace su a irin farauta babba musamman idan za a je kudanci ne inda ake samun daji sosai. Mutane sukan yi tururuwa su shiga daji a inda za a yi tsawon kwanaki ana kambaɗar dabbobi da tsuntsaye don a kashe ko a kama da rai. Misalin dazuzzukan da akan aiwatar da wannan farauta cikin gundumar Sakkwato ya haɗa da dajin Gundumi, da dajin Rugu, da dajin Kibli, da dai sauran su. (Hira da Ango Ɗanillela Falale)

3.3 Sa-rani

 Ra’ayin mafarauta ya bambanta dangane da wace farauta ce ake kira sa-rani? Akwai masu ra’ayin cewa sa-rani farauta ce ta mutum guda sai kuwa karensa, kuma ana fita aiwatar da ita ne da yamma. A wani ƙauli kuwa, ana ganin sa-rani farauta ce wadda yara suke fita daji da ke kusa da gari wadda a al’adance, yaran sukan fita da yamma. Wasu mafarautan kuwa gani suke cewa sa-rani farauta ce wadda yara tare da manya suke yi, a fita daji da yamma domin neman abin sakawa a miya. Dangane da lokacin fita sa-rani, wasu ma gani suke cewa akan fita daji kowane lokaci aka ga dama. Bambancin sa-rani da farauta babba shi ne a sa-rani, ba a gayyatar mutane daga sauran garuruwa maƙwabta. (Hira da Sama’ila Fingilla, unguwar Kabobi, Gummi)

3.4 Farautar Biki

Farauta ce da ta yi kama da ta sa-rani sai dai ita wannan ana shirya ta ne idan wani mafarauci zai yi aure ko aka yi masa haihuwa. Akan fita daji tun da sassafe yadda ko da za a ɗaura aure ko a raɗa wa abin da aka haifa suna, har an dawo daga farautar. Duk dabba ko tsuntsu da aka kama ana bayar da shi ne ga ango ko wanda aka yi wa haihuwa a matsayin gudunmawa. (Hira da Maidaji Muhammadu Sani, Ɗanmadi, ƙasar Tambawal)

3.5 Farautar Haƙa Tarko

Nau’i ne na farauta wadda galibi ba taro ake yi ba wajen aiwatar da ita. Mutum guda ko biyu suke zuwa daji inda suka san dabbobi ko tsuntsaye suna zuwa kiwo, su haƙa tarko. Kayan haƙo ko tarkon da za a yi amfani da shi kan bambanta dangane da irin abin da ake son a kama. Ana amfani da guru domin kama nau’in dabbobi kamar gada, da barewa, da maje, da sauran su. Idan kuwa tsuntsu ake son a kama kamar zabin daji, da fakara, da badara, da makamantansu, ana amfani da tarko da ake kira asuta. Ana amfani da katawa domin kama ƙananan dabbobi kamar gafiya, da zomo, da ɓera, da sauransu. (Hira da Sama’ila Fingilla, unguwar Kabobi, Gummi)

3.6 Farautar Fadama

Farauta ce da akan gudanar da ita a bakin kogi da tafukka ko duk wani ruwa da aka san tsuntsaye suna taruwa don kiwo ko kuma shan ruwa. Farautar ba ta taron jama’a ba ce, mutum ɗaya ko biyu zuwa uku sukan aiwatar da ita kuma suna kama tsuntsaye ne kawai ba da dabbobi ba. Akan yi farautar da rana ko da yamma kuma ta fi gudana yawanci a lokacin damina don kuwa a lokacin, tafukka da gulaben yankin sukan cika da ruwa amma da zarar rani ya kama, da yawa-yawan tafukkan da gulabe kan ƙafe don haka tsuntsayen sai su ƙaura. Domin aiwatar da farautar, ana amfani da tarko na raga ko kalli wanda ake tare wuri da shi. Mafarautan sukan yi shigar burtu. Burtun ya yi kama da kanun tsuntsaye kamar dunya, da ƙirinjijiya. Ana saka burtun ne a ka sannan a duƙa ana laɓaɓe-laɓaɓe ta hanyar tayar da kan burtun, ana noƙe shi yayin da aka tasar wa wurin da gungun tsuntsayen yake. Tsutsayen za su zaci burtun nan kan tsuntsu ne ɗan uwansu. Da zarar mafarauci ya kusanci gungun tsuntsayen, sai ya harba bindigarsa ta toka. Harbin zai kashe wasu daga cikin tsuntsayen, yayin da wasu za su faɗa wa tarkon da aka haƙa na raga lokacin da suke yunƙurin tashi domin kuɓuta. (Hira da Maidaji Muhammadu Sani, Ɗanmadi, Tambawal)

4.0 Kayan Aikin Farauta

Kafin a fita farauta, ana yi mata shiri na musamman. Maidaji na yankin da za a yi farauta yake da haƙƙin shiryawa da aza farauta ta hanyar sanar da mafarauta ‘yan uwansa idan aka haɗu a kasuwa, da yake a cikin kowace kasuwa za a tarar mafarauta suna da rumfa inda nan ne dabar da suke haɗuwa kowace ranar kasuwa. Da zarar labarin shirya farauta ya kai ga mafarauci, ba abin da zai yi sai tanadar kayan aiki. Daga cikin kayayyakin aiki da ake tanada akwai kare ko karnuka domin shishita shi ga dabba mai gudu kamar zomo da barewa. Ana kuma tanadar kokara wadda wata sanda ce ta jifar naman dawa, da kuma dukarsa. Burgami yana da amfani domin a ciki ake ajiye ‘yan ƙananan namu da aka kama. Ana tanadar wuƙa domin yankan dabba da feɗe ta. Takobi da adda ana tanadar su domin saran naman da mutum (abokin gaba), lokacin da faɗa ya ɓarke tsakaninsu. Gatari da gitta suna da muhimmanci wajen saran nama, kwari da baka kuwa don harbin namun daji. Mafarauta kan tanadi usur ko tabusa, da kuma ƙaho domin amfani da su wurin kiran karnuka da sanar da inda farautar take ga wanda ɗemuwa ta kama. (Hira da mafarauta daban-daban)

4.1 Shirin Fita Farauta

Duk lokacin da ranar da aka aza farauta ta ƙarato, mafarauci kan yi shirye-shirye na tafiya. Farko yakan tanadi guzuri na abinci da kuɗi musamman idan farautar babba ce wadda ake kwana da kwanaki a cikin jeji, nan ake kwana, nan kuma ake tashi. Bayan tanadar kuɗi ko abinci, abu na gaba da sukan tanada shi ne kayayyakin tsari da kariya daga dukkan abokan gaba, dabba, aljani ko mutum. Farauta sana’a ce ta ‘yan tauri da ma wasu waɗanda ba ‘yan tauri ba ne, sha’awa ce ta ingiza su kutsa kai cikin sana’ar. Da ɗan tauri da ma wanda ba ɗan tauri ba, mafarauci yakan tanadi maganin ƙarfe ko da kuwa na ƙanƙanin lokaci ne, kamar dadale. Ba tauri kaɗai ba mafarauta kan tanadi asirai kamar baduhu wanda kan sa mai shi ya ɓace da zarar ya razana ko ya ji tsoro, ko hankalinsa ya tashi ko ya nasa a zuciyarsa yana son ya ɓace. Ana neman wannan ne domin kariya daga abokan gaba musamman miyagun dabbobi kamar ɓauna, da zaki. Wasu daga cikin mafarauta kan mallaki layar zana wanda asiri ne da kan sa mai shi ya ɓace amma bai gurgusawa daga wurin da yake. Da zarar ya ɗaga daga inda ya ɓata, za a iya ganinsa. Magani ne da ake haɗawa da fakara domin ita take da wannan ɗabi’a. (Hira da Dantaro, Ɗanfaƙo, Gummi)

4.2 Shiga/Sutura Ta Farauta

A da can kafin wadatuwar yadi irin na zamani, mafarauta kan ɗaura kulsa ne wanda ake yi da fatar dabbobi. Ana ɗaura falle ɗaya domin a rufe al’aura daga gaba, sannan a ɗaura wani fallen daga baya domin rufe ɗuwawu in ya so a bar kwatolo a fili. Wani lokaci kuwa akan rataya warki don rufe saman jiki da kwatolo na raɓi ɗaya. Bayan da aka sami wadatar sutura ta zamani, suturar mafarauci ba ta wuce taguwa ‘yar shara wadda galibi zaure ce kuma yawanci da yadi baƙi ake ɗinka ta. Tsayin taguwar ba ya wuce iya guiwa ko cinya. Sukan sa gajeren wandon da tsayinsa iya guiwa ne. Ana rufe kai da wata hula irin ta saƙi, haɓar kada mai launi baƙi.

Takalman mafarauci ba sa wuce ɓantale waɗanda a da can farare ne na fatar shanu. Zamananci ya kawo ɓantale na danƙo, irin wanda ake yi da tayar mota. Sukan ratayo burgami a gefen kafaɗa, a kuma ratayo usur a wuya. A daidai ƙugu da dantsen hannaye guda biyu kuwa, suna ɗaura layu da daguma da guraye da karhuna. (Hira da Maidaji Muhammadu Sani Ɗanmadi, Tambawal)

 

5.0 Wasu Al’adu A Cikin Farauta

Sana’ar farauta ƙunshe take da al’adu daban-daban. Waɗannan al’adu sun haɗa da kiɗa, da ɗaurin daji, da tsaraka, da sauransu. Kafin a ɗauke su ɗaya bayan ɗaya ya dace a fara kawo ma’anar al’ada.

5.1 Ma’anar Al’ada

A ƙoƙarinsa na bayyana ma’anar al’ada, Bunza, (2006:xxxii) cewa ya yi al’ada ita ce dukkanin rayuwar ɗan’adam tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa. Ta la’akari da abin da masanin ya faɗa, ana iya cewa al’ada tana nufin hanya ta gudanar da rayuwa wadda aka saba da ita a wata al’umma ta mutane. Hanyar ta gudanar da rayuwa kan shafi kowane mataki na rayuwa kamar haifuwa, da aure da mutuwa. Da yake ana magana ne a kan farauta, al’adun farauta su ne abubuwan da aka saba da su, suka riga suka zama jiki a duk lokacin da za a yi farauta ta yadda idan aka saɓa masu, sai a ga abin bambarkwai. Wasu daga cikin waɗannan abubuwa kuwa sun haɗa da kiɗa, da tsaraka.

5.2 Kiɗa Da Busa

Bisa al’ada, kiɗa da busa suna da muhimanci a sha’anin farauta. Idan za a fita farauta ko da sa-rani ce, mafarauta kan fara kiɗa da bushe-bushe tun gabanin fita daji. Akan yi kiɗa ne domin sanar da ‘yan uwa mafarauta cewa za a fita a fagen daga. Kayan kiɗan farauta sun bambanta daga wuri zuwa wuri. A wasu wurare, komo ake kaɗawa, a wasu wuraren kunkumi suke kaɗawa, yayin da wasu kurya ce kayan kiɗansu na farauta da tauri, kalangu ma wani kayan kiɗa ne na farauta. Kayan bushe-bushe kuwa sun haɗa da ƙaho, da mabusa ta kara, da kuma usur wadda kowane mafarauci kan yi amfani da ita. Kiɗa abu ne mai muhimmanci a sha’ani irin na farauta. Baya ga amfani da shi domin sadar da saƙo, kiɗa yana farkar da maza sannan yana hana wa mafarauta ɓacewa a daji; ko da farautar ta bar wasu a baya suna iya gane gefen da ayarin farauta yake. Haka kuma kiɗa a lokacin farauta kan tayar da namun jeji daga maɓuyarsu, su fito a sarari, karnuka su yi arangama da su.(Hira Dandi Makaɗa, Rijiyar Fari, Gummi)

5.3 Tsaraka

Tsaraka ta samo asali ne daga wani haki da masu sayar da ganye, da fura da sauran kayan cimaka kan ɗiba su saka a cikin ƙwarya ko duk wani mazubin sana’arsu da nufin jawo ciniki ga sana’ar tasu. Bisa ma’ana, CNHN (2016:453) a Ƙamusun Hausa, an bayyana cewa tsaraka ita ce magani da mutum yake yi don samun sa’a ta fuskar ciniki. Wata ma’anar ita ce neman sa’a a wajen kamun kifi. Da yake ba a harkar ciniki da kamun kifi kaɗai ake yin tsaraka ba, ana iya cewa tsaraka na nufin magani da mai sana’a ke yi domin neman sa’a kan sana’arsa koyaushe aka fita wajen aiwatar da ita. Bisa la’akari da yadda mafarauta suke yin tsaraka, ana iya kasa ta nau’uka kamar haka:

5.3.1 Tsarakar Turare

Kafin a fita daji wajen farauta, kowane mafarauci sai ya yi nasa asiri irin na tsaraka wanda ya sani. Misali na wata tsaraka shi ne a sami saiwun jema, da kan tofa wanda ya fara bushewa a haɗa da kashin zomo a dake su tare. Mafarauci zai ɗan shaya da’ira ta ɗan yi rami kaɗan a ƙasa, sai ya ɗauko garin nan ya barbaɗa cikin garwashi yadda hayaƙi zai tashi. Da shi da karnukansa za su shaƙi hayaƙin sosai har sai wutar ta suƙe. Yin haka zai sa a kama zomo. Idan gada ake son a kama sai a nemi kaucin bagaruwa, da kaucin aduwa tare da tagullarta. Dake su za a yi sannan a yi turare kamar yadda aka yi a bayanin da ya gabata. Ita kuwa barewa tsarakarta ita ce a sami kumfa na ruwan gulbi da kaucin tumfafiya, a dake shi. Ana zuba garin a cikin ruwa yadda zai wadaci mutum ya kurkure baki sau uku. Idan aka yi haka ko kiran barewa aka yi za ta zo. (Hira da (Hira da Maidaji Muhammadu Lema)[3]

5.3.2 Tsarakar Addu’a

Wasu daga cikin mafarauta sukan haɗa da addu’a irin ta surkulle wajen yin tsaraka. Misali idan tsarakar kama zabo ake son a yi, ana samun suri (ƙunƙuwa) ƙarama sai a buge ta. ‘Yan hakukuwan da aka tarar a ciki sai a tsince su a haɗa da gindin ciyawar bubburwa uku tare da jar kanwa, a tattauna sannan a fesa a hannu tare yin wannan addu’a.

 Bismillahi, na ɗauri anniyar yi wa nama tsaraka. Idan na yi

 daga nan ban tashi sai zabuwa ta zo, sai ta kawo kanta in yanke .

 (Hira da Ɗantaro, Ɗanfaƙo. Gummi)

Wani misali na wata tsaraka wadda addu’a kaɗai ake yi ba tare da an haɗa da ganyaye ko saiwa na wata bishiya ba ita ce:

 Bismillahi za ni biɗa. Arrahamani na gani

 Alhamdulillahi na samu.

 (Hira da Mamman Karma, Ƙofar Jaro, Gummi)

Ana karanta addu’ar ƙafa bakwai sannan a tofa.

5.3.3. Ɗaurin Daji

A cewar Alhassan da Wasu (1982:40) Kwanaki huɗu gabanin fita farauta, mafarauta kan yi ɗaurin daji. Ɗaurin daji wata al’ada ce mai muhimmanci sosai a sha’anin farauta. Bisa yadda aka saba, Maidaji wanda ya shirya farauta shi yake yin ɗaurin daji gabanin a fantsama cikin daji. Ko baya ga ɗaurin daji da Maidaji yake yi, kusan kowane mafarauci yana da tasa dabara ta ɗaure daji. ɗaurin daji ba wani abu ba ne face wasu dabaru na magani da mafarauta kan yi domin su ɗaure duk wata muguwar halitta ta cikin daji kamar dabbobi da mugun Iska (aljannu) don gudun kar su cutar da wani ko wasu yayin da ake cikin yin farauta, wato a shiga lafiya a ƙare lafiya. Maidaji tun daga gida yake ɗaure daji amma yayin da aka fita a bakin daji, yakan yi wani dodorido da sunan ɗaurin daji.[4] Yadda zai yi kuwa shi ne sai ya sami suri ko wani koren ice, ya duƙa tare da tona ɗan rami inda zai yi duk addu’o’in da ya sani. Ana yin wannan ne a suri ko wani koren ice domin a riya a zuciya cewa yadda suri ko koren ice ba ya motsi, haka miyagun da aka ɗaure ba za su motsa ba har a ƙare farautar. Yayin da Maidaji yake duƙe, sauran mafarauta duƙawa za su yi suna jiran ya ƙare. Da ƙare wannan sai ya rufe ramin sannan ya doki ƙasar wurin da sandarsa ko gatarinsa. Sauran mafarauta da suke duƙe za su yi koyi da shi da hanyar buga makamansu a ƙasa, sannan su fantsama cikin daji, tare da yin ‘yan kuwace-kuwace. ( Hira da Muhammadu Lema, a kasuwar Gummi)

ɗaurin daji na haƙiƙa tun gida ake yin sa ba sai an fita daji ba. Kowane Maidaji yana da tasa dabara ta ɗaure daji. Yadda wani yake yin nasa ba haka wani yake yi ba. Misalin yadda wani yake dabarar ɗaure daji shi ne ana samun allura sai a yi mata kube. Da safe, sa’ilin da rana ta tako Maidaji zai ɗauki allurarsa da kubenta ya nufi bayan gari. Bayan ya fitar da allurar daga kubenta, zai fuskanci gabas, ya karanta wata addu’a ƙafa bakwai, ya tofa ga allurar nan. Mayar da allurar ake yi a cikin kubenta sannan a sami wuri a ɓoye ta ko ya saka ta a burgaminsa. Matuƙar allurar nan tana cikin kubenta, da ikon Allah duk wani mugu ba zai cuta wa kowa ba har a kare farauta. Addu’ar da ake karantawa kuwa ita ce:

 Bismillahi, Uzramaita, umalamaita, wala kinnalaha

 mugu lammai.ƙarfa tanki, muzattanki, kama tanki.

 Manzon Allah ya shiga ni ko in shiga. Daga ruwanai

 sai ruwanai.

 (Hira da Mamman Karma, Ƙofar Jaro, Gummi)

Mafarauta, a ɗaiɗaikunsu, suna da addu’o’i daban-daban da suke yi domin ɗaure daji. Misali na yadda wani kan yi nasa ɗaurin daji shi ne yana karanta wannan addu’a ta surkulle, ƙafa bakwai sannan ya tofa. Addu’ar ita ce:

 Bismillahi na ɗauri anniya.

 Dutci ciki, baƙar akuya cikin ciki take.

 Ba ta haihuwa sai na shiga na fito.

 (Hira da Mamman Karma, Ƙofar Jaro, Gummi)

 Wata addu’ar ta ɗaurin daji wadda ɗaiɗaikun mafarauta suke yi ita ce wadda suke yi kamar haka:

 Bismillahi, izat tanki, ƙafat tanki, tanki tantantan.

 Na ɗaure mugu da jiyojin jikinai.

 Baya zuwa gaba sai dai ya komo baya

 (Hira da Muhammadu Lema)

6.0 Yadda Ake Farauta Jiya Da Yau

Kamar yadda bayani ya gabata, kafin a shiga daji wajen farauta, kowane mafarauci yakan yi tsaraka domin neman sa’a. Maidaji kuwa aikinsa ne ya ɗaure daji, domin neman tsari daga cutarwa kowace iri. Lokacin da ya ƙare, yana dukar ƙasa da makaminsa sannan sauran mafarauta waɗanda suke duƙe sai su yi koyi da shi ta hanyar dukar ƙasa sai ji kake tim! Tititim! Daga nan sai kowa ya miƙe tsaye, a shiga daji neman abinci.

Idan aka fara farauta kowane mafarauci yana riƙe da karensa a hannu ɗaya, makami riƙe a ɗaya hannun. Idan aka tayar da dabba akan sa makami a doke ta in kuwa akwai tazara tsakanin ta da mafarauci, ba abin da zai yi sai ya kai jifa da kokararsa. In ya kasa samun dabbar sai ya shishita karensa gare ta. Da zarar karensa ya zabura ya bi dabbar a guje, sai ya bi su, ya riƙa yi masa kirari.

A lokacin farauta akan sami matsala idan karnuka da dama suka bi dabba suka kama ta sai a rasa karen wa ya fara kama dabbar ? Irin wannan yanayi yakan haifar da yamutsi da ɓataccen faɗa tsakanin mafarauta. Irin wannan yamutsi ne yake sa wani lokaci dabbar farauta ba ta samun yanka sai dai a yi wawarta. Irin wannan lamari Garba ɗanwasa Gummi ya kawo a wani ɗan waƙa tasa da yake cewa:

 Anka koro gwanki cikin ƙarin kwana

 Garba gwanki yaf faɗi kwance yana kuka

 Anka sare gaba, baya ba ta bar motci ba

 Shi da ɗai naman wawa bai samun yanka

 Na Garba sai yab busa usur nai

 Yana busa usur sai matcata nak kawo

 Ana ta saran arna kamag girbin gero.

 (Alh. Garba Ɗanwasa Gummi, waƙar Ɗantaragon Fatara na Lema)

Irin wannan yanayi da Makaɗa Garba ɗanwasa ya kawo a cikin waƙarsa a halin yanzu ana iya cewa ya kau. Hukuma tare da sa hannun shugabannin farauta wato Masu daji sun bi matakai na hana aukuwar faɗace-faɗace da kan kai ga sare-saren juna a lokacin farauta. Haka ma sun yi ƙoƙari suka hana ƙwace a sha’anin farauta. A halin yanzu idan ana jayayya dangane da karen wa ya fara kama dabba, akan kai matsalar a wurin Maidaji don yanke hukunci. Yadda Maidaji yake yanke hukunci shi ne yakan nemi shaidu wanda ya ga abin da ya faru. Idan aka rasa shaidu ko aka rasa gano gaskiyar lamari, ana gilma dabbar a rufe ta da ganye sannan a umurci waɗanda suke jayayya su ƙetari dabbar. Wanda duk ya kuskura ya ƙetari dabbar cikin rashin gaskiya, kwanansa sun ƙare don kuwa mutuwa zai yi. ( Hira da Muhammadu Lema)

A halin yanzu shugabannin farauta kamar Karma da Maidaji suna bin matakan hukunta duk wani marar gaskiya a sha’anin farauta. Daga cikin matakan akwai cin tara mai tsanani ga duk wanda aka tabbatar ya yi ƙwace ko wata yaudara a lokacin farauta. Zartar hukunce-hukunce da shugabanni farauta kan yi haƙiƙa, yana saka tsoro a zukatan mafarauta, yadda a yanzu an rage yawan faɗace-faɗace a lamarin farauta.

7.0 Muhimmancin Farauta

Farauta tamfar yaƙi take don haka ne ake yi mata shiri da fita makamanciyar ta yaƙi. Tun da haka abin yake, ɗaya daga cikin muhimmancin farauta shi ne cewa tana ba da wata dama ko fage na koyon juriya ta wahala, da yunwa, da ƙishirwa. Tana ƙara wa masu yin ta kuzari da bajinta. Farauta hanya ce ta neman abinci, sana’a ce da ke samar da abinci musamman nama wanda yake ƙunshe da sinadarai masu gina jiki da ƙara masa lafiya. Baya ga wannan ta fuskar farauta ana samun kuɗin shiga domin biyan buƙatun yau da kullun na Mafarauta. Don haka ta taimaka wajen samar wa mutane aikin yi, da hana su zaman banza wanda aka ce da yin sa ƙara aikin kishiya.

Mafarauta ba a baya suke ba wajen sha’anin kiwon lafiya na gargajiya. Masana itatuwa ne da kuma amfaninsu don haka suke bayar da magunguna na cututtuka, da na biyan wasu buƙatun rayuwa ga al’umma. Misali sukan bayar da maganin iska, da maganin zaga da maganin tauri. Ko baya ga haka, sana’ar farauta ta taimaka wajen samuwa da bunƙasar wasu sana’o’i na gargajiya. Babban misali a nan shi ne sana’ar ɗan maiganye, ba domin mafarauta ba, da sana’ar ba ta ingantu ba sosai. Haƙiƙa a wajen mafarauta ne ‘Yan masu ganye suke samun kitse da gashi da kashi har ma da sassan dabbobin dawa daban-daban, waɗanda ake amfani da su wurin harhaɗa magungunan gargajiya.

8.0 Sakamakon Bincike

Wannan bincike ya sami nasarar fito da wasu al’adu na farauta a sarari. Yin haka zai taimaka ainun wajen adana waɗannan al’adu musamman idan aka yi la’akari irin barazanar da wannan muhimmiyar sana’a ta ke fuskanta. A halin yanzu, dabbobin dawa sun ƙaranta a dazukan wannan yanki sakamakon yawan saran itatuwa domin faɗaɗa gonakin noma da kuma makamashi. A cikin wannan muƙala, an kawo wasu sunayen daga cikin dabbobi da mafarauta suke kamawa. Yin haka gwargwado, zai adana sunayen waɗannan dabbobin dawa.

9.0 Kammalawa

Wannan muƙala ta yi tsokaci dangane da farauta, yadda take, da yadda ake aiwatar da ita a gundumar Sakkwato. Haka ma an kawo a cikin muƙalar, bayanai dangane da al’adu daban-daban da suka jiɓinci farauta. Waɗannan al’adu sun haɗa da kiɗa da busa a sha’anin farauta, da yadda masu farauta suke shirya wa farauta, da irin tsaraka da suke yi domin neman sa’a a duk lokacin da aka fita nema. Waɗannan al’adu da aka bayyana a muƙalar ba su kaɗai ba ne al’adu da suka shafi farauta ba, don haka ra’ayin wannan muƙala ne cewa a ƙara zurfafa bincike a kan lamarin domin fito da al’adun fili ganin cewa yanzu lamarin farauta sai ja da baya yake yi saboda wasu dalilai kamar ƙarancin dabbobi da dazuzuka ga misali. Idan aka yi haka an kare wannan muhimmin abu daga haɗarin salwanta gaba ɗaya.Wannan ba ƙaramin taimako ba ne ga al’ummar Hausawa masu tasowa, da mazauna birane, waɗanda za su rayu a wani lokaci nan gaba.

 

MANAZARTA

Tuntuɓi mai takarda.



[1] Na ɗauki wannan ra’ayi ne dalilin wata hirar baka da na yi da malamina, farfesa Aliyu Muhammad Bunza. Ya bayyana man cewa kamar lardi Larabci ce da nufin ƙasa. Gunduma kuwa Hausa ce da ke nufin yanki na wata ƙasa. A faɗarsa da lardin Sakkwato da gundumar Sakkwato duk abu ɗaya ne, wato yana nufin yankin Sakkwato.

[2] Duba CNHN (2016) Ƙamusun Hausa Na Jami;ar Bayero Shafi na 135

[3] Na yi hira da wannan mafarauci a rumfar mafarauta cikin kasuwar Gummi ranar Jumu’a 06/04/2018.

[4] A hirar da na yi da shi, Muhammadu Lema ya tabbatar da cewa akasari ɗaurin daji tun gida ake yinsa amma ɗaiɗaikun mafarauta kan yi nasu ɗaurin daji ko baya ga wanda maidaji yake yi.

Post a Comment

0 Comments