Ticker

6/recent/ticker-posts

Wakar Yusuf Musa Illela Ta Alhaji Musa Danba’u Gidan Buwai

Sauraro Da Rubutawa

Hirabri Shehu Sakkwato

08143533314


Amshi: Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,


Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.


Jagora:  Wanda Allah ya ba,

A bi shi shi ad daidai,

Wad’anda ba su buk’atakka,

Ga su nan sun muzanta,

Yara:    Tunda ba su da komai,

K’asa kuma ba su da kowa.

 

Amshi: Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

https://www.amsoshi.com/2017/06/30/audu-stem-difiti-gwamna-dan-baraden-wamakko/

Jagora: Baba d’an Audu,

Na Audu mai gidan Haji ‘Danba’u,

Na Alhaji Mani mai yi ma yak’i tahiyayya,

Yara:   Mai buga ga mak’oshi,

Dambe da kai ba ya da dad’i.

 

Amshi: Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

 

Jagora:  Adamu Bakane,

Ka yi dangali bana ka huta,

Adamu Bakane,

Mai gida baban Shehu da Inuwa,

Yi zamaninka ka huta,

K’attan banzan ga masu kuri Illela,

Yara:    K’yale su da yara suka ruga musu kashi.

 

Amshi: Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

 

Jagora:  Duk bak’o ya shigo a birnin Illela,

Sai ka ji ya ce,

Garin ga maye ni ka shakku,

Bak’in angulu,

Ka yi hurhura ka gama aski,

Yara:    Kai ka shafa mana lahiya,

A bar ce muna mayu.

 

Amshi: Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

 

Jagora:  Ar! Ga wani ya yi takarab bayis,

Ta ruhe da shi ya hwasa kuka,

Yanzu swata yaka nema,

Bak’in dutse kakai ka iske,

Yara:    Tun da d’an asali ba ya kasuwanci da k’azami.

Amshi:  Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

Jagora:   Buhun lalle yay kama buhu bai yi buhu ba,

Shi buhun lalle ya yi kama buhu ba ya da nauyi,

Da ina tsoron wane yanzu na bar tsoronshi,

Yara:     Tunda bakin garkassu munka watce masa kaya.

 

Amshi:   Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

 

Jagora:   Shi buhun lalle ya yi kamar buhu ba ya da nauyi,

Shi buhun lalle yai kamar buhu bai yi buhu ba,

Da ina tsoron wane yanzu na bar tsoranshi,

Yara:     Wanga lokaci ba ka da k’arhi.

 

Amshi:   Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

 

Jagora:    Bambad’awan lokal,

Su wane sank’ira,

Kada ka hwad’a ‘Danba’u,

Yara:      Wanga lokaci ba ka da k’arhi.

 

Jagora:     Da kai nike kai wane,

Rak’umi d’an atalolo bana ina za ka da kaya?

Yara:       Za ya je ‘bantalagindi,

Inda mata suke banza.

 

Amshi:    Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

https://www.amsoshi.com/2017/06/30/cali-cajinge-siyasa-ta-dawo/

Jagora:     Godiya Haji Hadi,

Yara:       Tunda hairan yaka yo man.

 

Jagora:     Godiya Haji Hadi,

Yara:       Saboda hairan yaka yo man.

 

Amshi:     Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

 

Jagora:      Mijin Hajiya Maryama Sadauki,

Yara:         Dattijo baba Allad dad’a girma. ×2

 

Jagora:     Mijin Asma’u,

Yara:        Dattijo Allad dad’a girma ×3

 

Jagora:     Mijin su Umaima,

Yara:       Dattijo Allad dad’a girma×2

 

Amshi:    Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

 

Jagora:    Sanusi d’an Wali,

Yara:       Yadda yay yi min,

Ban iya ramma.

 

Jagora:    Sanusi na gode,

Yara:       Yadda yay yi mini,

Ban iya rammai,

 

Jagora:    Sanusi d’an Wali,

Yara:       Yadda yay yi man,

Ban iya rammai.

 

Jagora:     Sarkin dawaki na gode,

Yara:        Yanda yay yi man,

Ban iya rammai.

 

Jagora:      Modi bakanike Modi,

Yara:         Yanda yay yi man

Ban iya rammai,

 

Jagora:       Bakanike Modi,

Yara:         Yanda yai yiman,

Ban iya rammai.

 

Jagora:       Godiya sarkin Shanu,

Wanda yai mani,

Yara:         Yanda yay yi man,

Ban iya rammai.

 

Jagora:      Godiya ga sarkin noma,

Yara:        Tunda ya kyauta.

 

Jagora:     Ina Sanusi d’an Wali?

Ubangidan ‘Danba’u abin ka yi mani,

Yara:        Yanda yay yi min,

Ban iya rammai.

 

Jagora:     Gaishe ka sarkin darabto,

Yara:        Yanda yay yi min,

Ban iya rammai.

 

Jagora:      Sarkin alaru na gode,

Yara:         Yanda yay yi min,

Ban iya rammai.

Jagora:      Magaji Darma ka kyauta,

Yara:        Yanda yay yi min,

Ban iya rammai.

 

Amshi:    Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

 

Jagora:     Godiya wajen Mustapha,

Ina alkali Alhaji ya gode,

Yanda yai man,

Ban iya rammai.

Jagora:     Haji Mamman mai mota baba na gode,

Yara:        Yanda yay yi min,

Ban iya rammai.

 

Amshi:     Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

 

Jagora:  Koma ganin bushiya a birnin Illela,

K’ila ko ta tahiyat ta?

Tana nan Illela,

Yara:    Don ku jiya mun ganat,

Ga ‘yan yara ga hannu.

 

Amshi:  Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

 

Jagora:   Baba Salihu ya yi d’a,

Alhaji na gode,

Yanda yai man,

Ban iya rammai.

 

Amshi:   Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.

 

Jagora:   Wanda Allah ya ba,

A bi shi shi ad daidai,

Wad’anda ba su buk’atakka,

Ga su nan sun muzanta,

Yara:      Tunda ba su da komai,

K’asa kuma ba su da kowa.

 

Jagora:    Rik’a bari wargi,

Karo da kai ba ya da dad’i,

Isuhu Musa ciyaman,

Kai ne suka sauna.
www.amsoshi.com 

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.