Sauraro Da Rubutawa
Hirabri Shehu Sakkwato
08143533314
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Allah ya cika manufakka,
Baba jahar Sakkwato,
Yara: Birni mu da k’auye,
Na ji kowa addu’a yakai.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Ga dai mulki gare shi,
Ga nera ta tsaya,
Ga jama’a nan gare shi×3
Ga ilimi yay yawa,
Ga Turanci.
Yara: Ko Amerikan gogawa sukai.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Yanzu ga Turanci,
Yara: Ko Amerikan gogawa sukai.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Na Walin Katsina,
Baba sahibin Sule Zurmi, ×2
Yara: Duk mai haye ma Hauka yakai.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Ka k’ara shiri Tahiru,
Ka ja d’amara ya hi kyau,
Mutum shakka tai nikai,
Ka k’ara shiri Tahiru,
Mutum ba ka ta tashi,
Yara: Sai yanai ma banda k’asa.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Mijin Alhajiya Amina,
Angon Murja,
Uban Sagiru da Babangida ×2
Yara: Shelto mai ganin k’uda ko da sun yawa.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Bafarawa Attahiru,
Yau duk harka Sakkwato,
Idan ba ka cin ta,
Mun ga ba harka ce ba×3
Yara: Duk kurun kuza ce sukai.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Bafarawa Attahiru,
Sana’a da yawa take,
Wani bi dai ni wak’a nikai,
Wani bi ku har wundaye inai,
Cikin bayin nan naku,
Ka ban jan Buzu guda.
Yara: Ya zan gyara min kaba.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Sakwkatawa ni ji suna fad’in,
Wane dai ba ya da hankali,
Wane shi dai ba d’a ba ne,
Zamanin can da ya wuce,
Bafarawa kai ne ya bid’a×2
Kuma kai ne ka taimaka,
Kuma kai ne kay mai tsaye,
Buk’atassa da ta biya,
Da can k’arshe,
Yara: Sakamakon sheri yai maka.
https://www.amsoshi.com/2017/06/30/dan-abai-hadarin-%c6%99asa-mai-maganin-sanin-kabido/
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Ni ma idan ka ganan Sakkwato,
Idan ba ni gidan Ila,
Yara: Bahwarawa ne yay kira.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Idan ka ga nan Sakkwato,
Idan ba ni gidan Ila,
Yara: Bahwarawa ne yai kira.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Yanzu idan ba ni gidan Ila,
Yara: Bahwarawa ne yay kira.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Allah ya cika manuhwakka,
Baba jaha Sakkwato,
Yara: Birninmu da k’auye,
Na ji kowa addu’a yake.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Ga d’ammanin haji ‘Danba’u,
Idan an je a wurin buki,
Idan masu kud’i sun had’u,
To da sun je kyauta sukai,
Yara: Wani mai kud’d’i ya barkace,
Rabon guraye ya kai.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Bafarawa Attahiru,
Ga mota za ya ban,
Yara: Katan kiki ya hana.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Na walin Katsina,
Baba sahibin Sule Zurmi,
Yara: Duk mai haye ma hauka ya kai.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Ni ma ina shakka duniya,
Ina tsoron duniyag ga,
Ka ja d’amara Tahiru,
Mutum ba ka ta tashi,
Yara: Sai yanai ma banda k’asa.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Abu dogo Alhaji,
Yara: Haira yay muna.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Mai siminti haji Bubakar,
Abu dogo ni tuna,
Yara: Zaman hairan yay muna.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Mai siminti haji Bubakar,
Abu dogo ni tuna,
Yara: Raben hairan yai muna.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Haji Sheu Ubandoma Shehu,
Yara: Zaman hairan yai mana ×2
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: D’anmaliki Bello na Acida,
Yara: Zaman hairan yai mana.
Amshi: Kar ka ji tsoron maza,
Rik’a zakin duniya,
Bai san tsoro ba,
Bafarawa Attahiru.
Jagora: Na gode magajin,
Baba Garba garin Kujeyu,
Yara: Zaman hairan yai mana.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.