𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. Barka da warhaka ya iyalin da sanyi ya kokari? Allah ya kara basira da ɗaukaka. Pls Dan Allah tambaya nake da ita. Dan Allah me Muslinci ya tanada game da rabon kwana akan mata fiye da ɗaya.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumusalam
warahmatallahi wabarakatuh.
Toh yar'uwa da farko dai
wanda yake da mata sama da ɗaya musulunci ya yi masa
umarni da dole ya yi adalci a tsakaninsu. Daga cikin abin da ya wajaba ya yi
adalci a cikinsa kuwa har da rabon kwana, wato ya baiwa kowace mace yini da
dare, kuma ya zauna da ita a wannan daren.
Imamus Sha’fa’i (RA) ya ce:
“Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da mahangar mafi yawan
rinjayen malaman Musulunci sun nuna cewa dole ne mutum ya raba yini da dare
tsakanin matansa [ya ba kowa dare da rana], da kuma cewa ya yi adalci wajen yin
haka. (al-Ummu, 5/158). Sai ya ce: Ban san wani saɓanin
(malamai) ba akan wannan. (al-Ummu, 5/280).
Imam Al-Baghawi (رحمه الله)
yana cewa: Idan mutum yana da mata sama da ɗaya,
to ya daidaita su, idan sun kasance 'yantattu [wato ba bayi ba], musulmai ne ko
kuma daga cikin Ahlul kitabi [watau Bayahudiya ko Kirista]. Idan kuma bai yi
masu adalci ba, to ya saɓa wa Allah, kuma dole ne ya
mayar da kwanan ga wacce ya zalunta.
An karɓo
daga Abu Hurairata Allah Ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi
Wasallam) ya ce: “Duk wanda yake da mata biyu, ya kuma karkata zuwa ga ɗaya
daga cikinsu (a kan ɗaya), zai zo ranar ƙiyama rabin jikinsa ya jingine (ya
shanye)”. (Abu Dawud ne ya rawaito shi, 2/242; al-Tirmizi, 3/447; al-Nasaa’i,
7/64; Ibn Maajah, 1/633; al-Haafiz ya inganta shi a cikin Buloogh al-Maraam,
3). 310, da al-Albaani a cikin Irwaa' al-Ghaleel, 7/80).
Abin da ake nufi da wannan shi
ne ya fifita wata ta fuskar ayyukansa; wannan kam ba za a kama mutum ga wani
aiki da karkata zuciyarsa da shi ba idan har ya yi daidai ga matansa a aikace. Allah
(تعالى)
yana cewa:
وَلَنْ تَسْتَطِيْعُوْۤا اَنْ تَعْدِلُوْا بَيْنَ النِّسَاۤءِ وَلَوْ حَرَصْتُمْ فَلَا تَمِيْلُوْا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوْهَا كَالْمُعَلَّقَةِۗوَاِنْ تُصْلِحُوْا وَتَتَّقُوْا فَاِنَّ اللّٰهَ كَانَ غَفُوْرًا رَّحِيْمًا
Kuma ba za ku iya yin adalci
ba a tsakanin mata ko da kun yi kwaɗayin
yi. Saboda haka kada ku karkata ga ɗaya
daga cikinsu, har ku bar ta kamar wadda aka rataye... [Suratul Nisa’i 4:129]
Abin da wannan ke nufi shi
ne, ba za ka taɓa iya yi musu daidai a cikin
zuciyarka ba, don haka kada ka karkata zuwa ga ɗaya
daga cikinsu, watau kar ka sanya ayyukanka su bi son zuciya da sha’awarka. (Sharh
al-Sunnah, 9/150-151).
Ibn Hazam (Allah Ya jiƙansa) ya ce: “Yiwa ma’aurata daidai wa
daida wajibi ne, mafi yawan kowa ya raba dare a tsakaninsu. (Al-Muhalla, 9/175)
Shaikhul Islam Ibn Taimiyyah
(rahimahullah) yana cewa: Wajibi ne ya yi wa matansa adalci bisa ijma'in
musulmi. A cikin sunan ɗin nan guda huɗu an
karɓo
daga Abu Hurairata, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:“Duk wanda yake
da mata biyu. Don haka idan ya zauna da ɗayansu
a dare ɗaya,
ko biyu ko uku, to sai ya zauna da ɗayan
ɗin a
makamancin kwanakin da ya yi da ta farkon, kuma kada ya fifita ɗaya
daga cikinsu a cikin rabon lokacinsa.(Majmu’ul Fataawa, 32/269).
Saboda haka dai wajibi ne
wannan mijin ya ji tsoron Allah, ya kuma yi adalci a cikin rabon lokacinsa. Matar
sa ta gaya masa hukuncin shari’ah game da abin da yake aikatawa, da gargadi
akan zaluncin da ya ke yi. Ta tunatar da shi Allah da Lahira, don ya duba
kansa, ya yi adalci a cikin rabonsa. Kuma Allaah ne Mafi sani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.