https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

Sauraro Da Rubutawa


Hirabri Shehu Sakkwato


08143533314


 

Amshi: Ciyaman bugun ciyamomi.

Bala ba a jan ka d’an Musa.

 

Jagora: A jahar Sakwkato,

Nake magana,

Ciyamominmu na PDP,

Su goma sha biyar daidai,

Mai gaskiya Obasanjo,

Zance da kai yi yai daidai,

Ka gaya ma ciyamomi,

Su rik’e mai kid’ansu ‘Danba’u,

Na zare Ido ina dubi,

Yara:    Ni hay yanzu ban ga komai ba.

 

Jagora: Na zare ido ina dubi,

Yara:    Ni hay yanzu ban ga komai ba.

 

Jagora: Jama’a kun shige inwa,

Yara:    Mai wak’arku na cikin rana.

 

Jagora: Im jama’a kun shige cikin lemat,

Yara:    Mai wak’arku na cikin rana.

 

Amshi: Ciyaman bugun ciyamomi.

Bala ba a jan ka d’an Musa.

 

Jagora: Yau duk ‘yan uwanmu sun yi sharaf,

Yara:    Ni ko an k’i yin su garkata.

 

Jagora: An ce mani an yi rabon kud’i,

Manya da yara sun samu,

Amma an k’i ba su ‘Danba’u,

In dai na yi hank’urin rowa,

Yara:     Ka sani ba ni hank’urin k’arya.

https://www.amsoshi.com/2017/07/01/alu-sarkin-yamma-dan-barade-jikan-umaru/

 

Jagora:  In na yi hank’urin cizo,

Yara:     Ka sani ba ni hank’urin yaga.

 

Amshi:  Ciyaman bugun ciyamomi.

Bala ba a jan ka d’an Musa.

 

Jagora:  Wani ya sha karo da d’a Musa,

Ado na ji Bala ya kasai,

Can nig gane shi Dagawa ×2

Wawa ya d’au buhuhunan lalle,

Yara:     Ya ce za ya kasuwa Muza.

 

Amshi:  Ciyaman bugun ciyamomi.

Bala ba a jan ka d’an Musa.

 

Jagora:  Yale mai mota,

Ka kai d’a,

Na san ka fi zuciya sauri,

K’arhe bakwai da sassahe,

Daga Sakkwato birni ka tashi,

Ka je cikin garin Legas,

Ka dawo Kaduna ka sha mai,

Sai ka wuce Kanon Dabo,

Yale ka gangaro garin Yabo,

Yara:     Yadda na d’au agogo nid duba,

K’arhe goma sha biyu rana.

 

Amshi:  Ciyaman bugun ciyamomi.

Bala ba a jan ka d’an Musa.

 

Jagora:   Yale mai mota,

Ka kai d’a,

Na san ka fi zuciya sauri,

K’arfe bakwai da sassahe,

Daga Sakkwato birni ka tashi,

Sai ka wuce garin Legas,

Ka je Abuja ka huta,

Ka dawo Kaduna ka sha mai,

Ka gangaro Kanon Dabo,

Yale ga sunta’ba gari Yabo,

Yara:     Yadda ni d’au agogo na duba,

K’arhe goma sha biyun rana.

 

Jagora:   Wani ciyaman na duba,

K’azami ne ku mun san shi,

Taro munka je da shi Legas,

Kwana uku bai yi wanka ba,

Yara:     Yada ya mammatso ni sai nic ce,

Tahi da nan kana yi min wari.

https://www.amsoshi.com/2017/12/15/waiwaye-kan-tasirin-makadan-baka-cikin-alummar-hausawa/

Jagora:   K’azamin ciyaman mun san shi,

Taro mun ka je da shi Legas,

Kwana uku bai yi wanka ba,

Yara:     Yada ya mammatso ni sai nic ce,

Tahi da nan kana yi man wari.

 

Jagora:   Wawa!

Yara:      Tahi da nan kana yi man wari,

 

Amshi:   Ciyaman bugun ciyamomi.

Bala ba a jan ka d’an Musa.

 

Jagora:   Saga!

Yara:      Tahi da nan kana yi man wari.

 

Jagora:    Kansiloli daban-daban Audu,

Kasiloli daban-daban Ada,

Ga kowane yana ta k’iba,

D’an tsuntsun tsorolo tsomodo,

Yara:      Shi har yanzu bai yi gwa’bi ba.

Jagora:   Kansiloli daban-daban Ada,

Kowansu na ga na ta k’iba,

D’an tsuntsu tsorolo tsumodo,

Yara:     Shi hay yanzu bai yi gwa’bi ba.

 

Amshi:   Ciyaman bugun ciyamomi.

Bala ba a jan ka d’an Musa.

 

Jagora:   A na Rabi mijin Amina,

Yara:      K’ara shirin duniya ga shi ya hi.

 

Jagora:   Haji Sabo Madawaki na gode,

Ban rena da k’ok’arinai ba,

Haji Sabo Madawaki can Yabo,

Ban rena da k’ok’arinai ba.

 

Jagora:   Uban jam’iyyar nan sanata,

Ban rena k’ok’arinai ba.

 

Jagora:   A na gode mai Ali mai goro,

Yara:      Ban rena da k’ok’arinai ba.

 

Jagora:   A dole in gode Ali maigoro,

Yara:      Ban rena k’ok’ari nai ba.

 

Jagora:   A Baba injiniya a gaishe ka,

Yara:      Ban rena k’ok’ari nai ba.

 

Jagora:   A Bala d’an Audu Sifawa,

Yara:      Ban rena k’ok’ari nai ba.

 

Jagora:   Baba Bala d’an Audu Sifawa

Yara:      Ban rena k’ok’arinai ba.

 

Amshi:   Ciyaman bugun ciyamomi.

Bala ba a jan ka d’an Musa.

 

Jagora:   Na ji mutane suna ta gode ma,

Yara:      Sun ce ka yi k’ok’ari Yabo×2

 

Jagora:    Baba injiniya ubangari zaki,

Ban rena k’ok’arinai ba.

 

Jagora:    In dai na je garin Yabo,

Yaya zan barin garin Yabo,

Ni kam ban ga maigidana ba.

 

Jagora:    Yale mai mota na gode ma,

Yara:       Ban rena k’ok’arinai ba.

 

Jagora:    In Yale mai mota mutumina ne,

Yara:       Ban raina k’ok’arinai ba.

 

Jagora:    Sanata Aliyu d’an Garba,

Yara:       Ban rena k’ok’arinai ba.

 

Amshi:    Ciyaman bugun ciyamomi.

Bala ba a jan ka d’an Musa.

 

Jagora:    Kun ji uban jam’iyya,

Dattijo senata,

Aliyu d’an Garba,

Yara:       Ban rena k’ok’arinai ba.

 

Jagora:   A na gode wa Sabo na gode,

Yara:      Ban rena k’ok’ari nai ba.

 

Jagora:   A Madawakin Yabo ina Sabo?

Yara:      Ban rena k’ok’arinai ba.

 

Jagora:   A Sani D’anmaliki,

Yara:      Ban rena k’ok’arinai ba.

 

Jagora:    Sani D’anbaba na gode,

Yara:       Ban rena k’ok’ari nai ba.

 

Jagora:    A Sani D’anbaba mutumena ne,

Yara:       Ban rena k’ok’arinai ba.

 

Amshi:   Ciyaman bugun ciyamomi.

Bala ba a jan ka d’an Musa.

 

Yaro:     Amadu mai d’amaray yak’i,

Ware hannunka tunda ka yi kisa,

Wancan ne wanda ka kod’a,

Kwana nai biyat yana zawo,

Kuma ‘ya’yan Yabo sun ka fad’i.

Jagora/Yara:  Wai har yanzu bai yi wanka ba.

 

Yaro:    Amadu mai d’ammaray yak’i,

Ware hannunka tun da ka yi kisa,

Wance ne wanda ka kod’e,

Kwananai biyaf yana zawo,

Mutan Yabo sun ka shaida mini,

Yara:    Wai hay yanzu bai yi wanka ba.

 

Jagora:   Ciyaman bugun ciyamomi,

Bala ba a jan ka d’an Musa.

Yara:     Ciyaman bugun ciyamomi,

Bala ba a jan ka d’an Musa.

https://www.amsoshi.com/game-da-mu/