Ticker

6/recent/ticker-posts

Kirgau Na Zabarma Da Nau’o’insa (3)

Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya
NA
BASHIRU SHEHU 

BABI NA BIYU: Ma’anonin Tubalan Bincike


2.0 Shimfid’a


A cikin wannan babin an waiwayi tak’aitaccen tarihin al’ummar Zabarma. Yin hakan shi zai taimaka wa wannan nazarin wajen zak’ulo abubuwan da suka shafi zabarmawa musammam abin day a shafi nahawun harshensu. Ganin cewa tarihin kowace al’umma ba ya cika cif-cif ba tare da an ta’bo bayanin harshensu ba, shi ya sa wannan nazarin yake ganin dacewar duba yadda masana suka ba da bayani dangane da harshen zabarma ko zarma kamar yadda masanan suke kiran harshen zabarmawa da shi.

2.1Tarihin K’abilar Zarma ko Zabarmawa Da Harshensu


        Tarihi ya nuna cewa kabilun zarma sun kasance sun fito ne daga Nijar ‘bangaren tabkin debo a yankin kogin Nijar tsakanin Mupti da Gundani wanda suke a gabashin tsohuwar daular songhai wanda a yau take a cikin yankin k’asar Mali. Dangantaka mai matukar kusanci tsakanin zarma da wasu k’abilu guda biyu da suke a cikin daular Songhai ya sa kabilun biyu suke addini iri d’aya da al’adu hadda ma yanayin siyasar su kusan iri guda. Zarma da k’abilun daular Songhai suna daukar junansu a matsayin taubasai ne, wanda ya haifar da wasa da auratayya tsakaninsu. Bayan farmaki daban- daban da yankin Debo ta yi fama da shi wajen kabilun Taureg da Ful’be da Mossi da Soninke a k’arni  na goma sha biyar wanda  ya sanya kabilar zarma ta fice daga yankin  nata zuwa gawo har zuwa kudu masu gabashin k’asar Mali. Zarma sun  ci gaba da wannan hijira har zuwa yankin kudu na k’asar Nijar a cikin k’arni na goma sha shida. A yayin da suka yada zango  a Anzoru da Zarmaganda  wanda  suke arewacin garin Niyami. A k’arni na goma sha bakwai har zuwa  k’arni na goma sha takwas, wasu daga cikin k’abilar zarma sun ci gaba da tafiya daga Zarmaganda  zuwa  cikin  wani  k’afaffen tafki da yake a gabashin Niyami da cikin garin Fakara da kuma cikin duwatsun Zigui da yake kudu masu gabashin Zarmateri. A cikin kowane matakin hijira da  k’abilar Zarma suke yi, a duk inda suka yada zango sukan  iske ‘yan asalin wannan garin wanda k’abilar  Zarma kan bak’unta, daga baya sai su fatattake su, su gaje muhallinsu.  Ko kuma su  murk’ushe su, su mai da su bayi kuma su zauni wurin. Misali kamar k’abilar K’ilafar kalle gole da Sije wanda suke cikin yankin  Dollols dake cikin duwatsun Zarmatare. Wannan halin ne  su kuma  kabilar Zarma suka  fuskanci farmaki  a hannun Mawri da  Kurfeyawa daga  gabashinsu,  amma yanzu  haka Zarma ta hadiye su. Hare-hare  ya yi sauki har zuwa farkon karni na goma sha tara lokacin da Zarmatarey ta fuskanci

hare-hare daga  hannun Lissawan da Kel Nanl tuareg da Imanan daga arewacin da kuma Ful’be  wad’anda suka yi  hijira  zuwa  Dallol Bosso daga Say.Wannan matsala ta yi tsamari har ya sa sarkin Zarman Dosso Zarmakoy Attikou ya nemi taimakon sojojin faransa a1898 wanda da suka yada zango  a Karimama, Benin Faransawa sun  masa wannan gayyatar amma abin mamaki ga sarki Zarmakoy da mabiyansa shi ne  Faransawa sun mamaye kasar Zarma tsawan shekaru sittin na mulkin mallaka a cikin kasar Nijar.

2.2 Harshen Zabarma Da Dangoginsa


Harshen zarma yana d’aya daga cikin harsunan Daular Songai . Wannan harshen  yana  daga  cikin harshen da masu  amfani da shi suke zaune a kudancin k’asar Nijar. Al’umma da dama suna kiran harshen da sunaye kamar haka;  Dijarma ko Diyabarma, ko Zarma ko Zarmanci Wasu ma kan kira shi da Zerima. Zarma shi ne harshe na biyu da al’ummar kasar Nijar  suke amfani da shi. Wato bayan  harshen Hausa sai na Zarma. Harshe ne da ya fito daga harsuna ‘yan dangin Nilo-sahara. Harshen yana da mutane  kimanin miliyan biyu da dubu  dari hudu  ke magana  da shi wajen  sadarwa. Harshen zarma ya fi  kowane  harshe da ya fito  daga  daular Songai wajen yawan masu amfani da shi. Harshen zarma ana amfani da shi  a fad’in daular Songai. Harsuna biyu da suke  mak’wabtaka  da harshen zarma  wad’anda mutanen k’asar  Mali suke amfani da su masu makwabtaka  da  harshen zarma  su ne; Koira boro senni da koira chirii.  Koira  boro  senni mutanen da suke zaune a tsakiyar  birnin  da ake  kira gawo suke amfani da shi. Ana hasashen cewa kimanin mutane dubu d’ari hud’u suke magana da harshen wajen sadarwa. Harshen ya yi mak’wabtaka da harshen Zarma ta gabas da ga’bar kogin Naija. Shi kuwa harshen koira chirii masu amfani da shi suna zaune ne a tsohon birnin da ya yi fice wanda aka kafa jami’ar Tambuktu a cikinsa. Yana da masu amfani da shi  kimanin mutane dubu dari biyu 200,000. Bisa ga hasashen dam asana suka bayar, ba dukkan masu magana da harshen Zarma ke iya magana da harshen Koyraboro senni ba. Harshen Zarma shi ne fitaccen harshen da akasarin mutanen Nijar suke amfani das hi, baya ga harshen Hausa. Abin nufi a nan shi ne, harshen Hausa shi babban harshen da al’ummar k’asar Nijar suke magana da shi, harshen Zarma shi ne na biyu da ke biye da harshen Hausa.

 

 2.3 Nad’ewa


Zabarmawa mutane ne masu kishin kansu tare da harshensu na Zabarmanci, kusan duk inda suke ba sa kushe junansu ballantana harshensu. Harshen Zabarmanci shi ne na biyu a yawan jama’a a k’asar Nijar, amma su ke samar da mafi yawan k’uri’un za’be a lokacin siyasa. Duk lokacin da wani abu ya taso na rashin jituwa tsakanin wata k’abila da al’ummar Zabarmawa, a Nijar ne ko a Nijeriya za a ga kowane d’an k’abilar Zabarma yana nuna goyon bayansa ga jama’arsa. Sannan ba yadda za a yi Bazabarme yana neman wani abu a hannun wani Bazabarme a ce ya hana shi ya ba d’an wata k’abila. Wannan kishin nasu shi ya haifar da ci gaban da suke samu na harshensu da al’ummarsu.

Post a Comment

2 Comments

  1. Allah yakara yadawa yaranmu wato zabarmanci. Kalatonton.albora. Bere?

    ReplyDelete

Post your comment or ask a question.