NA
BASHIRU SHEHU
BABI NA UKU: K’irgau Na Zabarma Da Nau’o’insa
3.0 Shimfid’a
K’irgau wani d’an rakiya ne mai bayyana adadin suna a lokacin da yake taimakawa suna a yankin suna na jimla. Sanin irin rud’anin da masu karatu kan samu a lokacin nazarin yankin sunan da d’an rakiya k’irgau yake raka suna shi ya sa wannan nazarin ya k’udurci bin sawun nau’o’in k’irgau na Zabarmanci daki-daki don fito da yanayin rakiyar da yake yi wa suna.
A kaso na farko za a kawo kalmomin lissafi, daga nan sai a nuna yadda kalmomin k’irgau kadina su biyo bayansu. Za a nuna yadda ake samun k’irgau odina na Zabarma da yadda yake gudana a cikin yankin suna. Haka kuma za a kawo nau’o’i kamar su; k’irgau ma’auni da na tambayau da na tsigalau da na amsa-kama da kuma na bai-d’aya. Za nuna yanayin rakiyarsu a yankin suna.
3.1 K’irgau Na Lissafi
Harshen Zarma kamar kowane harshe na duniya, shi ma yana da hanyar yin amfani da kalmomi don gudanar da lissafi. Zarma kamar harshen Hausa, yana da tsarin lissafi daga d’aya zuwa goma kamar haka:
ZARMA HAUSA
Aho d’aya
Ihinka biyu
Ihinza uku
Itaki hud’u
Igu biyar
ZARMA HAUSA
Iddu shida
Iyye bakwai
Ahakku takwas
Yagga tara
Iwai goma
Wad’annan kalmomin su harshen Zarma ke amfani das u wajen lissafi daga d’aya zuwa goma. Harshen Zarma kamar na Hausa harshen yana da tsarin bayyana k’arin da aka samu bayan kalmar lissafi ta goma. A Hausa ana amfani da kalmar k’awatau ta ‘sha’. Amma a harshen Zarma kuwa ana amfani da ga’bar k’arshe ta kalmar adadin goma ne wajen bayyana k’arin da aka samu a kan goma wato’wai’ sannan a sake k’ara kalmar ‘kindi’ sannan kuma a yanke ga’bar farko ta adadin lissafi na d’aya zuwa biyar.Sauran ana kawo a cikakkun kalmomi. Ga yadda abin yake:
ZABARMA HAUSA
Wai kindi hoo goma sha d’aya
Wai kindi hinka goma sha biyu
Wai kindi hinza goma sha uku
Wai kindi taaki goma sha hud’u
Wai kindi guu goma sha biyar
Wai kindi iddu goma sha shida
Wai kindi iyye goma sha bakwai
Wai kindi ahakkuu goma sha takwas
Wai kindi yaggaa goma sha tara
A nan za a kawo kalmomin lissafi da suka fara daga ashirin zu ashirin da tara. Harshen Zarma ya yi tarayya da na Hausa wajen amfani da kalmomin k’idayar da ake son yi wa k’ari. Idan goma ce za a fara da ambaton kalmar goma sannan a fad’i k’arin da aka yi mata haka abin yake a ashirin ko talatin ko arba’in, kusan duk gomiya haka ake bin su. Misali:
ZABARMA HAUSA
Waranka ashirin
Waranka kindi hoo ashirin da d’aya
Waranka kindi hinka ashirin da biyu
Waranka kindi hinza ashirin da uku
Waranka kindi taakii ashirin da hud’u
Waranka kindi guu ashirin da biyar
ZABARMA HAUSA
Waranka kindi idduu ashirin da shida
Waranka kindi iyyee ashirin da bakwai
Waranka kindi ahakkuu ashirin da takwas
Waranka kindi oyaggaa ashirin da tara
Haka abin yake a dukkan lissafin da za a yi wa k’ari daga gomiya. Ta ‘bangare lissafi day a kai d’ari harshen Zarma kan kira kalmar d’arid a Zangu don haka kamar yadda ake bayyana adadin yawa d’aruruwan da ake magana a kan ta hanyar amfani da kalmomin adadi na d’aya zuwa tara haka abin yake a harshen Zarma. Misali:
ZABARMA HAUSA
Zangu d’ari
Zangu hinka d’ari biyu
Zangu hinza d’ari uku
Zangu taki d’ari hud’u
Zangu gu d’ari biyar
Zangu iddu d’ari shida
Zangu iyye d’ari bakwai
Zangu ahakku d’ari takwas
Zangu yaggu d’ari tara
Kalmar da ake amfani da ita wajen lissafin da adadin sa ya kai dubu kuwa a harshen Zarma ita ce ‘zambar’. Ana amfani da tsari k’idaya tun daga d’aya zuwa tara wajen ambaton adadin yawan dubunnan da ake son fad’i. Misali:
ZABARMA HAUSA
Zambar hinka dubu biyu
Zambar hinza dubu uku
Zambar taki dubu hud’u
Zambar gu dubu biyar
Zambar iddu dubu shida
Zambar iyyee dubu bakwai
Zambar ahakku dubu tawas
Zambar yaggu dubu tara
A wannan lissafin duk adadin da ake son k’arawa a saman dubu tun daga d’aya zuwa d’ari tara da casa’in da tara dole ne sai an yi amfani da d’afin ‘nda’.
3.2 K’irgau Odina (Ordinal System)
Harshen Zabarma ba kamar harshen Hausa ba ne ta fuskar nuna yanayi matakin kimar suna a lokacin amfani da k’irgau odina. Kalmomin k’irgau odina na zuwa ne kamar haka:
ZABARMA HAUSA
Sangina/shintine na/ta farko
Ihinkante na/ta biyu
Ihinzante na/ta uku
Itakante na/ta hud’u
Iggunte na/ta biyar
Iddunte na/ta shida
Iyyante na/ta bakwai
Ahakkunte na/ta takwas
Yaggunte na/ta tara
Iwante na/ta goma
3.3 K’irgau Kadina (Cardinal Quantifier)
K’irgau kadina shi ne lambobin adadin lissafi ne da sukan biyo bayan suna a yankin suna don su bayyana adadinsa a lokacin da suke raka shi don yankin suna ya fad’ad’a. A Hausa akwai kalmomi irin su ‘d’aya’ ‘biyu’ ‘tara’ ‘bakwai’ ‘goma’ ‘ishirin’ ‘talatin’ ‘d’ari’ ‘dubu’ da makantansu. A hashen Zabarma kuwa akwai kalmomin irin su; ‘yagga’ ‘iyye’ ‘ahakku’ ‘iddu’ ‘iwai’ ‘waranka’ ‘zangu’ ‘zambar’. Duk wad’nnan kalmomin na iya zuwa tare da suna a yankin suna na jimla don su raka shi, ta hanyar fayyace adadinsa. Misali:
ZABARMA HAUSA
kuiya/manekuiyi iddu riga/riguna shida
kwayiberi igu manyan riguna biyar
kway ikaina ihinka k’ananan riguna biyu
3.4 K’irgau Na Tambayau
Wannnan adadin na k’irgau na tambayau a harshen Hausa ana amfani da kalmar tambaya ta ’nawa?’ ne wajen
k’ok’arin fito da adadin sunan da yake raka wa. A harshen Zabarma kuwa ana amfani da kalmar ‘marge’ a matsayin Kalmar k’irgau tambayau wajen bayyana adadin suna a yankin suna na jimlar Zabarma. Misali
ZABARMA HAUSA
marge ‘ tifar yashi nawa?’
ko
marge-marge nawa-nawa tifar yashi?
3.5 K’irgau Na Ma’auni
K’irgau na ma’auni ana amfani da sunan abin da aka auna suna gagara k’irga ne wajen bayyana adadin suna a yankin suna na jumla. Misalin kalmomin da ake amfani da su na ma’auni su ne: ‘wuya’ ‘ mudu’ ‘tiya’ ‘buhu’. Ga yadda fasalin rakiyar take:
ZABARMA HAUSA
Sa’i mudu
Kwanabeeri tiya
Kwalba kwalba
Kwarfoo iggiya
Tifa tifa
Mangala mangala
Wad’annan su ne kad’an daga cikin kalmomin k’irgau ma’auni da ake amfani da su a harshen Zabarma. Ga misalign su a cikin yankin suna:
ZABARMA HAUSA
Haamoo kwanabeeri foo dawa tiya d’aya
Hainii sai iyyee gero mudu d’aya
Manja kwalba iddu manja kwalba uku
‘Dansi mangala itaki gyada mangala biyu
Tasi tifa igu yashi tifa hud’u
Fili kwarfoo zangu fegi/ fili kafa dari
3.6 K’IRGAU NA BAI-’DAYA
A adadin k’irgau na bai-d’aya a harshen Hausa akwai kalmomi irin su; ‘duk’ dukka’ ‘yawa’ ‘ da dama’ ‘da yawa’ ‘kad’an’ ‘kad’ai’ da ake amfani da su wajen bayyana adadin suna jam’i a yankin suna na jimlar Hausa. A Harshen Zabarma kuwa akwai kalmomin irin su:
misalin rakiyarsu a yankin suna ita ce:
ZABARMA HAUSA
Farkai iboobo jakai da yawa
Zankai ikulu ikwai dukkan yaran sun tafi.
Mudum agasassabai wanduna da dama
mudum aigabaa ibobo wanduna nake so da yawa
3.7 K’IRGAU NA MAIMAICI
Wannan nau’in yana d’auke ne da kalmomin adadin lissafi da ake maimaitawa, don samar da k’irgau na maimaici. Ana amfani da shi ne domin nuna adadin suna a yankin suna na jimlolin Hausa da na Zabarma. Misali kalmomin daga harsunan biu su ne:
ZABARMA HAUSA
Ihinka- hinka biyu-biyu ko bibbiyu
Ihinza-hinza uku-uku
Ahakku-hakku takwas-takwas
Itaki-taki hurhud’u ko hud’u-hud’u
Marge-marge? nawa-nawa?
Misalin su a yankin suna:
ZABARMA HAUSA
‘Damsi marge-marge? nawa-nawa gyad’a?
Wanna shi ne tsarin k’irgau na harshen Zabarma tare da misalan da aka kawo ta hanyar kwatanta shi da na harshen Hausa.
3.8 Nad’ewa
A wannan babin an tattauna kan nau’o’in k’irgau na Zabarma har guda bakwai. Da farko an kawo tsarin k’irgau na odina tare da misalan da aka bayar a yankin suna na sassauk’ar jimlar Zabarma, don bayyana yanayin yadda yake raka suna a cikinsa. Sai kuma aka jero kalmomin k’irgau kadina da yadda suke raka suna. A mataki na uku an kawo nau’in k’irgau tambayau tare da misalansa a yankin suna. An kawo nau’o’in k’irgau na ma’auni da na bai-d’aya da kuma na maimaici, tare da kwatanta su da na harshen Hausa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.