Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'ar Neman Zabin Allah (Istikhara)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Malam dan Allah a ba ni mafita akan wannan matsalan da ke damu na, ni ne soyayya ta shiga tsakanina da wata yar' gurin kanin babana wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya ma'ana kanwata kenan, Amma suna zargina akan aikin banza duk da hakan yakare a tunani ne kawai kuma har shi kanin baban nawa ya yi min maganar hakan, amma uwar yarinyar ba ta yimin maganar ba, amma alamunta ya nuna hakan. Sai dai babu Yanda za su yi ne kada a ce ba sa so, itama yarinyar da farko tafara bin irin ra'ayin iyayen amma ba ta fito fili ta bayyana min abin da take nufi ba sai dai tana yawan tambayoyina, kuma har wasu daga cikin kannenta sukan min wasu kallon da ke nuni da akwai magana, kuma mahaifiyata da babana suna son auren amma basu san can ana yimin irin wannan kallon zargin ba (zina) sai dai babu wata hujja da za su kawo (solid evidence) wanda zai tabbatar da hakan. Amma a yanzun yarinyar tana nuna tana so na sosai kuma babu matsala duk da hakan ina tsoron abin da zai iya biyo baya idan an yi auren ni kuma ba na son abin da zai ba ta mana zumunci, tabbas ni dai da za a fasa wannan auren danaji daɗi sai dai ban san yanda zan ɓullo ma wannan abun ba. Dan Allah a taimake ni da addu'a Istikhara na nemi zabin Allah domin koda kuwa ni ne za a ce mai laifi na yarda ni dai bana son auren da zai haddasa gaba a tsakkanin iyayenmu Na gode. Allah ya kara basira.

ADDU'AR NEMAN ZAƁIN ALLAH (ISTIKHARA)

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Godiya ta tabbata ga Allah, salati da aminci su tabbata bisa Shugaban halittar Allah, da iyalan gidansa da dukkan Salihan bayin Allah.

Na karanta dukkan bayaninka tun daga farko har Ƙarshe. Amma sai dai na lura kamar ka gina mafi yawan batutuwanka ne bisa zato. Misali: Kana zaton kamar iyayen yarinyar da Ƙannenta duk suna yi maka kallon mazinaci. Sannan yanzu kuma bayan ka riga ka samu soyayyarka ta zauna azuciyar yarinyar, sai kake zaton kamar wai za a samu matsala atsakanin Mahaifinka da ɗan'uwansa. Gashi kuwa Allah (Maɗaukakin Sarki) ya hana bayinsa muminai su rika gina al'amura akan zato. Allah ya ce:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اجْتَنِبُوا كَثِيرًا مِّنَ الظَّنِّ إِنَّ بَعْضَ الظَّنِّ إِثْمٌ ۖ وَلَا تَجَسَّسُوا وَلَا يَغْتَب بَّعْضُكُم بَعْضًا ۚ أَيُحِبُّ أَحَدُكُمْ أَن يَأْكُلَ لَحْمَ أَخِيهِ مَيْتًا فَكَرِهْتُمُوهُ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۚ إِنَّ اللَّهَ تَوَّابٌ رَّحِيمٌ

Ya kũ waɗanda suka yi ĩmani! Ku nĩsanci abu mai yawa na zato. Lalle sashen zato laifi ne. Kuma kada ku yi rahoto, kuma kada sashenku ya yi gulmar sashe. Shin, ɗayanku na son ya ci naman ɗan'uwansa yana matacce? To, kun ƙĩ shi (cin naman). Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai karɓar tũba ne, Mai jin ƙai (suratul Hujurat Aya ta 12)

Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce "KU RIKA YIWA MUMINAI ZATON ALKHAIRI".

Shawarar farko da zan baka ita ce: Ka karkade duk wani mummunan zato daga zuciyarka, ka dogara da Allah a cikin dukkan lamuranka. Ka sani cewa duk lokacin da Mutum zai Ƙulla wani muhimmin al'amari sai Shaiɗan ya zo gareshi ya sanya masa waswasi da mummunan tunani domin ganin ya lalata masa al'amarinsa.

Bayyanar da Ƙiyayya ga auren nan daga gareka zai iya janyo maka matsaloli sosai. Musamman ma fushin mahaifanka, da zubewar mutuncinka a cikin danginku, sannan koda nan gaba idan ka tashi yin aure, za su iya bayyanar da Ƙiyayyarsu ko suce babu ruwansu a cikin sha'aninka.

Ka mika wa Allah dukkan al'amarinka, ka dogara gareshi. Ka roki Allah ya zaɓa maka abin da zaifi zama alkhairi gareka arayuwar duniya da lahira. In sha Allahu za ka samu nutsuwar jiki da ta ruhi. Sannan ka samu lokaci mai muhimmanci kamar sulusin dare na ƙarshe (kamar daga karfe uku na dare har zuwa alfijir) ka yi sallah raka'a biyu, ka zauna ka yi wa Annabi salati sannan ka karanta addu'ar nan ta istikhara wacce take cikin Sahihu Muslim, akwaita ma a cikin Hisnul Muslim.

Jabir ɗan Abdullah ya ruwaito cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya kasance yana koyar da mu istihara akan dukkan al'amura kamar yadda yake koya mamu Surah a Alƙur'ani, kamar yadda Imamul Bukhariy ya ruwaito a hadisi mai lamba ta 6382.

Sallar istikhara sallah ce da ake yin raka'o'i guda biyu kamar yadda ake yin sauran sallolin nafila, abin da ke bambanta su shi ne niyya. Ana yin sallar istihara ce don barin ma Allah zaɓi a kan wata buƙata da mutum ke da ita. Sannan kuma Sallar istikhara sunnah ce ba farilla ba. Bayan mutum ya kammala sallar, sai ya karanta wannan addu'ar:

اللّٰهُمَّ إِنِّيْ أَسْتَخِيْرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ العَظِيْمِ فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلاَ أَقْدِرُ، وَتَعْلَمُ وَلاَ أَعْلَمُ، وَأَنْتَ عَلاَّمُ الغُيُوْبِ اللّٰهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأمْرَ (وَيُسَمِّيْ حَاجَتَهُ) خَيْرٌ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاقْدُرْهُ لِيْ وَيَسِّرْهُ لِيْ ثُمَّ بَارِكْ لِيْ فِيْهِ وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَ شَرٌّ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِيْ فَاصْرِفْهُ عَنِّيْ وَاصْرِفْنِيْ عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ، ثُمَّ أَرْضِنِيْ بِهِ

Ya Allah ina neman zaɓinka domin ilminka, kuma ina neman ka ba ni iko domin ikon ka, kuma ina rokonka daga falalarka mai girma, domin kai ne mai iko, ni kuwa ba ni da iko, kuma Kaine masani, ni kuwa ban Sani ba, kuma Kaine masanin abubuwan fake, Ya Allah! Idan kasan cewa wannan al'amari (sai ya ambaci buƙatar tasa) alheri ne gareni a cikin addinina, da rayuwa ta, da kuma ƙarshen al'amarina, - a wata ruwayar da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa - ka ƙaddara mini shi, kuma ka saukake mini shi, sannan ka albarkaceni a cikin sa, kuma idan kasan wannan al'amari sharrine a gare ni a cikin addinina, da rayuwata da ƙarshen al'amarina - a wata ruwaya; da magaugaucin al'amarina da majinkircinsa - Ka kawar da shi daga gare ni, kuma ka kawar DA NI daga gare shi, kuma ka kaddara mini alherin a duk inda yake, kuma ka sanya ni in yar da shi.

Ana karanta addu'ar ce bayan an idar da sallar an yi sallama, sai mutum ya ɗaga hannuwansa sama, ya yi yabo da jinjina ga Ubangiji, sannan ya yi salati ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam. Daga nan kuma sai ya yi ita waccan addu'ar ta istikhara.

Kuma ya halasta ga wanda ba ya iya yin ta da Larabci ya furta ma'anoninta da Hausa, ko kuma da duk harshen da yake iyawa, amma a yi addu'a da Larabci shi ne ya fi kamar yadda malaman Fiƙhu suka bayyanar.

Duk lokacin da kaji wani mummunan tunani ya zo maka game da lamarin nan, yi sauri ka yi addu'a ka nemi tsarin Allah daga sharrin shaiɗan.

Duk wanda ya nemi zaɓin Mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma ya yi azama a cikin lamarinsa, to bazai yi nadama ba. In sha Allah. Domin Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: "Kuma ka shawarce su cikin lamarinka, idan kuma ka ƙuduri aniya, to ka dogara ga Allah.

Daga ƙarshe ina yi maka fatan dukkan alkhairi, da fatan Allah ya sanya maka alkhairi a cikin aurenka da dukkan lamuranka. Ameen.

WALLAHU A'ALAM.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments