Ticker

6/recent/ticker-posts

Kirgau Na Zabarma Da Nau’o’insa (2)

NA

BASHIRU SHEHU 

KUNDIN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO SASHEN NAZARIN HARSUNAN NAJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO

Babi na ‘Daya: Gabatarwa

Gabatarwa


Nazari fage ne da masana da manazarta kan yi k’ok’arin binciko wani abu mahimmi game da wasu al’amura da suka shafi rayuwar al’umma. Abubuwan da akan nazarto suna da tarin yawa. A wannan nazarin za a yi k’ok’arin nazarto abin da ya shafi harshe ne, harshen da za a nazarto kuwa shi ne na Zabarma. Nazarin harshe yana da manyan ‘bangarori guda biyar, wad’anda suka had’a da: Nazarin k’wayoyin sauti da na tsarin sautuka da na ginin kalma da na ginin jimla da kuma na ilimin ma’ana. A nan za a dubi tsarin ilimin ginin jimla ne, a cikin sa ma za a mai da hankali ne kan yankin suna na jimlar Zabarma. A yankin sunan kuma za a waiwayi d’an rakiyar da ake kira da suna k’irgau ne ta yadda za dubi tsarin rakiyarsa da kuma nau’o’insa a harshen Zabarma.  Don samun sauk’ain aikin an kasa babukan zuwa gida hud’u kamar haka:

A cikin babi na d’aya an waiwayi aikin da masana da manazarta suka aiwatar, wad’anda suke da nasaba da wannan aikin domin tabbatar da cewa ba a maimaita aikin da wani ya rigaya ya aiwatar ba. Daga nan sai aka sami dalilan da suka haifar da yiwuwar wannan binciken.        Ganin an sami dalilin gudanuwar binciken sai aka bayyana farfajiyar da aka ke’bewa binciken. An kawo irin mahimmancin binciken ga rayuwar al’ummar Zabarma, musamman ma’abota nazari. Nad’ewa ita ta zama marfin wannan babin.

Babi na biyu kuwa yana d’auke ne da tarihin k’abilar Zabarma ko Zabarmawa da harshensu. Sannan aka dubi harshen da kuma dangoginsa, wato wad’anda ya yi makwabtaka da su da kuma wad’anda suke ‘yan gida d’aya. Sai aka nad’e babin.

A babi na uku an gabatar da shimfid’ar binciken sannan aka dubi nau’in k’irgau na lissafi a kason farko. A kaso na biyu aka waiwayi tsarin k’irgau odina. Bayan k’irgau odina sai aka kawo nau’in k’irgau kadina. An nazarto nau’in k’irgau na tambayau tare da na ma’auni, inda nau’in k’irgau na bai-d’aya ya biyo bayansu. K’irgau na maimaici shi ya zo daga k’arshe sai aka nad’e babin. Ga yadda aka aiwatar da nazarin:

1.1Bitar Ayyukan da Suka Gabata


Waiwaye a fagen bincike don gudanar da nazari da nufin aiwatar da bita kan ayyukan da masana da manazarta suka gudanar, yana da mahimmanci don kaucewa maimaita aikin da wasu suka rigaya suka aiwatar. Sanin haka shi ya sa wannan aikin ya k’uduri niyyar gudanar da bitar ire-iren wad’annan ayyuka ta hanyoyi uku.

  • Ta hanyar duba kudayen da aka buga a fagen ilimi a manyan makarantu (Jami’o’i).

  • Hanya ta biyu ita ce ta duba litattafan da aka buga, musamman wad’anda aka yi magana kan k’irgau cikin harshen zabarma.

  • Aikin ya dubi ire-iren muk’alu da k’asidu da mujallu da aka aiwatar a matakai daban–daban.


Binciken ya fara ne da kundayen da aka samu. Sannan aka gudanar da bitar su, wad’anda suke da nasaba da wannan nazarin. Nasabar ko dai ta kusa wato wadda ta shafi harshen zabarma ko wadda ta shafi al’ummar zabarma ko kuma ta nesa wato wadda ta shafi mak’wabtan zabarma kamar Hausawa da harshen Hausa.

1.1.1 Bitar Litattafai


Daga cikin ayyukan da aka yi waiwaye a kansu, akwai aiki irin na;  Arnotte (1970). Wannan marubunci ya yi bayani ne a kan ilimin Nahawu (grammar) da ya shafi ilmin ginin jimla (syntax) da ilmin tsarin sauti (phonology), da sauran abubuwan da suka shafi wannan fannin. Amma wannan aikin nashi ya yi shi ne a cikin rubutu na harshen Fulatanci da na harshen Igilishi. Wannan marubucin ya yi bayanin ginin jimla (syntax) ne a babi na biyu, inda sauran babukan ya nazarci sauran ‘bangarorin nahawun Fulatanci da Ingilishi. Wannan aiki yana da alak’a da wannan binciken. To amma sai dai wannan binciken yana magana ne a kan kwatanci na kamanci ko bambanci na azuzuwan kalmomin harshen Hausa da na Fulatanci, haka kuma an yi amfani da su don kwatanta su cikin sassauk’ar jimlar Hausa da ta Fulatanci. Wato yadda azuzuwan kalmomi na harshen Hausa da na Fulatanci su ke zuwa a cikin jimla.

Daga cikin ayyuka da aka samu don gudanar da bitarsu, akwai na Kraft da Kirk– Green (1973). Marubutan sun gudanar da aikin nasu kan abin da ya shafi harshen Hausa. Sun ta’bo magana kan nahawun harshen Hausa, inda suka gabatar da bayanin k’irgau a shafi na 57 kuma suka raba k’irgau zuwa nau’i bakwai. Sannan kowane nau’i sun bayyana yadda yake fito da adadin suna a yankin suna na jumla. Ga yadda abin ya kasance:

  • Nau’in farko: Sun bayyana cewa, k’irgau wani sashin suna ne, wanda yake d’auke da lambobi tare da wasu kalmomi. Wato k’irgau yana biyo bayan suna kai - tsaye ba tare da wani d’afi na ‘n’ ko ‘r’ ba. Marubutan sun bayyana cewa, idan k’irgau ya biyo bayan suna ba a kowane lokaci ake buk’atar suna jam’i ba. Misali:


(1)

(i) ‘Dgida goma.d’YSn

 

Sn      K’gkadina

(ii) ‘DYara nawa?d’YSn

 

Sn   K’gtambayau

(iii) ‘DYarinya biyu.d’YSn

 

Sn        K’gkadina

  • K’irgau Kadina: A wannan nau’in sun yi bayani ne kan k’irgau kadina, wato lambobin lissafi, inda suka kawo misali kamar haka: ‘d’aya’ ‘biyu’ ‘uku’ ‘hud’u’ ‘bakwai’ ‘tara’ ‘goma’ ‘d’ari’ ‘dubu’ da sauransu. Sun bayyana cewa kalmar ‘sha’ ana amfani da ita wajen k’ara wa k’irgau kadina adadi bayan kalmar ‘goma’. Misali:


 

  • (a)‘goma sha d’aya’


(b)‘goma sha tara’

Sannan ana iya cire kalmar ‘goma’ kuma lissafin ya  ba da ma’ana. Misali: sha d’aya’, da ‘sha bakwai’, da ‘sha tara’.

Haka kuma ana k’ara kalmar ‘da’ inda adadin lissafin ya wuce ‘ashirin’ ko ‘talatin’ ko ‘casa’in’ da makamantansu. Misali: ‘talatin da biyu’, ‘arba’in da tara.’

  • K’irgau tambayau: A wannan nau’in sun yi bayani ne a kan kalmar tambaya ta k’irgau tambayau wato ‘nawa?’. Misali: mutum nawa?’ ‘Su nawa?’ ‘kud’i nawa?’

  • K’irgau na bai - d’aya: Sun nazarci kalmar ‘duka’ ko ‘duk’, inda suka ba da misalin kamar haka:


(3)

(i) yara duka                yara uku

(ii) Su duka                   su hud’u

  • K’irgau da ake yi wa d’afi : A nan sun ce duk sauran nau’o’in k’irgau ana iya yi masu d’afin ‘n’ ko ‘r’ tare da kalmar wakilin suna d’an mallaka, amma ban da kalmar k’irgau tambayau ta ‘nawa?’. Misali: ‘d’ayansu’, ‘biyunsu’, ko ‘biyar d’insu’, ‘dukan mutane’.

  • K’irgau odina: Sun yi bayani ne kan kalmomin  ‘na’ da ‘ta’,  wato kalmomin da ake amfani da su wajen samar da k’irgau odina. Misali:na/ta farko/fari’, ‘na/ta biyu’, ‘na/ta goma’, ‘na/ta nawa?’ ‘na/ta tsakiya’, ‘na/ta k’arshe’.

  • K’irgau ma’auni: A nau’i na bakwai sun yi bayanin ne kan kalmar ma’auni, ta ‘guda’,  inda suka ce ana had’a ta da kalmomin lissafi na k’irgau kadina kuma tana iya zaman kanta a maimakon kalmar k’irgau kadina na ‘d’aya’. Misali: yara ‘guda biyu’, ‘mota guda’.


Kraft da K’irk-Greene (1973) sun tak’aita bayani matuk’a ta yadda mai nazari zai iya samun matsala wurin fahimtar ko me ake nufi da k’irgau. Kuma da wuya mai nazari ya gano manufarsu dangane da nau’o’in k’irgau. Saboda rashin gamsasshen tsarin rabo.

Wani aikin da aka aiwatar kan k’irgau shi ne, na Galadanci (1976). Marubucin wannan littafin ya gudanar da aikinsa  a kan jumlar Hausa da sassanta. ‘Daya daga cikin sassan da ya gudanar da aiki a kansa shi ne yankin suna (YSn). A yankin suna, ya ta’bo magana kan ‘yanrakiyar suna wanda d’aya daga cikin su shi ne k’irgau. Galadanci (1976) ya gabatar da manyan rukunonin k’irgau guda uku.Wato rukuni na d’aya, da na biyu da na uku.  Bugu da k’ari ya nuna cewa kowane babban rukuni yana d’auke da ire – iren k’irgau a yankin suna (YSn). Ga yadda ya bayar da su:

A rukuni na d’aya Galadanci (1976) ya nuna cewa irin wannan k’irgau yana k’unshe da lambobin lissafi na k’irgau kadi b na. Tare da kalmomin k’irgau ma’aunin. Ga misali:

 

(4)  hula   guda    biyu.

Sn        K’gMn    K’gkadina

A wannan yankin suna (YSn), akwai suna “ hula” da kalmar  k’irgau ma’aunin “ guda” da k’irgau kadina “biyu”. Galadanci (1976)  ya nuna cewa ma’aunin k’idaya zuwansa ba dole ba ne, na za’bi ne. Wato ke nan, ana iya samunsa, kamar haka:

(5)             (i) hula   guda   biyu

Sn     K’gMn   K’gkadina

ko

(ii) hula    biyu.

Sn       K’gkadina

A rukuni na biyu Galadanci (1976) ya nuna cewa yana k’unshe da kalmomin k’irgau irin su, kad’an’  (kalma d’aya) ko sashen jumla irin su, ‘ da yawa’ da ‘da dama’ masu kalmomi biyu ko fiye. Ko ‘nawa?’ kalmar k’irgau tambayau. Ga misali:

(6)     kud’i  kad’an.

Sn       K’gbaid’aya

 

(7)

(i)      mutane da yawa.

Sn         K’gbaid’aya

(ii)     yaaraa nawa?

 

Sn    K’gtambayau

 

                                                (iii)    buhuna da dama.

Sn              K’gbaid’aya

A rukuni na uku Galadanci (1976) ya nuna cewa rukuni na uku ya k’unshi maimai na kalmomin k’irgau kadina. Misali: biyu-biyu, ko na kalmar k’irgau tambayau. Misali: ‘nawa – nawa?’ Wad’annan kalmomin su ke samar da rukuni na uku ta hanyar maimaita su sau biyu.  Misali  a cikin yankin suna;

(8)                     (a)      riguna  uku - uku

Sn               K’gmaimaici

(b) nawa – nawa gyad’a?

K’gmmc           Sn

Bisa la’akari da aikin Galadanci (1976) da ya gudanar na rabon manyan rukunonin k’irgau zuwa gida uku, da yadda ya gudanar da bayaninsu dangane da ire – iren kalmomin k’irgau da suke k’unshe a cikin kowane rukuni na k’irgau, wasu tambayoyi na iya biyo baya, don nuna irin yadda matsalolin da ke k’unshe a cikin aikin.

Skinner,  (1977) Marubucin ya yi bayani dangane da ma’anar suna a shafi na ar’ba’in da bakwai (sh47) ya kuma bayyana kashe-kashen suna a nahawun Hausa. Wannan bayani yana da alak’a da wannan aikin. Sai dai kuma shi wannan aikin yana magana ne a kan azuzuwan kalmomi na harsuna biyu, wato Hausa da Fulatanci (fulfulde).

Crystal,  (1980) Shi ma ya kawo ma’anar  suna da sifa wanda yake yana da dangantaka da wannan binciken, amma shi wannan bincike yana k’ok’arin kawo cikakkun azuzuwan kalmomin harsunan Hausa da na Fulatanci ne ta hanyar kwatanta su da juna domin fito da kamanci da bambanci a tsakanin su.

Junju, (1980), a cikin littafinsa ya yi bayyanin ma’anar sifa da suna,ya kuma kawo nau’o’insu, a harshen Hausa. Aikin na Junju yana da alak’a da binciken da aka gudanar a cikin wannan nazari sai dai shi Junjun ya tak’aita ne kan  harshen Hausa ne. Inda wannan nazarin ya gudanar da bincike kan azuzuwan kalmomin  harshen Hausa da na Fulatanci (fulfulde), da kuma nuna yadda suke  iya zuwa a cikin jimla.

Mc. Intosh (1984) wannan wata Baturiya ce marubuciya kan nahawun harshe, a cikin littafinta ta yi bayanai masu d’imbi yawa wad’anda suka danganci ilimin ginin jimla (syntax) da ilimin tsarin sauti (phonology) da sauran abubuwan da suka danganci nahawu (grammar). Marubuciyar ta yi bayani a kan nahawu a babi na biyu a cikin littafinta, bisa ga tsarin rubutun Ingilishi da kuma Fulatanci (fulfulde). Abin la’akari a nan shi ne, wannan aiki na Mary (1984), aiki ne da ya ke da alak’a da wannan binciken. To amma sai dai ita ta rubuta  littafin ne a kan harshen Ingilishi da nas harshen Fulatanci. Inda wannan aikin zai mai da hakali kan kamancin daidaito na azuzuwan kalmomi da sassauk’ar jimlar Hausa da ta Fulatanci, tare da fito da bambancin da ke tsakanin su.

George, (1985) a wani bincike da ya gudanar don k’ok’arinsa na fayyace gaskiyar al’amarin da ya shafi ma’anar harshe ya kawo ma’anar harshe ba tare da  fito da azuzuwan kalmomin harshen ba, kuma manazarci ya tak’aita ne kan ba da ma’anar harshe kad’ai.Sai dai ban sani ba ko ya yi magana kan ajin kalmomin harshe, wanda hannun wannan binciken bai kai gare shi ba.

Bagari (1986) ya nazarci k’irgau, inda ya dube shi, ta hanyar yanayin zuwan sa don ya raka suna, a yankin suna (NP) na jimla. Bagari (1986:120) ya kawo fasalin yadda k’irgau kan zo kafin kalmar suna a lokacin rakiya. Inda ya kawo irin wad’annan kalmomi da ya kira da siffofin adadi; ‘d’imbi’ da ‘tari’ da ‘tsibi’ da ‘dukka’ da ‘yawanci’ da ‘galibi’ da ‘rabi’.  Ya ce ire – iren wad’annan kalmomin na iya zuwa kafin suna (zagi) domin su raka shi ya zama yankin suna. Misali:

d’imbin mutane.

tarin alk’alumma.

dukkan yaran.

yawancin mutane.

Bagari (1986) ya bayyana cewa ajin siffofin adadi kamar ajin siffa yake, ta fuskar yin amfani da harafin lik’i tsakanin su da suna. Amma sun bambanta ta daidaiton jinsi da adadi. Domin su kalmomin siffofin adadi ba su da sharad’in nuna daidaiton jinsi da adadi tsakanin su da suna. Saboda haka Bagari yake ganin ya fi dacewa da ya kira su da ‘harafin adadi’. Sannan kuma wad’annan kalmomin suna iya zuwa bayan suna. Misali:

kaya tuli.

kaya tsibi.

A shafi na 122, Bagari (1986) ya kawo wasu daga cikin kalmomin k’irgau da ya kira da ‘adadin k’idaya’. Kalmomin da ya ba da misali: da su, sune; ‘yaro d’aya’ da ‘yara goma’ da ‘shekara ta biyar’ da ‘wata na goma’ da ‘kwana na bakwai’. Misali:

yaro d’aya.

shekara ta biyar.

wata na goma.

Bagari (1986) ya kawo wannan misalin ne don ya nuna irin kalmomin k’irgau da kan iya zuwa a bayan suna. kuma ya bayyana cewa jigon adadin lissafi na iya zama mufradi (tilo) ko jam’i. Misali:

yaro/yara uku.

doki /dawaki ashirin.

Ya ce ana iya tsarma kalmar ‘guda’ a tsakanin jigo da adadi. Misali:

mutum /mutane guda talatin.

Sani (1999) ya gudanar da nasa nazarin wanda ya ta’allak’a shi da gurbin fitowar k’irgau. Ga yadda abin yake:

Sani (1999) ya ba da misali: da kalmomin k’irgau a matsayin ‘yan rakiya da  kan iya zuwa bayan suna. Inda ya kawo misali: da kalmomi kamar haka: tuli’ ‘kad’an’ ‘d’aya’ ‘hamsin da biyar’. Misali:

littafi d’aya.

ganye tuli.

takardu kad’an.

naira goma .

akwatuna shida.

Ya ba da misali: a cikin jimla kamar haka:

littafi d’aya aka saya.

Newman, (2000) ya nazarci k’irgau da kyau, inda ya yi magana kan k’irgau a cikin aikin nasa,  a babi na hamsin da uku (53), cikin shafi na 379 zuwa na 391. Newman, (2000), ya raba k’irgau zuwa manyan rukunoni guda uku. A k’ark’ashin kowane rukuni akwai wasu k’ananan nau’o’in k’irgau, wad’anda suke nuna yadda kowace kalma ta k’irgau take aikin tantance suna dangane da adadi. Ga yadda nazarin ya kasance:

  • Babban rukuni na d’aya: Ya kasa shi zuwa nau’i goma sha hud’u kamar haka:

  • Nau’i na d’aya Newman (2000) ya kawo tsarin kalmomin k’irgau kadina, yadda ake amfani da su wajen lissafi da yadda suke raka suna. Misali: d’aya, biyu, biyar, tara, goma, d’ari, dubu. Ya kawo kalmomin lissafi na asali a harshen Hausa, irin su d’aya zuwa goma, da kuma tsarin yadda ake ci gaba da lissafi bayan goma zuwa dubu. Ga yadda abin yake; ‘gomiya d’aya’ da ‘gomiya biyu’. Ya kuma bayyana cewa ana amfani da kalmar háùya d’aya a matsayin ashirin. Kalmomin dubu da d’ari duk na Hausa ne amma kalmomi irin su; ashirin, talatin, arba’in, hamsin, sittin, saba’in tamanin, casa’in, duk na Larabci ne. Haka kuma kalmomin miliyan, ko miliyoyi, na Ingilishi ne.


(ii)K’irgau nau’i na biyu: A wannan nau’in ya yi bayani ne a kan  ma’auni, Misalin irin kalmomin su ne; guda, da mudu, da tulu, da wuya, da kilo d.s. Ga misalinsu a yankin suna:

(i)      kujera (guda) d’aya,

(ii)     gidan – ashana (guda) hamsin.

(iii)A nau’i na uku: Newman (2000) ya kawo kalmomin k’irgau kadina na maimaici da ake iya maimaita su don fayyace suna, tare da wasu kalmomin k’irgau na bai-d’aya.

Kalmomin su ne; d’aya - d’aya ko d’aid’ai, biyu – biyu ko bibbiyu, uku  uku, ‘tara – tara’  ‘kad’an – kad’an’  ‘nawa – nawa’. Misalinsu a yankin suna shi ne;  riguna shida – shida, nawa – nawa gyad’a?

  • Nau’i na hud’u ya nuna yadda kalmar k’irgau kadina suke zuwa domin fayyace suna. Misali: mata goma, katifa hud’u.

  • K’ark’ashin nau’i na biyar Newman (2000) ya yi bayani kan yadda k’irgau na kadina suke fitar da adadin wakilin suna. Misali:


(i)      Mu shida muka ci jarrabawa,

(ii)     Ku bakwai d’in nan ba za a kar’be ku ba.

  • Nau’i na shida ya dubi yadda k’irgau kan had’u da wasu kalmomin harshe da suka shafi yankin suna domin fito da adadin suna tare da ire –iren wad’annan kalmomin. Misali:


(a) ‘yanmakaranta talatin

(b) sojojin gwamnati metan da hamsin

(c) d’aya yaron      d’aya yarinyar

(d) mahaukatan karnuka shida

(e) yanmata uku masu kyan gani.

  • Newman (2000) ya nuna yadda k’irgau ma’auni yake zuwa tare da k’irgau kadina don fayyace suna marar k’irguwa. Misali:


(i)      gero buhu biyar.

(ii)     dawa dami hud’u.

(iii)    kananzir duro goma.

  • A nau’i na takwas Newman (2000) ya yi bayanin yadda kalmar k’irgau kadina ke had’uwa da kalmar k’irgau na bai-d’aya su fayyace suna ya zama yankin daidaito. Misali:


duk d’aya ne.

  • A wannan nau’in na tara, Newman (2000) ya yi bayani ne dangane da yankin suna d’aya da yake d’auke da kalmomin suna guda biyu da k’irgau ya fayyace kowanne daga cikinsu. Misali:


ayaba sha biyu da mangwaro hud’u.

  • Nau’i na goma ya dubi kalmomin k’irgau odina ‘na’ da ‘ta’ wad’anda ake had’a su da kalmomin k’irgau kadina don su bayyana adadin suna a yankin suna. Misali:


na farko, ta tsakiya, babi na hud’u.

  • A cikin wannan nau’in na sha d’aya, Newman (2000) ya kalli kalmar da ake amfani da ita tare da k’irgau kadina don nuna yadda ake ninka adadin lambobin k’irgau kadina ta hanyar lissafi. Kalmar ita ce ‘sau’. Misali:


(i)      sau d’aya.

(ii)     tara sau shida.

  • A nau’ in nan na sha biyu, ya yi bayani ne  dangane da kalmomin amsa – kama, yadda suke fayyace kalmomin k’irgau kadina a yankin suna. Misali:


(i)      lemu d’aya tak aka ba ni.

(ii)     awa biyu cur  ya yi a kan hanya.

Newman (2000) ya dubi yadda yankin harafi yake zuwa tare da k’irgau kadina don su nuna adadin suna. Ga misali:

yana nan wajen mil goma daga gari.

  • Nau’i na sha uku, Newman (2000) ya kalli kalmomin k’irgau kadina a matsayin suna. Ga misali:


(i)      goma ce.

(ii)     goma ta fi takwas.

  • A nau’i na goma sha hud’u a nan Newman (2000) ya dubi kalmar k’irgau kadina a matsayin wakilin suna. Ga misalin yadda abin yake:


d’aya ta fi son kofi, d’aya ta fi son shayi.

(b) A babban rukuni na biyu, Newman (2000) ya mai da hankali ne kan k’irgau na bai - d’aya, amma kalmar ‘duk’ kad’ai ya duba inda ya kasa ta gida uku. Ga yadda ya yi nazarinta:

  • Duk a matsayin mafayyaciya.


Ya bayyana cewa tana da fasali iri biyu, tana zuwa da wasali a k’arshenta ‘duka’, sannan tana iya zuwa babu wasali, ‘duk’.  Ya ce tana zuwa kafin suna, a nan an fi son wadda ba ta zo da wasali a k’arshenta ba. Amma ana amfani da mai wasali a k’arshe. Kuma tana zuwa bayan suna, a nan an fi son mai wasali a k’arshenta duk da cewa ana amfani da marar wasali. Ga misali:               (i) duk fasinjojin                   fasinjijon duka

  • Duk a matsayin wakilin suna.


A nan Newman (2000) ya bayyana cewa kalmar ‘duk’ kan yi aiki irin na wakilin suna. Misali:                                                            duk za su shiga jirgi.

Amma idan ta zo da kar’bau kalmar za ta zo a matsayin wakilin suna na jam’i. Misali:

(a)      dukkansu.

(b)     dukkan biran.

  • ‘Duk’ a matsayin kalmar bayanau.


Idan ta zo kafin suna kalmar tana aiki ne irin na bayanau. Misali:

(a) duk ya lalace.

(b) duk ban damu ba.

(c) Babban rukuni na uku, a wannan rukunin Newman (2000) ya yi bayani kan sauran k’irgau da ba a saka su cikin kason da ya gabata ba. A cikin wannan rukuni ya kalli kalmomin k’irgau irin su ‘yawa’ da ’nawa’ da ‘kad’ai’ da ‘kad’an’ da ‘dama’ da ‘dama - dama’ da ‘k’alilan’, inda ya yi bayanin cewa kalmar ‘dama’ da ‘yawa’ ana had’a su da mahad’i sannan a wani lokaci ana had’a su da kalmar ‘gaske’.

Jaggar (2001) Marubucin ya gudanar da aikin nazarin nahawun Hausa, inda ya dubi k’irgau a shafi na 358 zuwa na 381. Sannan ya raba k’irgau zuwa manyan rukunoni biyu. Rukuni na d’aya yana d’auke da nau’o’in k’irgau guda shida. Da farko an samar da kalmomin k’irgau na kadina (cardinal quantifier). Inda Jaggar (2001) ya fara da adadin lissafi na; ‘sifiri’ ‘d’aya’ ‘biyu’ ‘uku’ ‘shida’ ‘tara’ ‘goma’. A nan Jaggar ya nuna cewa idan aka sami k’ari kan adadin k’idaya ‘goma’ to ana amfani da kalmar ‘sha’ a tsakanin ‘goma’ da k’arin da aka samu. Misali:

‘goma sha d’aya’, ‘goma sha biyu’.

Ya bayyana cewa adadin lissafi irin su; ‘ashirin’ da ‘talatin’ da ‘arba’in’ da ‘hamsin’ da ‘sittin’ da ‘saba’in’ da ‘tamanin’ da ‘casa’in’ duk an aro su ne daga kalmomin lissafi na Larabci. Sannan idan aka sami k’arin adadi a kan kalmomin lissafi na Larabci, Ya bayyana cewa sai an k’ara kalmar ‘da’ a tsakanin su da k’arin da aka samu. Misali:

‘ashirin da d’aya’ ‘casa’in da tara’ tamanin da bakwai’. Haka kuma ya bayyana kalmomin k’idaya na iya fayyace suna a yankin suna na jimlagau kadina na iya zuwa a bayan suna tilo ko jam’i domin ya fayyace shi. Ga misali:n zuwan su a yankin suna:

mota hud’u.

yara biyu.

‘ya’yansa goma.

Jaggar (2001:359) ya bayyana cewa ‘d’aya’ ko ‘guda’ yana fayyace suna tilo ne. Misali:             yaro d’aya/guda.

yarinya d’aya/guda

Bayan wannan Jaggar (2001) ya ci gaba da bayani kan k’irgau ma’auni (enumerator). Inda ya kawo kalmar  ‘guda’ da takan zo domin fayyace suna tare da adadin lissafi na k’irgau kadina ( cardinal number). Marubucin ya nuna cewa kalmar ma’auni ana tsarma ta ne a tsakanin kalmar suna jam’i da kalmar k’irgau kadina (cardinal number)  Misali:

hatsi dami biyu.

fetir galan goma.

dawa mudu hud’u.

Haka kuma ana iya samun harafin nasaba ya zo lik’e da ma’auni. Misali:

damin hatsi biyu.

Kalmar k’igau ta ‘fiye da’ tana zuwa a matsayin ma’auni a inda take zuwa tsakanin suna da k’irgau kadina don bayyana adadin hard’ad’d’en yankin suna (complex compound NP). Misali:

Ya na da ‘ya’ya fiye da goma.

Jaggar (2001) ya nuna yadda kalmar k’irgau na tambayau ke zuwa tare da suna. kalmar ita ce ‘nawa?’. Ga yadda misalin yake:

nawa aka kawo?

mutane nawa suka kaama?

jakuna guda nawa suka mutu?

Jaggar (2001) ya dubi yadda kalmomin da ake amfani da su domin ba da misali: suke zuwa tare da k’irgau. Misali:  ‘wajen’ da ‘kamar’ da ‘kusa’. A nan Jaggar ya nuna irin yadda ake amfani da su a yankin suna. misali:;

kamar kwana nawa za ka yi a Legas?

Jaggar (2001) yace ana iya maimaita kalmomin k’irgau kadina wajen bayyana adadin suna. misalin kalmomin su ne: ‘d’aya - d’aya’ ko ‘d’ai-d’ai’, ‘biyu-biyu’ ko ‘bibbiyu’, ‘uku-uku’ ‘tara-tara’ ‘goma-goma’ ‘d’ari-d’ari’.

Misalin su a yankin suna:

raguna tara-tara aka ba malamai.

gero mudu bakwai-bakwai.

 

Jaggar (2001) ya dubi kalmomin k’irgau odina (ordinal number), ya bayyana cewa kalmomin k’irgau odina suna zuwa ne a tsakanin suna aikau (NP1) (idan a bayyane yake),da k’irgau kadina (cardinal number), wad’annan kalmomin su ne: ‘na’ da ‘ta’. Misali:

babi na d’aya.

Manunin mallaka na zuwa a lik’e da suna aikau, kafin kalmar k’irgau odina. Misali:

matata ta biyu.

Kuma k’irgau odina yana zuwa ne da suna tilo a yankin suna. Misali:

littafi na uku.

matata ta hud’u.

Kalmar k’irgau odina ta gaba d’aya (general ordinals) Jaggar (2001) ya ce wani lokoci ana samar da sune, ta hanya suna d’an aikatau. misali:  ‘farko’ ‘tsakiya’ ‘k’arshe’. Kamar haka:

farko = fari(i) = fara

Inda ya fassara da harshen Ingilishi kamar haka:

beginning = begin

Ya ce wani lokaci ana had’a shi da kalmomin ‘na’ da ‘ta’, don su fito da adadin suna tilo da jam’i tare da manunin mallaka. Misali:

zuwana na farko ke nan.

aji na farko.

Jaggar (2001) ya bayyana cewa, kalmar k’irgau odina ta ‘farko’ da ‘k’arshe’ ana had’a su da suna aikau tare da harafin mallaka. Misali:

gwajin farko.

A shafi na 365 Jaggar (2001) ya dubi adadin lissafin da kai adadin d’aya ba (fraction number) a Hausa. Ya bayyana cewa akasarin kalmomin da ke nuna irin wannan adadin Hausa ta aro su ne daga Larabci. Ire –iren wad’annan kalmomin sune; ‘sulusi’ ‘rubu’i’ ‘rabi’ ‘humusi’ ‘ushiri’ . Wad’annan kalmomin suna zuwa ne tare da harafin mallaka. Misali:

humusi n dukiyarsa.

sulusin gadonsa.

A kan yi amfani da kalmar ‘bisa’ waje bayyana adadin. Misali:

d’aya bisa uku.

bakwai bisa takwas.

Ana amfani da kalmar ‘kwata’ da aka aro daga Ingilishi wurin bayyana kashi d’aya bisa hud’u (1/4).

Jaggar (2001) ya nuna yadda Hausa take amfani da adadi ta fuskar nuna lokacin agogo da kwanan wata, da lokutan shekara. Ya ce akwai mahad’in nasaba da yake zuwa tare da suna na adadin kwanan wata. Jaggar ya ce ana ambatar kalmomin ‘k’arfe’ da ‘minti’ da ‘sakan’ tare da adadin k’irgau kadina wajen bayyana adadin suna na lokacin agogo. Misali:

zan dawo da k’arfe biyu.

yanzu k’arfe goma sha biyu da minti ashiri.

Misali: na kwanan wata;

ranar goma sha biyar ga watan safar.

Jaggar (2001) ya bayyana yadda ake sarrafa ‘kashi’ (percentage) a Hausa. A wannan wuri Jaggar ya ba da misali kamar haka:

kashi talatin cikin d’ari na gidaje suna da ruwan famfo.

haka kuma jaggar ya nuna cewa ana amfani da kalmar ‘d’igo’ wajen nuna adadi na kashi. Misali:

hamsin d’igo biyu.

Jaggar (2001) ya yi bayani kan kalmar k’irgau na bai d’aya (universal quantifier) ya dubi kalmomin ‘ko’ da ‘duk’. Inda ya ce ana iya amfani da su, ta fuskoki uku.

Da farko kalmar ‘ko’ tana iya zuwa a had’e da kalmomin ‘wace’ da ‘wane’ da ‘wad’anne’ a matsayin mafayyaciya (determiner). Ga yadda ya ba da misali:n su:                                                               kowace

kowane

kowad’anne

misalin su a cikin yankin suna:

kowane d’an Nijeriya idan ya had’u da d’an’uwansa

kowace yarinya za ta sayi zare.

kowad’anne irin kaya.

A wani nau’in Jaggar ya bayyana cewa kalmar ‘ko’ idan ta had’u da kalmomin tambaya na ‘wa’ da ‘me’ tana zuwa a matsayin wakilin suna. Jaggar (2001) ya kawo wannan tsarin kamar haka:

kowa

kome

Ya fassara wad’annan kalmomin da harshen Ingilishi, inda ya ce;

kowa                         ‘everyone/ everybody’

kome                      ‘everything’

Misali a yankin suna:

kowa ya san haka.

ya san kowa a nan garin.

zan gaya masa kome.

‘Yar’aduwa (1984) da Newman (2000) da Jaggar (2001) sun yi tarayya kan matsayi kalmar ‘duk’ a fannin nazarin k’irgau. Inda suka ce tana iya zuwa a matsayi uku. Wato a ‘wakiln suna da bayanau da kuma matsayin mafayyaciya.

 1.1.2 Bitar Kundaye


‘Yar’aduwa (1984), wannan aiki na ‘Yar’aduwa kundin digiri na biyu ne, da aka  yi a A.B.U. Zaria. Marubucin wannan kundin ya yi k’ok’arin bayyana d’anrakiya k’irgau gwargwadon iyawarsa, ya raba aikin nasa zuwa babuka hud’u. A babi na farko ya gabatar da fasalin aikin nasa. Sannan ya gudanar da bitar ayyukan da suka gabaci nasa.Ya kawo ma’anar k’irgau, sai kuma ya kawo rabe – raben suna, don ya gabatar da tsarin  da yake son bi, na amfani da k’irgau wajen nuna adadin suna, da gurbin da  k’irgau ke iya fitowa don ya raka suna. Misali: shi ne, ya kawo suna k’irgau (countable noun) ‘hula’ da ‘gida’ da ‘awaki’ sannan kuma ya kawo suna marar k’irguwa (uncountable noun) kamar  ‘gishiri’ da ‘suga’ da ‘gero’ ya nuna yadda k’irgau ke zuwa don raka kowane rukuni da wad’annan rabe – raben na suna. Ya kawo hanyoyin da za a bi don nuna yadda k’irgau ke iya raka suna. Ga yadda suke:

  • Fasalin k’irgau


A k’ark’ashin wannan kason ya bayyana cewa sunaye da k’irgau zai iya raka wa su ne, suna na zahiri wanda za a iya ta’bawa (Concrete object) wannan rukunin ya shafi suna mai k’irguwa da marar k’irga.

  • Fasalin rakiya


Wannan rukunin ya kawo nau’o’in suna da adadin k’irgau kadina na lambobi (Numerical) da k’irgau ma’auni ke iya raka wa. Misali:

  • Fad’i: Wato sunan da k’irgau ma’auni da k’irgau kadina ke iya rakawa. Ya kawo misali:n kalmomin k’irgau ma’auni da ke zuwa tare da k’irgau kadina wajen raka suna kamar haka:


laba’ da ‘k’afa’ d.s.

  • Tsawo: Ya ba da kalmomin da ake amfani da su wajen nuna tsawo, da suka had’a da:


‘dungu’ da ‘taki’ da ‘inci’ da ‘yadi’ da ‘mil’

  • Zurfi: ya nuna irin kalmomin da suke nuna adadin zurfi irin su:


‘gaba’ da ‘k’afa’

  • Manunin lokaci : ya fito da kalmomin masu nuna lokaci, wad’anda suka k’unshi:


‘sakan’ da ‘minti’ da ‘awa’.

A babi na biyu ‘Yar’aduwa (1984) ya bayyana cewa k’irgau a Hausa ya rabu zuwa gida biyu kuma rabon yace ya yi shi ne bisa la’akari da tsarin zuwan k’irgau a cikin jimla, da kuma fasalin ma’anar shi.

Rukunin farko ya kira shi da suna k’irgau na k’irgau kadina/ asali (absolute Quantifier), wato k’irgau kadina mai nuna adadin lissafi (cardinal number) a wannan rukunin an bayyana cewa kalmomin lissafi irin, ‘d’aya’ da ‘biyu’ da ‘goma’ da ‘hamsin’, su ne ake amfani da su a wannan rukunin. Kuma ana nuna adadin suna mai k’irguwa (countable noun) da suna marar k’irguwa (uncountable noun) da shi. Rukuni na biyu kuwa ya kira shi da k’irgau dogarau (Relative Quantifier) kuma ya ce, ya nazarce su ne bisa la’akari da ma’anar da suke d’auke da ita. Wannan rukunin yana d’auke da wasu ire – iren k’irgau har guda biyar. Ga yadda ya bayyana su:

  • K’irgau dogarau na d’aya (relative quantifier1): Wannan rukunin yana d’auke da kalmomi irin su; ‘kad’an’ da ‘da yawa’ da ‘da dama’.

  • K’irgau dogarau na biyu (relative quantifier2): Shi kuma yana k’unshe da kalmar k’irgau na tambayau (Interrogative Quantifier) ‘nawa?’.

  • K’irgau dogarau na uku (relative quantifier3): A wannan rukunin kalmomin amsa - kama yake d’auke da su, kamar;  ‘jingim’ da ‘da’ba’ba’ da ‘tak’. Kuma ya kira shi da suna k’irgau na amsa – kama (Ideophonic Quantifier).

  • K’irgau dogarau na hud’u (relative quantifier4): Ya kira shi da suna k’irgau na tsigalau (Demunitive Quantifier) kuma yana d’auke da kalmomin tsigalau, su ne; ‘yar’ da ‘d’an’ da ‘ ‘yan’.

  • K’irgau dogarau na biyar(relative quantifier 5): Shi ya kira da k’irgau na - d’aya (Universal Quantifier) inda ya kawo kalmar ‘duk a matsayin k’irgau na - d’aya.


‘Yar’aduwa, (1984) ya d’auki kowane d’aya daga cikin wad’annan rukunoni ya gudanar da bayani a kansa. A rukunin farko ya nuna yadda k’irgau kadina yake raka suna, inda ya bayyana cewa k’irgau kadina yana zuwa ne bayan suna. Kuma ba a yarda da zuwan shi kafin suna ba.

Umar, (2012) Nazari ne da aka gudanar kan k’irgau na Hausa, inda aka dubi wasu mahimman wurare da magabata suka bari a cinkushe ba tare da an warware su dalla-dalla ba ta yadda manazarta za su fahimci yadda fasalin ire-iren wad’annan kalmomin na k’irgau suke. A babi na biyu an gudanar da bitar ayyukan da aka yi kan k’irgau na Hausa inda nazarin ya warware ayyukan masana irin su; Kraft da Kirk-green (1973) da Galadanci (1976) da ‘Yar’aduwa (1984) da Bagari (1986) da Sani (1999) da Newman (2000) da Jaggar (2001) da Amfani (2010). Bayan bitar sai aka biyo da bayanin tsarin ginin jimlar Hausa da nau’o’inta tare da gabatar da yankunan jimla a babi na uku. A babi na hud’u kuwa a nan ne aka baje mahimman wuraren da nazarin ya tato su daga babi na biyu a lokacin gudanar da bitar ayyukan.

1.1.3 Bita kan Muk’alu  Da Mujallu


Amfani (2004), a wata takarda da ya gabatar mai taken “waiwaye adon tafiya: bitar rabe-raben azuzuwan kalmomi” inda har ya kawo irin muhawarar masana dangane da ajin sifa, wanda yace masana sun yi mahawara a kan ajin sifa. Wasu na ganin Hausa na da ajin sifa, wasu kuma na ganin Hausa ba ta da ajin sifa.  Wanda yake wannan takarda ta shi tana da alak’a da aikina, saboda ya ta’bo maganar azuzuwan kalmomi biyu ne; wato ajin sifa da ajin wakilin suna.

Amfani (2010), ya yi tsokaci ne kan wasu gurabe na ayyukan da Newman (2000) da Jaggar (2001) suka yi a game da k’irgau. Ya yi bayani kan wasu matsalolin fahimta da aka samu a lokacin nazartar wad’annan nau’o’in na k’irgau. Nau’o’in sun had’a:

K’irgau amsa-kama: Amfani ya k’ara haske kan kalmomin k’irgau amsa –kama wad’anda ke zuwa tare da k’irgau kadina. Ire-iren wad’annan kalmomi sun had’a da; ‘cur’ da ‘tak’ da ‘tal’ da ‘kawai’ inda ya ce k’irgau ne masu cin gashin kansu. Kuma ya fassara da harshe Ingilishi da cewa ‘only’. Amfani y ace zuwan ire-iren wad’annan kalmomi da k’irgau kadina shi ya sa wasu manazarta suke ganin kamar suna fayyace kalmomin k’irgau kadina ne, amma abun ba haka yake ba. Misali:

yaaroo d’aya tak/tal/kawai

maataa biyu rak/kawai

Ya fassara su da Ingilishi kama haka;

‘one boy only’

‘two women only’

A nan Amfani ya tabbatar da cewa kalmomin da aka kira da k’irgau amsa -kama, ba su dace da wannan kason ba domin kalmomi ne masu zaman kansu a fannin k’irgau.

Amfani (2010) ya dubi maganar da Newman (2000) ya yi kan kalmar k’irgau kadina inda ya ce tana iya zuwa a matsayin suna aikau (subject). Misali:

hamsin ce

Kalmar suna a nan ita ce ‘hamsin’  ita kuwa kalmar ‘ce’ ta k’arfafa ce. Amfani ya ce wannan batu ba haka yake ba. Ya ce Hausa ta amince da a shafe suna idan sunan sananne ne. Misali

naira hamsin ce.

‘naira’ kalmar suna ce, ‘hamsin’ kuma k’irgau kadina ce, sannan ‘ce’ kalmar k’arfafawa ce.

K’irgau ma’auni: Amfani ya sake ba da haske a kansa ne sakamakon nazartar aikin su Newaman (2000) da Jaggar (2001) da ya yi. Inda ya kawo yanayin yiwuwar fitowar k’irgau ma’auni  a mahalli biyu. Inda ya fara da cewa Hausa ba ta aminta da zuwan kalmomin k’irgau kadina kai – tsaye ba wajen nuna adadin suna marar k’irguwa. Misali:

daawaa gooma

ruwa biyar

Sai an sak’ala kalmar k’irgau ma’auni. Misali:

daawaa buhuu gooma

manja kwalbaa biyar

Haka kuma kalmar k’irgau ma’auni na iya zuwa kafin suna.Misali:

buhun dawa gooma

kwalbar manja biyar

Amfani (2010) ya yi k’arin haske ne kan manunin bagire (location marker). Inda ya bayyana cewa manunin bagire shi ke nuna muhallin da k’irgau ma’auni yake zuwa, ko dai ya zo kafin suna ko a bayan suna. Ya ce idan ya zo kafin suna k’wayoyin ma’ana na –n da –r da –n suke nuna zuwan nasa, idan kuwa a bayan suna ne, to wasalin k’arshe na kalmar k’irgau ma’auni yake komawa dogo.

Amfani (2010) ya dubi k’irgau odina, inda ya ce kalmomin ‘na’ da ‘ta’ su, suke bambantawa tsakanin odina na gaskiya (true ordinal) da odina na lak’abi (ordinary ordinal). Misali:

Na asali: (na/taa) farkoo ‘first’, (na/ta) k’arshee, ‘last’ (na/ta) tsakiya ‘mid’.

Na lak’abi: farkoo ‘beginning’, ‘k’arshe’ ‘end’, tsakiya ‘middle’.

Misalin su a cikin yanki (phrases)

(i)      shekara r farkoo    (a)      farko n shekara

(ii)     wata n k’arshee     (b)     k’arshe n wata

(iii)    wata n tsakiya       (c)      tsakiya r wata

A misali na ‘i’ da ‘ii’ da ‘iii’ Amfani (2010)  ya ce wad’annan k’wayoyin ma’anar da suka zo a cikin misalin suna a matsayin manunin nasaba ne. A misali na ‘a’ da ‘b’ da ‘c’ suna a matsayin kalmomin harafi ne. Sannan a misali na ‘i’ zuwa ‘iii’ kalmomin suna na ‘shekara’ da ‘wata’ su suke jagorantar yankin. Kuma sun eke fayyace ‘farko’ da ‘tsakiya’ da’k’arshe’.

Newman (2000) da  Jaggar (2001) sun ce a cikin aikinsu kalmomin ‘na’ da ‘ta’ ana cire masu wasullansu su koma ‘-n’ da ‘-n’ da ‘-r’ kuma dukkan su manunin nasaba ne. Amfani (2010) ya ce wad’annan kalmomi ba d’aya suke ba. Amfani ya ci gaba da cewa; a misali na ‘i’ da ‘ii’ da ‘iii’ wad’annan sune manunin nasaba. Amma a misali na ‘a’ da ‘b’ da ‘c’ su kuma harafi ne.

Amfani (2010) ya ce wasu yankunan na harafi suna aiki irin na k’irgau, ire-iren wad’annan yankunan ana samun kalmar harafi ke jagorantar yankin sai kuma yankin suna ko k’irgau kadina ya biyo baya a cikon batu. Misali a alamce:

YHf                   Hrf  cikon batu (complement)

Cikon batu            (YSn / K’gkadina)

Ire- iren wad’annan yankin na harafi sun had’a da:

‘fiye da ‘ da ‘k’asa da’ da  ‘sama da’ da ‘kusa da’ da ‘kamar’ da ‘wajen’ da ‘kusan’. Misali:

fiye da mil goma.

Audu ya saci kud’i  fiye da Lawal.

Irin wad’annan yankunan na harafi sukan yi aiki irin na k’irgau.

Amfani (2010) ya dubi aikin da su Newman (2000) da Jaggar (2001) suka yi kan k’irgau na d’aya (universal quantifier). Inda ya gudanar da k’arin bayani kan kalmomin ‘duk’ da ‘ko’.

Newman (2000) da Jaggar (2001) sun ce kalmar ‘duk’ tana aiki irin na wakilin suna a muhallin da suna ke fitowa. Misali:

duk su n mutu.                ‘All died’

Kalmar ‘duk’ ita ce wakilin suna a matsayin suna aikau (subject). A nan Amfani ya ce ba su kula ba ne, akwai sunan da yake shi ne aikau na yanki wanda aka ajiye. Ga yadda abin yake:

duk mutanee su n mutu.            ‘All people’

‘duk’ a matsayin wakilin suna na jam’i. A nan Newman (2000) da Jaggar (2001) sun ce kalmar ‘duk’ ko ‘duka’ yana iya zama suna aikau (subject). Misali:

Mu duka mu n yarda

e za n harbee su duka.

Mu kula a nan kalmomin wakilin suna na aikau da wakilin suna  kar’bau, an ajiye su, sai aka bar k’irgau na bai d’aya kad’ai. Amfani ya ce doka ta yarda da  ajiye wakilin sunan da ya zo a yankin suna na jimla.

Amfani (2010) ya sake duban   aikin Jaggar (2001:380) inda ya ce ‘duk’ na iya zama bayanau idan aka kwatanta ta da kalmomin Ingilishi ta ‘completely’ da ‘entirely’ da ‘totally’. Misali:

Hausa                                                Ingilishi

(i)      Duk naa mantaa da shi.              ‘I completely forgot about it.’

(ii)     Duk zaafii ya naa daamuunaa    ‘the pain is totally bothering me’

(iii)    Oofishiinaa duk yaa k’oonee      ‘My office burned down completely’

Amfani ya ce a nan ‘duk’ ba bayanau ba ce, saboda an ajiye suna aikau na yankin suna. Inda aka bar kalmar k’irgau ta d’aya. Ga yadda abin yake:

A misali na (i) yankin sunan shi ne ‘ Nii duk’ a misali na (ii) shi kuma ‘duk zaafii’  a misali na (iii) yankin suna shi ne ‘oofiishii naa’. Amfani ya ce idan  aka yi la’akari da fassarar Ingilishi da Jaggar ya yi ana iya cewa k’irgau na d’aya ‘duk’ bayanau ne.

Amfani (2010) ya sake duba kalmar ‘ko’  inda ya k’alubalanci Jaggar (2001:372) da Caron (1991), inda suka ce ‘koowaa’ da ‘koomee’ da ke nufin ‘everything’ a Ingilishi cewa ‘koo’ an had’a ta da kalmomin tambaya (wh-words) a Hausar Arewa, ba daidai ba ne.

‘Koowaa’ ko ‘koowaa da koowaa’ da ‘koomee’ ko ‘koomee da koomee’ sun fi kama da suna bisa k’irgau  (ba mafayyaciya). Misali:

Koowa ya a zoo.  ‘everyone/everybody came’

Koomee ya a fitoo tsaf.  ‘everything appeared well’

Amfani (2010) ya fito da yadda kasafin Kalmar ‘koo’ filla – filla inda ya kawo sauran misalan kamar haka:

Kalmomin tambaya (wh-words) na zahiri su ne; ‘koowaa’ da ‘koomee’ da ‘koo’inaa’ da ‘kooyaya’.

Amfani ya ce Jaggar (2001:370) ya tattauna kan tsarin tasarifi na k’irgau na bai d’aya, na kalmar ‘every’ a Hausa. Amfani ya tunatar da cewa a aikinsa na (1996:88) ya bayyana yadda ake gudanar da tasafin kalmar ‘koo’ a Hausa. A matsayin tan a cikakken k’irgau (quantifier proper) da yadda take had’uwa da kalmar manunin yarjejeniya (agreement suffix) wanda yake fayyace suna dangane da jinsi da adadi.

Muhammad, (2013) muk’ala ce da aka gabatar a wurin taron k’ungiyar masana kimiyyar harshe ta Nijeriya (Linguistic Association of Nigeria). Wannan aka gudanar kan kalmomin lissafi na harsunan Nijeriya. Muhammad ya kawo jerin kalmomin lissafi na Zabarmanci tun daga matakin lissafi na d’aya zuwa goma. Sannan ya sake kawo jerin kalmomin lissafi daga goma sha d’aya zuwa goma sha tara. Ya kuma kawo na ishirin da d’aya zuwa ishirin da tara. Dagan an ya jero kalmomin d’ari biyu zuwa d’ari tara. Muhammad (2013) ya kawo tak’aitaccen bayani kan kalmomin k’irgau odina daga na farko zuwa na goma. Ya kawo yadda kalmomin k’irgau na maimaci da na sau. Duk da cewa Muhammad (2013) ya gudanar da wannan nazari ba zai hana wannan nazarin gudanuwa ba, saboda bai fad’ad’a bincike kan k’irgau kadina da k’irgau ma’auni da na tambayau da kuma na tsigalau da na amsa-kama ba.

Umar, (2013) muk’ala ce da aka buga a mujallar ‘Dund’aye ta sashen harsunan Nijeriya, wadda take bayani kan matsayin k’irgau a nahawun Hausa. Inda aka kawo bayanin kan nahawun harshe daga nan sai aka waiwayi mahimman ayyukan da aka gabatar game da k’irgau d’in Hausa. Muk’alar ta sake waiwayar aikin da aka yi wanda ya shafi ma’anar k’irgau a harsunan duniya. Muk’alar ta kawo rabe-raben k’irgan Hausa inda ta kawo nau’o’in k’irgau goma daga k’irgau na Hausa tare da ingantattun misalai.

Abin la’akari a nan shi ne duk binciken da aka gabatar wajen bitar ayyukan da suka gabaci wannan aiki ba a samu wani aiki da ya yi daidai da wannan aikin ba, ta fuskar take ko manufa. Don haka wannan bincike ya samu hurumi daidaitacce da za a iya aiwatar da shi.

 

 

 

1.2 Dalilan Bincike


Komai na da dalili idan har za a gudanar da shi, don haka wannan nazari yana da na shi dalilai. Daga cikin dalilan sun had’a da:

  • Cika k’a’idojin da jami’a ta shimfida kan duk wani dalibi da ya zo shekarar k’arshe ta karatu don ya ba da ta shi gudunmuwa a fagen da yake karatu.

  • Domin bunk’asa da kuma ciyar da harshen Hausa da na Zabarmanci gaba ta fuskar nazarin kwatanci.

  • Lokacin da ake gudanar da bitar ayyukan da suka gabata, ba a ci karo da wani aiki da ya yi daidai da wannan bincike ba, ko ta fuskar take, ko tsarin aiki ko manufa. Don haka wannan aikin ya sami dalilin gudanuwa.


1.3 Manufar Bincike


Manufar wannan bincike shi ne fito da irin tsarin nahawun Zabarmanci musamman a fagen nazarin ginin jimla. A ginin jimlar ma yankin suna za a duba, don fito da yanayin rakiyar d’an rakiyar nan da ake kira k’irgau. Za a yi amfani da harshen Hausa wajen gudanar da wannan nazarin don kasancewar Zabarmawa makwabtan Hausawa ne.

1.4    Farfajiyar Bincike


Wannan bincike za a gudanar da shi ne a kan batun ire-iren k’irgau na harshen Zabarma tare da bayyana irin mahimmancinsa. Farfajiyar wannan binciken za ta kasance ne a k’asar Argungu da Dolekaina da Mak’era da ke jihar Kebbi.

 

 

1.5    Hanyoyin Gudanar Da Bincike


Manyan hanyoyin da za a bi wajen gudanar da wannan binciken su ne kamar           haka:

  1. Za a yi hira da tsofaffin zabarmawa na k’asar Argungu da Dolekaina da Mak’era maza da mata.

  2. Za a gudanar da karance-karance na litattafan nahawu da suka shafi ilimin ginin jimla. Domin samun nasarar kammaluwar wannan binciken.

  3. Ziyartar d’akunan karatu na manyan makarantu zai taimaka wajen tattaro bayanan da suka dace da wannan binciken.

  4. Duba mujallu da k’asidu da muk’alu da aka buga, hanya ce babba da za a inganta wannan nazarin.


1.6    Mahmmancin Bincike


Bincike kowane iri ne yana da muhimmanci ga rayuwar al’umma, da yake zai iya ilmantarwa a kan wani abu da  ba a sani ba, ko ya fito da muhimmancin wani abu don mutane su yi koyi don su amfana. Ko kuma ya fito da illar wani abu don mutane su guje masa. Saboda haka shi ma wannan bincike yana da nasa muhimmanci.

Wannan binciken ya shafi fannin nahawu ne musamman kan ginin jimla. Saboda haka zai zama a matsayin cike gurbi ne a kan abin da aka bari a baya wajen bayyana tsarin ginin jimlar d’aya daga harsunan Nijeriya da wasu suke ganin kamar babu shi a Nijeriya sai a k’asar Nijar, wato Zabarmanci . Wannan nazari zai taimaka wa d’alibai ta fuskar samun damar sanin irin tsarin nahawun harshen Zabarma, wadda yana d’aya daga cikin harsunan da suke mak’wabtaka da harshen Hausa.

Irin wannan  nazari zai wayar da kan mutane da yawa da suke da jahilci kan cewa harshen Zabarmanci yana d’aya daga cikin harsunan Arewacin Nijeriya, ganin cewa ba a kowane sashen k’asar Hausa ake iya samun al’ummar Zabarmawa ba. Ba abin mamaki ba ne a sami al’ummar Zabarmawa a wasu wurare da dama a wasu sassan na k’asar Hausa, amma rashin fito da irin gudummawar da suke bayar wa ga ha’baka rayuwar al’umma da bunk’asa tattalin arzik’in k’asa ya ‘boye su ballantana a san su. Gudanar da wannan binciken zai zama wata hanya ta fito da al’ummar Zabarmawa don a san cewa suna d’aya daga cikin al’ummar Arewacin Nijeriya ba a Nijar kad’ai suke ba. Kai har a jihar Sakkwato a kwai a a garin Bankanu. Kammala wannan bincike zai fito da al’ummar Zabarmawa a matsayinsu na ‘Yan Arewa ba ke’ba’b’bun mutane ba  ne, kamar yadda wasu suke d’aukar su. Wannan kundin zai taimakawa sauran d’alibai  suma, su mayar da hankali wurin bincike a kan irin wad’annan nazarce-nazarce da suka karanta musamman kan k’ananan harsunan da ake neman a mai da su saniyar ware har su mutu.

1.7 Nad’ewa


Bayan shimfid’a ga bak’o in ya tafi sai a nad’e. Don haka a nan za a nad’e wannan babin da tak’aitaccen bayanin abin da babin ya k’umsa. Abin lura a nan shi ne, duk  ayyukan da aka gudanar  wajen bitar aikin da suka gabaci wannan aikin, ba a sami wani aiki da ya yi dai da wannan aikin ba. Sannan aiki d’aya kacal aka gudanar kan harshen Zabarman wanda ya danganci k’irgau amma na lissafi kad’ai aka duba. Don haka wannan nazarin ya sami damar gudanuwa.

 

 

Post a Comment

0 Comments