Ticker

6/recent/ticker-posts

Harshen Wasa: Tsokaci Daga Shirin Labarin Wasanni Na Gidan Rediyon BBC (1)

NA

ALIYU MUSTAPHA

KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO 


TABBABTARWA

Na amince da cewa wannan kundi mai taken: “Harshen Wasa: Tsokaci Daga  Shirin Labarin Wasanni Na Gidan Rediyon BBC,” na Aliyu Mustapha mai lamba 1310106029 ya cika sharad’d’i da kuma k’a’idojin da aka shimfida domin samun digir na farko (B. A Hausa) A ssashen nazarin harsunan Nigeriya na Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

 
                                                                                                                           

Sa Hannun Mai Dubawa                                                  Kwanan Wata

Farfesa Salisu Ahmad Yakasai

 

 

                                                                                                                           

Sahannun Shugaban Sashe                                              Kwanan Wata

Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa

 

 

 

                                                                                                                           

Sahannun Mai Dubawa Na Waje                                     Kwanan Wata

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/nazarin-harshen-rubuce-rubucen-hausa-jikin-motoci/

 

 

 

 

 

SADAUKARWA

Na sadaukar da wannan aiki ga mahaifana da ‘yan uwana maza da mata da abokan arziki. Haka kuma ina sadaukantar da wannan aiki zuwa ga manazarta da d’alibai na Hausa a kowane fanni.

https://www.amsoshi.com/tuntubi-masu-gudanarwa/

 

GODIYA

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ubangiji mad’aukakin sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W) da Alayansa da Sahabbansa da duk wad’anda suka biyo su a kan tafarkin shiriya da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Bayan haka, ina mai farin cikin  godiyata musamman ga malamina da ya sadaukar da lokacinsa wajen duba wannan aiki wato, Farfesa Salisu Ahmad Yakasi. Ya kasance bangon sukari kowa ya jingina sai ya lasa, haske mai yaye duhu, ruwa a gulbi duk mai shigarsa ba biya, bak’i da haske mai kyau kamar zinariya. Ya baka ko ka gode yayi maka magiya, d’awisu sarki a ado shigarka ta biya, kura matsa can zaki gabanki kinjiya.ga sadauki kuma alkakin gani a lasa. Allah ya saka da masa da mafificin alherinsa Amin.

Sai godiya zuwa ga dukkan malamai na wannan sashe da suka koyar da ni darassa daban-daban a wannan mataki na digiri na d’aya. Allah ya biya su da mafificin sakamako Amin. Haka kuma ina godiya ga mahaifina Alhaji Muhammad Mustapha Alkali da Mahifiyata Hajiya Amina game da kulawar da suka bani har na kawo wannan mataki na rayuwa. Haka kuma ina mik’a godiyata ga malam Lawali Sifawa (SSCOE), da malam Nura (SSCOE) da Dr. Sabi’u Alhaji Garba (BBC) da malam Tukur Sifawa (SSCOE).

A karshe ina mik’a cikakkiyar godiya ga yayye na maza da mata da k’anne na da kuma abokai na kamar su sa’idu shu’aibu (System), Abdulazeez, Najibu Shatima, Mansur (Mansho), Mashakur (Slow), Mubarak Jekada (Mbk), Lukuman, Faruk Jabo da sauran wad’an da ban ambata ba, Allah ya saka maku da alherinsa Amin.
www.amsoshi.com

Post a Comment

2 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.