Ticker

6/recent/ticker-posts

Harshen Wasa: Tsokaci Daga Shirin Labarin Wasanni Na Gidan Rediyon BBC (2)

NA

ALIYU MUSTAPHA

BABI NA DAYA

GABATARWA

Shimfid’a


Kasancewar kowane irin mutum akwai irin abin da yake ba shi sha’awa a rayua, wanda yakan iya wayuar gari sha’awar ta yi tasiri a zuciyarsa ko kuma a kan abin da yake so ya sani. Irin wanan yanayi shi ke sa mutum damar yin bincike a kan sa. Wasa na da matuk’ar muhimmanci ga raywuar d’an Adam. Wasa na nufin yin wani abu kai kad’ai ko tare da wasu domin samun nishad’i. Mafi yawanci wasanni manufarsu ita ce yin nasara ta hnayar doke aboki ko abokan wasa, ko kuma cimma wani buri da ake bauk’ata. Yana daga cikin muhimmancin wasa nishad’antarwa, fad’akarwa da kuma ilmantarwa. Wannan ya sa kafafen yad’a labarai suke shirya shiraruwan wasanni iri daban-daban ta ‘bangarori daban-daban domin a nishad’antar, a fad’akar a kuma ilmantar a al’umma.

Kamar yadda muka sani cea gidajen rediyo na d’aya daga cikin muhimman hanyoyin sadarwa ko kuma yad’a labaria ta fuskar wayar da kan jama’a a hanyoyi daban-daban na raywua ta yau da kullum. Saboda wannan aikin bincike namu, zai yi tsokaci ne a kan abin da ya shafi “Shirin Labarin Wasanni” na gidan rediyon BBC Hausa.

Babi na d’aya zai yi bayani ne a kan gabatarwa. Ya k’unshi illahirin abin da aikin zai tattauna. Sai kuma dalilin gudanar da bincike, da farajiyar bincike, da muhimmancinsa da bitar ayyukan da suka gabata. Inda daga k’arshe za a ba da tak’aitaccen tarihin gidan rediyon BBC.

Ababi na biyu, za mu dubi alak’ar da ke tsakanin harshe da rukunin jama’a. inda za mu ga yadda tsarin rukunin jama’a yake,l da nau’o’in Hausa, da Hausa a kafafen yad’a labarai. Babi na uku kuma zai kawo bayanin manufar shirin labarin wasanni, da zubi da tsarinsa, da kuma yadda ake shiryawa da gabatar da shirin. Babi na hud’u, babi ne wanda za a yi nazarin Hausar shirin labarin wasanni.

Babi na biyar wanda shi ne babin k’arshe, yana k’unshe da jawaban tak’iaitawa, sakamakon bincike, shawarwari da kuma manazarta.

1.1 Dalilin Gudanar da Bincike


        Dalilin da ya haifar da wannan binciken shi ne; a lokacin gudanar da bitar ayyukand a magabata suka aiwatar ba a sami wani aiki da ya yi daidai da wannan nazarin ba, ko da kuwa ta fuskar taken binciken ne. wani dalilin kuma shi ne, yin wannan binciken zai taimaka ajen fayyace alak’ar da ke tsakain harshe da kuma rukunin jama’a, da ire-iren nau’o’in Hausa, da kuma irin girma, da maraba da matsayin da harshen Hausa yake da shi a kafafen yad’a labarai a cikin al’umma.

Daga k’arshe dalilin gudanar da wannan bincike zai taimaka wajen fad’akar da manazarta ko masu sha’awa a kan manufar shirin labarin wasanni na gidan rediyon BBC da zubi da tsarinsa, da kuma yadda ake shiryawa da gabatar da shi.

1.2 Muhimmancin Bincike


Wannan binciken ba zai rasa rawar da zai taka ba a gaban manazarta, watau ma’ana ba zai rasa kasancewa mai muhimmanci ba ga masu karatu ko nazarin abin da ya shafi harshe, musamman wad’anda suka shafi gudmmuwar shirye-shiryen da gidajen rediyo ke aiwatarwa ga al’umma. Wannan binciken, zai fito da amfanin da shirin ke da shi musamman na fad’akarwa, da raha, da nishad’antarwa da annushuwa da kuma ilmantarwa da masu sauraron shirin ke samu a tsakanin al’umma da kuma yadda ya yi tasiri ga rayuarsu.

1.3 Farfajiyar Bincike


        Muhallin wannan binciken mai taken “Tsokaci Daga Shirin Labarin Wasanni Na Gidan Rediyon BBC,” na tak’aita shi ne a iya sashen labaru na gidan rediyon BBC Hausa.

1.4 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata


        Hak’ik’a wasu masu bincike, ko nazari sun yi k’ok’ari wajen bayar da tasu gudummuwa a kan shirye-shiryen kafofin yad’a labari musamman na gidan rediyo. Dawannan na ga ya kamata in gabatar da bitar ayyukan da suka gabata musamman ma wad’anda ke da makusanciyar alak’a da dangantaka da shirin labarin wasanni na gidan rediyon BBC. Ga kuma kad’andaga cikin ha’b’basar da masana suka yi domin ha’baka harkar bincike:

Dogon Daji (2009) a kundin digirinsa na farko ya nuna fasaha da zalak’a a labarun nishad’i a cikin shirin “Dad’in Zuciya” inda ya nuna alfanun shirye-shiryen gidan rediyo wajen nishad’antar da masu sauraro.

Ahmad D’Aan mai Goro, a kundinsa na (Ph. D.) Harsen Hausa a kafofin yad’a Labarai: Gudunmuwa ga Cigaban K’asa. Ya nuna irin muhimmiyar rwar da harshen Hausa yake takwa a gidajen rediyo na cikin gida da ma k’asashen waje.

Nasiru Abubakar, Harshen Hausa a Kafafen Yad’a Labarai: Sharhi A Kan Tsaro da kuma Siyasa a Arewacin Nijeriya. Takardar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani na k’asa karo na farko a Jami’ar Usmanu d’an Fodiyo Sakwkato (2016). Ya bayyana amfanin shirye-shiryen Hausa na gidajen rediyo da jaridu, inda ya nuna irin tasirinsu wajen bunk’asa al’adu da tsaro da wayar da kai da ha’baka harkokin mulki da siyasa a la’ummar Arwacin Nijeriya.

Amfani A. H. (2014) “Ha’baka Hausa da Yayata Hausa a Duniyar Yau.” A wanan takarda an tattauna ne a kan hanyoyin da ake ha’baka Hausa da yayata ta, inda aka nuna hanyoyin a ake ha’baka ta sun k’umshi kakafen yad’a albarai, da kasuwanci da siyasa.

  1. A. Garba (2013) Shirye-shiryen Rediyo na Hausa: Tubalan Ginin Dimokarad’iya. Takardar da aka gabatar a taron k’arawa juna sani na farko a kan Harshe da adabi da al’adun Hausawa a cibiyar nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano. Ya bayyana cewa, harshen Hausa na d’aya daga cikin ahrsunan Afirka da aka fara watsa shirye-shirye a gidajen rediyo na k’asarshen waje.


S.A. Yakasai (2012) Jagoran Ilimin Walwalar Harshe. Ya yi bayani a kan harshe, tsarin rukunin jama’a da kuma nau’o’in Hausa.

Yakasai, S. A. (2005) Aro ko K’irk’ira: Nazarin samuwar sabbin kalmomin Hausa a jami’a da kuma Garin Sakkwato, Departmental Seminar, NLD, UDUS. Ya yi bayani a kan yanayi da tsarin aro a harshe, da kuma k’irk’ira da dalilan da suke haddasa bunk’asar k’irk’irarrun kalmomi.

Yakasai, S. A. (2015) “How well does google translate? Hausa an English in focus” wannan takarda ta mai da hankali ne a kan buk’atar da ke akwai wajen inganta yadda kafar yad’a labarai ta kamfanin Google ke fassara wasu bayanai daga Ingilishi zuwa Hausa.

https://www.amsoshi.com/2018/01/12/aladun-mutuwar-maguzawan-kambari-na-birnin-yawuri-5/

1.5 Tak’aitaccen Tarihin Gidan Rediyon BBC


Gidan rediyon BBC ya fara watsa labru cikin ahrshen Hausa a ranar sha uku (13) ga watan Maris a shekarar (1057), a babban birnin London. Inda daga baya gidajen rediyon Jamus da muryar Amurka, da Faransa (FRI) jamhuriyar Masar, jamhuriyar musulnci ta Iran, Libya da Ghana suka biyo baya.

An kafa sashin BBC na Emprie Ser’bice a watan Disamba (1932), ta hanyar gajeren zango wanda ke bayar da damar watsa bayanai zuwa dogon zango. Duk da cewa darakta janar na BBC John Reith ya yi hasashen cewa shirye-shiryen ba za su k’ayatar ba, shirin da aka watsa daga d’akin watsa labarai na broadcasting house ya samu kyakkyawan yabo. Jawabin sarki kwanaki shida bayan bud’e tashar, sai sarki King George ya yi jawabi kai tsaye daga Sandringham. Marubucin nan Rudyardkiphing ne ya rubuta jawabin. An saurari jawabin sarkin a sassa daban-daban na duniya. Darakta janar na BBC ya bayyan hawabin da cewa wata babbar nasara ce ga BBC.

Yak’in duniya na biyu ya haifar da sauyawa tashar suna  inda ta koma tashar k’asashen waje: (o’beeseas Ser’bice) a watan Nuwamba, 1939 tare da bud’e sabbin tashohi na harshen Larabci da Spanning ga Latin Amaurka, Jamusanci, Italiyanci, Afrika, Spaniyanci ga Turai da kuma Portugal. A k’arshen 1949 BBC na watsa shirye-shiryenta a harsuna talatin da hud’u (34). Rasshin isasshen wuri ga sauran harsunan k’asashen waje a broadcasting house da fashewar wata nakiya ta Jamus a wajen ginin a 1940, ta haifar da gobara wacce ta lalata ginin sosai. Harsunan da ke watsa shirye-shirye zuwa k’asashen Turai sun koma Bush House a tsakiyar birnin London inda ake biyan fan talatin (30) a kowanne mako a matsayin kud’in haya. Tarihi ya nuna cewa BBC ta watsa shirye-shirye a cikin harsuna sittin da takwas (68). Yawanci wad’annan ahrsunan na zuwa ne su tafi ciki har da Maltesa, Gujarati da dai sauransu. Fad’uwar bangon Berlin ta sa an rufe harsunan Turai da dama domin mayar da hankali kan yankunan da suka fi muhimmanci wasu rage-ragen da aka kuma yi sun sa adadin harsuna a yanzu ya zamo ashirin da takwas (28) yawancinsu suna watsa shirin ne ta hanyar internet kawai.

Bayan rugujewar tarayyar Sobiyet farkon shekarar 1990, sai wani sabon zaman d’ar-d’ar ya ‘barke a yankin Gulf, a ranar biyu ga watan Ogusta (1990, dakarun Irak’i k’ark’ashin jagorancin Saddam Hussain suka mamaye Kuwait. Loakacin da dakarun had’in guiwa suka fara kai hari kan Irak’i a watan Junairun 1991, sai BBC ta sauya akalar shirinta ta koma kawo rahotanni da sharhi kai tsaye a karon farko. Bayan aiki na wani d’an lokaci a 1990, gidan talabijin d’in Larabci na BBC ya sake fara aiki a watan Maris na shekarar 2008, sannan gidan talabijin na sashin Pariss ya bi bayansa a 2009. An fara watsa shirin talabijin zuwa k’asashen duniya a Turanci a 1991 da world Ser’bice T’B wacce a yanzu ake kira BBC World News.

A shekara ta 2012 BBC za ta sake komawa Broad Casting Hourse bayan shekaru saba’in da d’aya (71), zuwa wani d’akin watsa Labarai na a zo a gani. Ma’aikatan world ser’bice za su had’u da rauran takwarorinsu na BBC, da masu aiki kan shafukan intanet da kuma talabijin domin samar da ingantattun labaran duniya.

1.6 Nad’ewa


A wannan babi ya nuna irin gudummuwar da magabata suka bayar ta hanayr bitar ayyukan da suka gabata, da kuma bayar da dalilin gidan wanan bincike. Musamman ta la’akari da gudunmuwarsa a fagen ilimi. Sai matakan da za mu bi wajen gudanar da wannan bincike, da kuma manufar da ake son a cimma a k’arshen wanann bincike da farfajiyarsa.

www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.