Ticker

6/recent/ticker-posts

Al’adun Mutuwar Maguzawan Kambari Na Birnin Yawuri (5)

KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO
NA

MUSA LUKMAN ALKASIM

BABI NA BIYAR

5.0 Kammalawa


        Ba shakka duk binciken da aka gudanar a kan wani al’amari, ana sa ran a gano wasu abubuwa masu muhimmanci wad’anda ba a san su ba kafin aiwatar da bincike.  Wad’annan abubuwa da aka gano su ake kira sakamakon bincike. Wannan binciken ya yi k’ok’arin tattauna yadda Maguzawan Kambari na Birnn Yawuri ke aiwatar da al’adun mutuwarsu. A kan haka ne, wannan binciken ya yi k’ok’arin bayyana yadda Maguzawan Kambari suke gudanar da al’adun mutuwarsu. Da farko binciken ya kawo yadda Maguzawan Kambari ke gudanar da jinyan mara lafiya.

Bayan wannan an kawo yadda suke isar da sak’o ga junansu a kan an yi mutuwa. Bayan wanann kuma, binciken ya kawo yadda suke kimtsa gawa, tare da muhallin da suke binne gawa. Bayan haka kuma, binciken ya fito da yadda Maguzawan Kambari ke binne gawa, tare da bayyana yadda suke zaman makaoki. Haka kuma an yi k’ok’arin kawo lafuzzan amsar gaisuwar mutuwa tare da yadda suke raba gado.

Haka kuma binciken ya yi k’ok’arin zak’ulo yadda matan mamaci ke gudanar da takaba, tare da bukukkuwan da suke yi bayan shekara uku da mutuwa.

www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.