Ticker

6/recent/ticker-posts

Sana’ar Noma A Ma’aunin Karin Magana

Takardar da aka gabatar a taron kara wa juna sani na kasa da kasa na farko mai take The Hausa People, Language and History: Past, Present and Future da Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Jihar Kaduna ta shirya daga ranar 22-25 ga watan Maris, 2015

NA

MUSA SHEHU
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
07031319454
msyauri@yahoo.com

1.0   Gabatarwa


Tun ran gini ran zane, al’ummar Hausawa tun can asali al’umma ce da ta dogara da kanta wajen samar da hanyoyin tattalin arzikinta. Ba a san Hausawa da ragganci ko kasala ba, domin tun asalatan suka tashi tsaye tsayin daka wajen  yin sana’o’i iri daban-daban don wadatar da kansu daga buk’atun rayuwar yau da kullum. Ta haka ne har ya zama a kowane gidan Bahaushe yana da sana’o’in da yake aiwatarwa. Buk’atar d’an Adam ta son abinci da sutura da muhalli ne ta haifar da sana’o’i irin su noma da  kasuwanci da su da fawa da k’ira da jima da sauransu. Sana’a ita ce ginshik’in rayuwa da tattalin arzikin Hausawa. Tana kuma d’aya daga cikin manyan hanyoyin gane martabar mutum da k’asaitarsa a cikin al’umma. Da yake al’adun Hausawa suna tafiya ne kafad’a da kafad’a da adabinsu, wannan ya sa kowane ‘bangare na rayuwar Hausawa ka d’auka, sana’a ce ko aure ko kasuwanci ko zamantakewa tsakanin al’umma da makamantansu, kana iske shi k’unshe da karin magana. Karin magana ya kasance wani babban rukuni a cikin adabin baka, haka ma gudummuwar da yake bayarwa a fagen bayyana al’adun Hausawa ya fi gaban a bayyana.

          Manufar wannan bincike shi ne yin tsokaci a kan d’aya daga cikin muhimman sana’o’in Hausawa na gargajiya wato sana’ar noma, da kuma gano matsayinta a cikin karin maganganun Hausawa na yau da kullum. Nazarin zai duba yadda karin magana ya taskace al’adun da suka shafi sana’ar noma, kama daga bayani a kan amfanin sana’ar, da matsalolin sana’ar, da kayan aikin gudanar da sana’ar, da aikace-aikacen gudanar da sana’ar, da ire-iren abincin da  ake nomawa, da makamantansu. Saboda haka, nazarin zai zak’ulo ire-iren wad’annan karin maganganu da suka ji’binci sana’ar noma, tare da yi sharhi a kan al’adu da falsafar da ke jibge a cikin su dangane da rayuwar Hausawa.

2.0   Karin Magana da Muhimmancinsa


Umar (1980) ya bayyana karin magana da cewa, “wata ‘yar gajeruwar jimla ce mai qunshe da hikima da voyayyar ma’ana idan za a tsaya a fassara”. Furniss (1996) ya kira karin magana da cewa, “ wata gajeruwar jimla ce da ake fad’a ta qunshi ma’anoni waxanda ba kasafai kalmomin da ke cikinta ke nuna su ba”. Yahaya (1992) cewa ya yi, karin magana tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaqa tare da bayar da ma’ana gamsasshiya, mai faxi, mai yalwa, musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki. Xanyaya (2007) cewa ya yi, “ karin magana zance ne mai faxakarwa kan zaman duniya”. Ya qara da cewa, kasancewar karin magana kirari, ba’a, habaici ko baqar magana, bai hana a ce yana faxakarwa matsawar an nazarce shi da kyau.

Bayyana amfanin karin magana abu ne mai faxin gaske, sai dai kawai mutum ya tofa albarkacin bakinsa. Babu wata al’umma wadda ba a samun karin magana a cikinta. Wannan yana faruwa ne saboda tsananin muhimmancinsa ga kyautata rayuwar al’umma. Ya isa ya zama hujjar cewa, karin magana yakan koyar da ilimin zaman duniya ne, ta inda za a san makomar kowane lamari. Wannan ne ma ya sa babu wani mutum baligi face yana da karin magana mai yawa a tare da shi wanda kan qara masa haske a kowane irin sha’ani ya sami kansa. (Xanyaya 2007). Malamai sukan kawo karin magana a zantukansu. Haka ma jahilai sukan kawo a nasu. Babu wani abu da ake nema game da adabin Bahaushe face akwai shi a karin magana. Babu wata al’ada da ake son a nazarta face akwai ta a karin magana. Manazarta harshe kuwa suna da abin da za su kama mai yawa a karin magana idan sun kula. Mu duba yadda shahararren marubucin nan Abubakar Imam ya riqi karin magana wata fitila a rubuce-rubucensa. Da karin magana ya tsara mafi yawan littafansa. Kai ! Duk da sunayen littafansa ma mafi yawa karin magana ne, kamar Magana Jari Ce, Tafiya Mabuxin Ilimi da sauransu. Karin magana yakan qara wa zance daxi da armashi, sannan ya nuna zalaqa da iya zurfin tunani da balaga da qwarewar mai zance. Karin magana ya danganci abubuwa da yawa tamkar al’adu da tarihi da fasaha da hikimomin Hausawa. Kusan karin magana komi da ruwanka ne. Yakan yi katsalandan a duk cikin ‘bangarorin rayuwa. Yakan ayyana falsafar Hausawa dangane da wasu abubuwa da suka shafi rayuwa kamar arziki da alheri da ilimi. Yana taimakawa qwarai wajen kyautata tarbiyya ta yadda za a gina halaye nagari. Karin magana yakan daidaita xabi’un mutane, ya kuma kyautata zumunta da makamantansu da dama. Bari mu dubi misalan wasu karin maganganun waxanda ke bayyana amfanonin da aka bayyana a baya :

  •   Mai arziki ko a kwara ya sai da ruwa

  • Alheri dank’o ne ba ya fad’uwa k’asa banza

  •   Ilimi gishirin zaman duniya

  • Zumunta a k’afa take

  • Zafin nema ba ya kawo samu

  •   Hassada ga mai rabo taki


A waxannan misalai za a ga cewa, dukkansu suna bayyana wasu halayya na rayuwa, kamar samun arziki da amfanin zumunci da ilimi da alheri da sauransu.

3.0   Gurbin Sana’ar Noma a Ma’aunin Karin Magana


Na duk’e tsohon ciniki, kowa ya zaka duniya kai ya taras. Na duk’e maikamar an huta. Wannan kirari ne da Hausawa ke yi wa noma. Kuma suna ce wa manomi “ bawan damina Baturen rani” saboda kud’in da yake samu idan kaka ta yi, kuma ga amfanin gonarsa wanda zai rik’a ci har zuwa wata shekara. Ana kuma yi wa noma kirari da “noma yanke talauci” don kuwa duk wanda ya rik’i noma rik’o na gaske ba shakka ba zai yi talauci ba. Noma dai shi ne tonon k’asa a fitar da amfaninta ta hanyar zafe ta , da zankad’e ta, da yin shuke-shuke a bayanta. Ta nan ne ake samun tsirrai iri-iri na ci da na tsotsa da na yin tufafi.(Alhassan da wasu 1982). Tun shekaru aru-aru da suka wuce, an san k’asashen Hausa da yin noma. Da Turawa suka zo k’asashen Hausa, sai suka k’ara k’arfafa sana’ar noma suka kawo kayan aiki na zamani wanda zai taimaka wajen bunk’asa noma cikin sauk’i. K’asar Hausa tana cikin k’asashen da suka dogara da noma na damina da kuma na rani. Sukan yi noman damina ne a lokacin da ruwan sama ya sauka, inda suke noma abubuwa da dama da suka had’a da shinkafa da dawa da masara da wake da gero da gyad’a da sauransu. Da rani kuma sukan yi amfani da ruwan gulbi ko na rijiya ko na tafki su noma abubuwa daban-daban da suka had’a da albasa da tumatir da tarugu da tattasai da tankwa da karas da alayyaho da sauransu. Hausawa suna da kayan aikin noma da yawa. Wad’anda aka fi sani su ne sungumi da fartanya da galma da lauje da kwasa da sauransu. Shugaban wannan sana’a ta noma ana kiransa Sarkin Noma. Wannan shugaba shi ke kula da dukkanin al’amurran da suka ji’binci sana’ar noma. Kasancewar noma dad’ad’d’en sana’a ga Hausawa ya haifar da samuwar karin maganganu masu tarin yawa wad’anda ke bayyana yadda al’amurran sana’ar ke gudana. Ga dai yadda al’amarin yake:

3.1  Amfanin Sana’ar Noma

          Amfanin sana’ar noma abu ne da ya fi k’arfin a bayyana, sai dai a yi addu’a a shafa fatiha. Wannan ne ya sa a zamanin da ya shed’e sana’ar noma a k’asar Hausa kusan sana’a ce ta kowa da kowa. Har ma zuwa yau, sana’ar tana taka muhimmiyar rawa wajen bunk’asa tattalin arzikin Hausawa da ci gaban rayuwarsu. Wannan ya sa za ka taras kusan kowane rukuni na al’ummar Hausawa ba a bar su a baya ba wajen gudanar da sana’ar, kama daga masu arziki da ma’aikata, balle ma talakawa. Wannan ya faru ne kasancewar irin ci gaban da zamani ya kawo na samar da hanyoyin sauk’ak’a gudanar da sana’ar ba kamar inda aka fito ba. Ganin irin muhimmancin wannan sana’a ya sa Hausawa sukan yawaita ambaton al’amurran da suka ji’binci sana’ar a karin maganganunsu na yau da kullum, ko dai domin nuna muhimmancin sana’ar a gare su, ko domin bayyana wani munimmin abu da ya kamata al’umma ta kula da shi, ko kuma domin yin gargad’i da fad’akarwa ko hannunka mai sanda. Ta haka Hausawa suka samar da karin maganganu daban-daban da ke k’unshe da bayanin amfanin sana’ar noma. Ga dai misalan ire-iren wad’annan karin maganganu kamar haka:

Noma Yanke Taluci: Irin muhimmancin da Hausawa suka ba noma, da kuma samun biyan buk’atocinsu na rayuwa daga gare shi, ya sa suke kallon sana’ar a matsayin hanyar ban kwana da talauci. Ko shakka babu, dukkan wanda ya rik’i noma rik’o na gaskiya, ko bai yi arziki mai yawa ba zai samu wadatar zuci, wato ba zai rasa abin da ya share wa kansa hawaye ba.

Ribar Noma, Sai Mai Hak’uri: Hak’ik’a noma sana’a ce mai matuk’ar riba da ba da amfani matuk’ar dai an yi hak’uri na wani lokaci, saboda ba sana’a ce da za a samu amfaninsa nan take ba. Saboda haka, idan manomi ya yi hak’uri zai wayi gari yana mai farin ciki ya manta da duk wata wahala da ya sha a baya, wato lokacin kaka ke nan. Saboda d’imbin ribarsa ne ma kowa bai yarda an bar shi baya ba, masu arziki da talakawa, har ma da ma’aikatan zamani.

Babbar Gona Maganin Awon Bad’i: Mai k’aramin gona ma ba kasafai yake yin awo ba sai dai idan damina ba ta yi kyau ba, bale mai babba. Da ma duk wanda ya bud’e babbar gona, ba shakka sun yi hannun riga da awo, sai dai ya aunar da saura domin bai iya canye amfanin da ya noma gaba d’aya.

Da Awo Kusa, Gara Noma Nesa: Sanin amfanin noma ya sa Bahaushe ke ganin komai wahalar noma gara yin sa da dogara da yin awo, domin kuwa idan mutum ya yi noma ko bai da ko anini ba zai rasa abinci ba. Dogara ga awo kuwa abu ne da babu tabbas saboda ba lallai ne wata rana a samu abin da za a yi awon ba.

3.2  Ire-iren Abubuwan da Hausawa ke Nomawa

K’asar Hausa k’asa ce da Allah ya albarkata da k’asar noma mai dausayi da taki managarci, wanda hakan ya ba al’ummar k’asar damar amfana da baiwar da Allaha ya ni’imta su wajen noma abubuwa iri daban-daban domin biyan buk’atun rayuwarsu. Sakamakon matsayi da muhimmancin da wad’annan abubuwa da suke nomawa suke da shi a wajensu ya sa suke yawan amfani da sunayen wasu daga cikinsu wajen karya maganganunsu na yau da kullum. Ga dai misalan wasu karin maganganun:

Alkamar Bisa Dutse, Allah Kan Ba Ka Ruwa: Daga cikin abubuwan da Hausawa suke nomawa a k’asar Hausa akwai abin da ake kira alkama wanda suke sarrafawa zuwa nau’ukan abinci daban-daban, kuma suke sayar da shi ga mak’wabta na kusa da na nesa da su.

Idan Ana Ba Albasa Ruwa, A Zan Tuna Gauta: Wannan karin magana yana d’auke da abubuwa biyu da Hausawa ke nomawa, wato albasa da gauta. Albasa yana daga cikin manyan abubuwan da Hausawa ke nomawa musamman a wuraren da ke da fadamu da k’aramu da koguna wanda za a iya amfani da su wajen ban ruwa. Haka shi ma gauta ana noma shi a wasu sassa na k’asar Hausa.

Gonar Baba, Da Ita Da Biri Sai Kallo: Duk da yake baba ba abinci ba ne, amma kuma Hausawa na noma shi musamman a lokutan baya. Baba dai wani ganye ne da Hausawa ke nomawa wanda suke amfani da shi wajen rina tufafinsu.

Bana Wake Ya Yi ‘Yaya, Damo Ya Makance: Wannan karin magana ne na dake bayyana d’aya daga cikin abincin Hausawa ke noma a kusan kowane sashe na k’asar Hausa, wato wake. Idan damina ta yi kyau kuma ba a samu wani tarnak’i na k’wari ko fari ba, yakan zuba ‘ya’ya mai yawa gwanin ban sha’awa.

Sauran ire-iren wad’annan karin maganganu sun had’a da;

  • Daga fake ruwa, sai shuka kabewa

  • A dad’in masha kara, dawa ta k’i ‘ya’ya

  • Ba a rarrabewa da d’aurin cikin rama, sai ta yi ganye

  • Allah ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba ya yi birgima

  • Kyautar tumu ba ta hana rumbu cika


3.3  Kayayyakin Sana’ar Noma da Muhallin Amfaninsu

          Sana’ar noma kamar sauran sana’o’i take, wato akwai kayayyakin da tilas sai an tanade su domin gudanar da sana’ar. Haka ma kowane d’aya daga cikin kayayyakin akwai ke’ba’b’ben muhallin da ake amfani daban da waninsa. Akwai karin maganganu masu tarin yawa da Hausawa suka samar wad’anda ke bayyana ire-iren wad’annan kayayyaki da muhallin amfaninsu. Ga misalai kamar haka:

Sungumi A So Ka Ranar Shuka : Sungumi wani kayan aiki ne daga cikin kayan aikin gona. Ana amfani da shi ne wajen shuka kawai. Sungumi ba kamar fartanya ko kwasa yake ba, waxanda aikinsu bai qarewa sai ranar da aka kai amfani gida. Shi sungumi da zarar an kammala shuka aikinsa ya qare sai kuma baxi, domin babu wani aiki da za a iya yi da shi wanda ya taka kara ya karya. Don haka, da zarar ruwan sama ya sauka aka xauki aniyar zuwa shuka, to dole ne a nemi sungumi. Wannan karin magana yana qara bayyana muna cewa, kowane irin abu da ranarsa kuma da lokacin amfaninsa zai zo matuqar akwai rayuwa.

 Ba a Qwace Wa Yaro Galma : Galma dai wani nau’in kayan aikin gona ne wanda ake amfani da shi wajen yin huxa kafin a yi shuka. Da yake aikin noma aiki ne mai wahalar gaske, manya ma da suka saba juriya ce kawai suke yi ba don daxinsa ba. Kusan duk wata sana’ar Bahaushe babu sana’a mai wahala kamar noma, tun daga saukan ruwan sama har zuwa xaukewarsa manomi bai da hutawa sai idan ya kawo amfani noma gida. Galma ba ta da wani aiki baya ga huxa, da zarar an yi huxa an qare, aikinta ya qare sai kuma baxi in rai ya kai mu. Sani Aliyu Xandawo ya ambaci wannan kayan aiki a waqarsa da ya yi wa sana’ar noma, yana cewa:

  1. wak’a: A mai da hankali wajjen noma


Mutane a kama sana’o’i

 

Jagora  :   Sha hura ka d’au galma malam

Ka kama hud’a hili has sahe

 

Amshi  :   Ka noma auduga tai ma haske

Mutane a kama sana’o’i

Allah Ya Tsari Gatari Da Noma, Sai Dai Fartanya : Gatari ba ya daga cikin kayan da manoma ke amfani da su wajen noma. Hawuya ko kwasa ko fartanya su ake amfani da su wajen noma ba gatari ba. Shi gatari ana amfani da shi ne kawai wajen da za a yi sare-saren itace ko ‘yan qirare da suka fito a cikin gona musamman idan sabon wuri ne. Don haka, wannan karin magana na nuna muna cewa, kowane irin kayan aikin gona da wurin da yake amfani domin tsare lafiyar shuka, domin babu abin da gatari zai iya yi wajen noma face sassare shuka wanda ba shi ne muradi ba. Don haka,  yadda hauya ba za ta yi aiki wurin gatari, haka gatari ba zai yi aiki wurin hauya ba.

Galma Uwar Rufi, Fartanya Sai Shirbe : Galma wani kayan aiki ne daga cikin kayan aikin gona. Ana kiranta uwar rufi ne saboda aikinta shi ne huxa wanda ake kamfato qasa sai a rufe haki da shi ta yadda idan shuka ya tsiro zai ji daxin girma, haka ma haki zai xauki lokaci bai sake fitowa ba. Baya ga huxa, galma ba ta da sauran wani aiki a cikin gona. Fartanya kuwa ba ruwanta da aikin rufi ko huxa, aikinta shi ne shirbe, wato nome hakin da ke fitowa a cikin shukar da aka yi. A wannan karin magana, Hausawa na son bayyana cewa, kowane kayan aikin gona da irin aikin da yake yi a gona daban da wanda ba shi ba, wato kowane yana cin gashin kansa ne.

Abin Nema Ya Samu, An Jefi ‘Yar Manomi Da Fartanya : Taqamar mutum bai wuce kayan amfaninsa ba. Don haka, alfaharin manomi kayan aikin gonarsa. A koyaushe kayan aikin gona abin nema da kulawa da tanadi ne ga manomi domin inganta sana’arsa. Wannan karin magana yana nuni ne da cewa, fartanya na daga cikin kayan aikin da manoma suke taqama da ita  koyaushe, wanda ya zama tilas a tanade ta matuqar ana buqatar gudanar da sana’ar kamar yadda ya kamata.

 

 

Sauran karin maganganu masu alak’a da wannan rukuni sun k’unshi:

  • Kada allura ta tono galma

  • Da walakin, lauje cikin nad’i

  • Duk abin da lauje ya d’ebo ciyawa ne

  • Lauje mai wuyar nad’i

  • Katarin wa ce? An ba karuwa kalme


3.4  Aikace-Aikacen Sana’ar Noma  

Bayan manomi ya tanadi dukkan kayan aikin da ya kamata a tanada kafin fara gudanar da sana’ar, akwai aikace-aikace da yawa da ake gudanarwa kafin a kai ga samun amfanin gona tun daga saukan ruwan sama har zuwa d’aukewarsa. Wad’annan aikace-aikace sun had’a da sassabe da shuka da dashe da noma da girbi da makamantansu. A wannan rukuni ma akwai karin maganganu da suke bayyana ire-iren wad’annan aikace-aikace, ga masalai kamar haka:

Sassabe Mafarin Noma : Sassabe wani aiki ne da manomi ke fara yi a gonarsa gabanin saukan ruwan sama a yi shuka. Sassabe aiki ne na gyaran gona da suka had’a da sassare ‘yan itatuwa ko ganyaye ko wani abu da ba a buk’ata a cikin gona. A al’adar manoma, idan aka ga mutum ya fara sassaben gona, alamu ne na shirin noma wannan gona a wannan shekara, domin shi ne aiki na farko da manoma ke fara yi idan damina ta kunno kai.

Shinge Kariyar Gona, Kowa Ya Yi Ka Ya Huta Da Ratse : Shinge wani kariya ne da ake yi wa gona da ‘yan itatuwa da k’irare kamar dai danni, musamman ga gonar da dabbobi ke yawaita ‘barna ko mutane suke yawan ratse a cikinta. Sai dai galibi an fi yin sa ga d’an k’aramin gona da bai da fad’i da tsawo sosai. Ba shakka duk wanda ya yi shinge a gonarsa ya kauce wa ‘barnan dabbobi da ratsawar mutane a cikinta.

Kar Ka Wuce Gona Da Iri : Iri wani hatsi ne da manoma ke warewa su aje domin shukawa idan damina ta sauka. Idan ruwan sama ya sauka, manoma kan d’auki irin da suka tanada na nau’in abin da suke buk’atar shukawa zuwa gona domin shukawa. Saboda haka, duk yadda abinci ya k’aranta a gida, ba a d’aukar irin da aka tanada domin shuka a yi abinci da shi.

Abin Da Mutum Ya Shuka, Shi Zai Girba : Wannan karin magana yana bayani ne a kan ayyukan gona guda biyu, wato shuka da kuma girbi.A d’aya ‘bangaren kuwa, haka yake cewa duk abin da ka shuka shi za ka girba. Idan ka shuka masara ko shakka babu masara za ka girba. Haka nan abin yake faruwa a rayuwar d’an Adam ta yau da kullum. Idan ka k’ulla alhairi za ka ga alhairi, idan kuma ka k’ulla sharri za ka ga abinka. Wannan ya yi daidai da ayar Alk’ur’ani da ke cewa, idan ka aikata alhairi komai k’ank’antarsa za ka ga abinka. Idan kuma ka aikata sharri komai k’ank’antarsa, shi ma za ka ga abinka.

Sauri Ya kawo Wane Me Ka Shuka : Wannan karin magana ma yana bayyana muna d’aya daga cikin ayyukan gona, wato shuka wanda shi ake fara yi idan damina ta sauka, kuma galibin shuka bai wuce kwana hud’u ya tsiro.

3.5  Matsalolin Sana’ar Noma

          Kowace sana’a tana da irin nata matsalolin da masu yin ta sukan fuskanta a lokacin gudanar da ita. Sana’ar noma duk da irin alfanun da ake samu gare shi, akan fuskanci wasu matsaloli yayin gudanar da shi. Ire-iren wad’annan matsaloli sun had’a da fari, wato katsewan ruwan sama, da ‘barnan dabbobi da tsuntsaye da makamantansu. A kan haka ne Hausawa suka samar da karin maganganu masu bayanin matsalolin domin samun maslaha a kansu. Ga wasu daga cikin irin wad’annan karin maganganu kamar haka:

An Yi Shuka A Idon Mak’warwa : Akwai dabbobi da tsuntsaye da dama wad’anda ke wahalar da manoma idan sun yi shuka. Mak’warwa na daga cikin tsuntsayen da ke ci wa manoma tuwo a k’warya idan sun shuka irinsu. Idan mak’warwa ta fahimci inda manomi ya shuka irinsa, kafin ya tsiro sai ta rik’a zuwa tana tonewa tana cinye tsabar. Don haka duk manomin da ya yi rashin sa’a ya yi shuka a idon mak’warwa, lallai ne ya sake shuka wani irin. Haka yake a rayuwa kamar mutum ya voye sirrinsa a idon mak’iyinsa.

K’arya Manoma Ke Yi, Maganin Ciyawa Rani : Manoma sukan yi iya k’ok’arinsu domin raba shukarsu da haki domin ya samu walwalar girma kamar yadda ya kamata. Wannan ne ya sa sukan yi noman farko da na biyu, a wani lokaci har noma na uku akan yi. Wani lokacin ma akan gaji a cire amfanin gonar a cikin haki. Wannan ya nuna duk k’ok’arin da manoma ke yi domin kashe haki baki d’aya a gonarsu ba zai yiyu ba, sai dai su yi iya k’ok’arinsu su rage masa karfi, amma idan rani ya kama za ka iske haki na laushi har ya kai ga fara bushewa. Idan rani ya yi rani kuwa, za ka iske hakin ya bushe baki d’aya kamar dai wuta aka sa masa. Daga k’arshe ma sai a nemi haki a rasa domin rani ya gama da shi sai kuma wata damanar. Mamman Yaro Hore a wak’arsa da ya yi wa ‘Dangarba Gungaman noma, ya nuna irin k’ok’arin da manoma ke yi wajen kashe haki. Ga irin yabon da Yaro Hore yake yi wa Gungaman noma:

Jagora :  Na gode wa ajalin haki jikan Sani

Dogo ‘yan mazan kada burburwar gona

Allobar haki maganin gutsun gamba

Bayan shuka ya tsiro kuma an yi masa noma ya fara girma, manoma kan ci karo da matsalar fari, wato katsewan ruwan sama bayan an yi shuka. A irin wannan yanayi na fari da manoma kan fuskanta, akan samu karin maganganu da ke nuni da wannan matsala :

Mahassada Suna Zaton Fari, Allah Ya Sauko Ruwa : Fari na daga cikin k’alu balen da manoma kan fuskanta bayan sun shuka iri a k’asa. Wata al’ada ce da manoma suka saba da ita a kusan kowane shekara bayan saukan ruwan sama, wato wani yanayi ne na dakatawar ruwan sama na d’an lokaci bayan manoma sun yi shuka. Fari yakan taka wa manoma hanzari ainun, domin wani lokaci idan ya tsawaita amfanin gona yakan bushe ta yadda sai an sake shuka wani, wanda hakan yakan sa sai an kai ga yin rok’on  ruwa. A wani lokaci idan ya tsawaita sosai shi kan haifar da yunwa a gari ko k’asa.

Yabanya Allah Fisshe Ki Fari : Idan aka ce yabanya ana nufin wani mataki da shuka ya cimma na girma da samun walwala musamman idan ya samu isasshen ruwan sama kuma iska na buga mai kamar yadda ya kamata. A irin wannan lokaci ne idan aka yi rashin sa’a sai fari ya gitta, wato sai ruwan sama ya dakata, ka ce dai ba cikin damana ake ba. Wannan ne ya sa a koyaushe damina ta sauka, manoma sukan yi fatar d’orewar ruwan sama kada a sami fari. Dalilin yi wa yabanya wannan rok’o shi ne, idan yabanya ta yi kyau ta sami walwala ana kyautata zaton samun albarkar noma mai yawa, idan kuwa aka sami akasin haka, abincin da za a samu a wannan shekara ba zai wadata ba. A falsafance, wannan karin magana tamkar addu’a ne na kariya ga mahassada ko wani tarnak’i da ka iya dak’ushe ci gaban d’an Adam.

Mai Gona Shi Ka Koran Biri : Daga cikin matsalolin da manoma kan yi fama da su akwai ‘barnar biri. Galibi idan manomi na fuskantar irin wannan barazana, yakan koma gona da zama tun safe har zuwa yamma, wani lokaci ma yakan kwana a gonar domin fake lafiyar amfanin gonarsa daga hare-haren irin wad’annan dabbobi. Ga wani d’an wak’a da Narambad’a ya yi wa Sarkin Gobir na Isa inda yake yi wa wasu zambo da bayyana halayyarsu  na ‘barna kamar biri:

Jagora      : Kai tashi Biri tsohon ma’bannaci

Karen ‘biki bai d’au shawarakka ba

Gonar K’ofa Ga Hatsi Ga ‘Barna : Gonar k’ofa gona ce da ke iyaka da gari ba sai an shiga daji ba. Akan samu albarkar gona sosai a irin wannan gona saboda takin da ake yawan kai a wurin kasancewarsa kusa da gari da kuma yawaitar kashi da jama’a ke yi. Sai dai kuma ba a nan gizo ke sak’a ba, domin mai irin wannan gona yakan sha fama da ‘barnar dabbobin makiyaya da ma na mutanen gari. Don haka, dole mai irin wannan gona ya kula sosai matuk’ar yana son cin gajiyar gonarsa. Shi ya sa a wani karin maganar ake cewa, “gonar k’ofa mai wuya mai dad’i”.

Jawabin Kammalawa


Nazari ko bincike wani al’amari ne mai muhimmancin gaske a rayuwar d’an Aadam, domin shi ke haifar da fahimtar abubuwa da dama wad’anda ba a fahimci amfaninsu ba, ko kuma an fahimce su amma an manta da su a kwandon shara. Akwai abubuwa da dama da manazarta za su iya lalabowa dangane da rayuwar Hausawa a cikin karin maganganunsu, kama daga matakan rayuwarsu da suka shafi rayuwar aure, haihuwa, da kuma mutuwa. Haka ma za a iya lalabo bayanin sarautun gargajiya da bukukuwa da zamantakewa a cikin karin magana. Saboda haka, za a iya amincewa da ni idan na ce, karin magana ya kasance tamkar wani taska na adanar illahirin harkokin rayuwar Hausawa tun daga haihuwa har zuwa mutuwa, musamman idan aka yi la’akari da yadda ya taskace al’adun gudanar da sana’ar noma tun daga farkota har zuwa k’arshe.

 

                      

 

 

Manazarta


Adamu, M. (1975)  “Distribution of  Trading  Centres  in the Central  Sudan  in  Eighteen  and

Nineteen Centuries” A paper presented at the Department of History, A.B.U, Zaria.

Alhassan, da wasu.(1982) Zaman Hausawa Na Biyu. Northern Nigerian Publishing Company.

Bachaka, T.M.  (2006) “Karin  Magana  Cikin Wak’ok’in  Sarauta: Nazari a kan Wak’ok’in Sani

Aliyu ‘Dandawo. Kundin digiri na d’aya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Bada, B.D. (1995) “Literary Study of  Themes, Functions, and Poetic Divices of  Hausa Karin

Magana”  Ph.D  Thesis, Department  of  Modern  European  Languages and Lingistics,

Usmanu ‘Danfodiyo University, Sokoto.

Balarabe, A.A (2008) “Kasuwanci a Ma’aunin Karin Magana” Kundin digiri na d’aya, Sashen

Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Birniwa, H.A. (2005)“Tsintar Dame a Kala: Matsayin Karin Magana a Cikin Wak’ok’in Siyasa

A cikin Mujallar ‘Dund’aye No 2. Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato.

Bunza, A.M.  (2005)  “Arashi  Shi  Gogi  Bak’auye: Nazarin  Karin  Maganganun  da  ke Jikin

Motoci”  Takardar  da  aka  gabatar  a  Sashen  Koyar  da  Harsunan  Nijeriya,  Jami’ar

Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Bunza, D.B. (2005)  “Noma  da Yadda  ake  Gudanar  da Shi a Garin Bunza” Kundin digiri na

d’aya, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

‘Danyaya, B.M. (2007) Karin Maganar Hausa. Makarantar Hausa Publishers, Sakkwato.

Garba, C.Y. (1991) Sana’o’in Gargajiya a K’asar Hausa. Baraka Press and Publishers Limited,

Kaduna.

Kankiya, I.M.  (1996)  “Sababbin  Karin  Magana  na  Hausa”  Kundin  digiri na d’aya, Sashen

Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Nahuce, M.I. (2008)  “Karin  Maganar Hausa a Rubuce” Kundin digiri na biyu, Sashen Koyar

da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.
www.amsoshi.com

Post a Comment

3 Comments

  1. Thanks for the wonderful guide

    ReplyDelete
  2. Youre so cool! I dont suppose Ive learn anything like this before. So good to find someone with some unique ideas on this subject. realy thanks for starting this up. this web site is one thing that is wanted on the internet, somebody with just a little originality. useful job for bringing one thing new to the internet!

    ReplyDelete

Post your comment or ask a question.