Ticker

6/recent/ticker-posts

Gambo Mawakin Maza Ne Ba Mai Cin Gashin Kansa Ba

MUSA SHEHU
Takardar da aka shirya a taron kara wa juna sani na musamman da
Sashen koyar da harsunan Nijeriya ta shirya, Jami’ar Usmanu
Danfodiyo, Sakkwato

28th Feb, 2009

1.0    GABATARWA


Alhaji Muhammadu Gambo Fagada wanda aka fi sani da Gambo mai wak’ar ‘barayi, mawak’i ne da ya yi fice a kowane sak’o na k’asar Hausa. Manya da yara, maza da mata, masu iko da talakawa, ma’aikata da masu hannu da shuni, babu wanda bai jin labarin Gambo. Watak’ila wannan fice da ya yi bai rtasa nasaba da irin wak’ar da yake yi da kuma wad’anda yake yi wa wak’ar. Da yake Gambo wak’ar ‘barayi yake yi, ko za a iya saka shi a rukunin mawak’an maza duk da yake wasu na kallonsa a matsayin fand’ararre ko mai cin gashin kansa ? Saboda haka ne wannan takarda za ta kalli Gambo ta kuma auna shi a mizanin mawak’an maza. Bari mu kalli mawak’an maza kamar yadda masana suka kalle su da zimmar shigar da Gambo a cikinsu.

2.0   MAWAKAN MAZA


Sa’idu Muhammad Gusau (1993) ya bayyana mawak’an maza da cewa “wak’ok’in maza wak’ok’i ne da ake yi wa wasu rukunin jama’a da suka had’a da ‘yan dambe da ‘yan tauri da ‘yan kokawa da ‘yan baura da sauransu”. Daga cikin makad’an wannan rukuni akwai ‘Dan’anace da Kassu Zurmi da Muhammadu Gambo da makamantansu.

Shi kuwa Balarabe (2000) cewa ya yi “ mawak’an maza su ne mawak’an da ke yi wa masu nuna jarunta ko bajinta wajen neman suna”.

A.B. Yahya (1997) yana cewa “wak’ar maza wak’a ce da ake yi wa mutanen da suka shahara ga abubuwan jaruntaka kamar dambe da kokawa da yak’i da tauri, idan aka had’a da sata ma babu laifi”.

Idan aka yi nazarin wad’annan ra’ayoyin masana da idon basira za a ga cewa, kusan kowanensu ya ta’bo wak’ar ‘barayi ko da a fakaice ne. Shi Gusau kai tsaye ya fito ya saka wak’ar ‘barayi a cikin rukunin mawak’an maza. Shi kuwa A.B. Yahya kawo sata ya yi daga cikin abubuwan da ya lissafa na jaruntaka da mawak’an maza ke yi wa masu yin ta kid’a.

3.0       DANGANTAKAR WAK’OK’IN MAZA DA WAK’OK’IN GAMBO


Hak’ik’a akwai dangantaka makusanciya tsakanin wak’ok’in maza da wak’ok’in Gambo musamman idan aka yi la’akari da jigogin ire-iren wak’ok’in maza da ake samu a wak’ok’in Gambo. Akwai jigogin wak’ok’in maza da yawa wad’anda idan aka tsaya aka yi nazarin wak’ok’in Gambo da idon basira za a samu kwatankwacinsu a ciki. Bari mu kalli jigogin wak’ok’in maza kamar yadda masana suka kalle su.

4.0    JIGOGIN WAK’OK’IN MAZA


Yahya (1997) ya bayyana ma’anar jigo da sak’o ko manufa ko bayani ko ruhin da wak’a ta k’unsa wanda kuma shi ne abin da wak’ar ke son isarwa ga mai saurare ko karatu ko nazarinta. Ya kuma bayyana muhimman jigogin wak’ok’in maza da suka had’a da zuga da zambo da ta’addanci da bajinta da kuma yabo. Bari mu kalli wad’annan jigogi daga wak’ok’in maza da kuma yadda suke fitowa a wak’ok’in.

4.1.1  JIGON ZUGA

Zuga a wak’ok’in maza na nufin amfani da wad’ansu kalamai ko kalmomin da za su sa maza yin wad’ansu abubuwa na bajinta a fagensu na dambe ko tauri ko kokawa ko sata. (Yahya 1997). Ana iya kallon wannan jigo a wak’ar Garba ‘Danwasa da ya yi wa Mamman Dogo kamar haka :

Jagora :                           Wa ka bid’an Muhamman Dogo

Yanzu gwani ya k’ask’anta shi

Don kowa yab buga bai kwana

Don ya yi karo da Mamman Dogo

(Garba ‘Danwasa)

A wannan d’an wak’a za a ga ‘Danwasa yana k’ok’arin zuga Mamman Dogo yana nuna cewa babu mai iya d’aukan kwaranniyarsa a fagen daga, ko wa ya tare shi kuwa, a yi ba da shi ba. Muhammadu Gambo ya fito da kwatankwacin wannan jigo a wata wak’arsa ta arangamar “Tudu Tsoho” da “Inuwa ‘Danmad’acci”, inda yake k’ok’arin zuga Tudu yana cewa ya buwayi duk wani ‘barawo mai ji da kansa da ya kwana a k’asar Hausa. Ga dai abin da Gambo ke cewa :

Jagora :                     Sai nik koma ga kan Tudu

Nic ce tsohon kolo kai kad dad’e Tudu

Mai hana maiki cin idanu

Gabanka gabas swai ya yi yamma

Yara ba su ganin takin k’ahwakka

(Gambo)

Kamar dai yadda ya faru a d’an wak’ar ‘Danwasa inda yake cewa babu mai iya karo da “Mamman Dogo”, shi ma Gambo yana zuga Tudu da cewa babu wani ‘barawo da ke iya tunkararsa da sunan yi masa sata.

 

 

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/gudummuwar-sanaoin-zamani-wajen-bunksa-tattalin-arzikin-ksar-hausa/

4.1.2   JIGON  TA’ADDANCI


Jigo ne da mawak’an maza ke bayyana irin ta’asa ko ta’addancin wanda ake yi wa wak’a ya aikata, a kuma nuna shi kad’ai ke iya aikata ta ba tare da fargaba ba. (Yahya 1997). Kassu zurmi ya fito da wannan jigo a wata wak’a da ya yi wa wani d’an tauri mai suna “Nomau Namagarya”, inda yake k’ok’arin ingiza Nomau ya aikata wani ta’addanci ga jama’ar garin Magarya domin ya sa ma garin wuta ya k’one gaba d’aya. Ga abin da Kassu ke cewa :

Nai tambaya cikin ‘yan tauri

Kuma nai tambaya ga manyan makad’a

Wa anka wa doki da gangami ba ni ba

Doki da gangami sai Nomau

..............................................................

Amsad doki gidan kara mina na ga matsiyaci

Bari sai gobe da sahe iskan nan ya taso

Mai kwasan sansami yana kar-kar-kar

Sannan d’ebo wuta ga ragga ka hita

Yac ce Kassu shawarakka ita za ni biya

Nic ce in kau kab bi ta baba doki aka yi Magarya

 

Kwatankwacin wannan jigo ya fito a wak’ar Gambo da ya yi wa wani ‘barawo da ya tafi sata a wani gida ya tarar da mai gida bai nan sai matarsa kawai da ke d’auke da tsohon ciki. Lokacin da ‘barawon ya d’auko kud’in mai gidanta sai matar ta rik’e shi ta hana shi wucewa. Daga k’arshe dai ‘barawon ya soka mata wuk’a ga ciki ya wuce da kud’in. Ga dai yadda Gambo ya kawo d’an wak’ar yana cewa :

 

Jagora :              Sad da yac ciri yuk’a yak kihwa mata

Tai wani tsalle tah hwad’i jicce

Dan nan wani dad’i yak’ k’ume ni

Mun bas su da gawa d’anya-d’anya

Mu ga mu da kud’d’i lahiya lau

Muna shagalin banza da yohi

Idan aka kwatanta d’an wak’ar Kassu da wannan d’an wak’a na Gambo za a ga dukkansu suna d’auke da bayanin ta’addanci, domin da wanda ya sa ma gari wuta cike da d’imbin jama’a da nufin k’ona su, da wanda ya soka wa mace mai tsohon ciki wuk’a duk ‘yan ta’adda ne da kuma aikata ta’addanci.

4.1.3   JIGON BAJINTA

Wannan jigo ne da ke bayyana abubuwan da gwarzon da ake yi wa wak’a ya aikata wad’anda da jin su mai saurare ko karatu ya san ba aikin matsoraci ba ne. Wannan jigo ya bayyana a wak’ar da “Kassu Zurmi” ya yi wa wani d’an tauri mai suna “Garugaru”, inda Kassu ya nuna an tafi wata farauta aka kama wata dabba ya nemi a ba shi rabonsa. Daga nan sai wasu ‘yan tauri suka ce masa ya nemo mai k’watar masa. Sai ga Garugaru ya iso sai Kassu ya ta da kid’insa. Nan take ‘yan tauri nan suka rufar wa Garugaru da sara, shi kuwa yana k’ok’arin kutsa kai da nufin k’wato wa Kassu rabonsa. A tak’aice, ga dai abin da Kassu ke cewa a d’an wak’arsa kamar haka :

Anka yi mai bukkat tauri

Bai hwasa tahowa ba

Su ko ba su hwasa kashi nai ba

Shaggun ba su hwasa kashi nai ba

Shi ko bai hwasa tahowa ba

Daga k’arshe dai tilas aka raba naman aka ba Kassu rabonsa. Irin wannan jigo ya yi daidai da wata wak’a da Gambo ya yi wa wani ‘barawo mai suna “Hantsi” lokacin da ya tafi wurin sata rana ta ‘baci aka ta da shi taron mutane suka rik’a jifansa shi ma yana mayar da martani yana jifansu. Ga abin da Gambo ke cewa a kan ‘barawon:

Jagora   :                Hantci shi jefa, su su jefe shi

Har anka zo hilin kid’inmu

Gambo bai gushe ba yana k’ara jaddada wannan jigo na bajinta a wani d’an wak’arsa da ya yi wa wani ‘barawo mai suna Na’bagarawa Bunsuru Bawa yana cewa:

Dubi Na’bagarawa Bunsuru Bawa

Wata rana an tasai kasuwag Gummi

Bawa sa’ad da Hulani nar ryhe shi

Mai zwage takobi mai zwago adda

Mai here sanda da masu ciro icce na danni

Da masu bid’o dutci a jihwai

Kai ku kashe kowa ka ce mishi

Babu guda mai kawo ceto

Ina tsaye sai ni’b ‘bata raina

Don komi akai in babu ceto

Ana wahala ko ba a mace ba

Bawa ana ta bugunai tun yana tsaye

Amman kan da a kai mugu k’asa

Ya hwashe kanu sun hi maitan

Don haka, idan aka kwatanta d’an wak’an Kassu da kuma d’an wak’ar Gambo za a ga cewa kusan rawa d’aya suka taka na nuna bajinta. Dukkansu sun nuna bajinta na rashin tsoro taron jama’a ko da kuwa rai zai salwanta.

4.1.4    JIGON YABO

Mawak’an baka kan rera wak’a mai d’auke da wannan jigo. Mawak’an kan yi hakan ne ta hanyar fito da wasu kyawawan halayen mutumin da suke yi wa wak’a suna yaba masa. Yabo a cikin wak’ok’in maza bai k’unshi kalmomin da mai saurare zai iya saurin d’auka a matsayin fad’ar abubuwan k’warai ga wanda ake yi wa shi ba tamkar yadda zai d’auki kalmomin yabon sarki a wak’ok’in sarauta ko na jama’a ba. (Yahya 1997). Dalili kuwa shi ne cewa, rayuwar gwaraje da irin abubuwan da al’umma ke d’ammahar ta gani a wajensu ta bambanta da ta sauran mutane. Jigo ne da ke yabon wani jarumi a kan wani ta’asa da ya yi ko wani bajinta ko jaruntaka ko k’arfi da makamantansu. ‘Dan’anace ya fito da wannan jigo a wak’ar da ya yi wa “‘Dandunawa” inda yake cewa :

Maza ga giwa masha dahi

Zaki mai k’ashi guda

Gwanki mai kiwon ‘bata

Idan aka koma ga wak’ok’in Gambo, za a iya samun kwatankwacin wannan jigo a wata wak’a ta arangamar “Tudu Tsoho” da “Inuwa ‘Danmad’acci”, inda Gambo yake yaba wa Tsoho, domin duk wani ‘barawo da ya kwana k’asar Hausa Tudu Tsoho ya gagare shi. Ga dai irin yabon da Gambo ke yi masa a wani d’an wak’a nasa:

Jagora :                 Tsohon kolo kai kad dad’e Tudu

Mai hana maiki cin idanu

Gabanka gabas swai ya yi yamma

Yara ba su ganin takin k’ahwakka

‘Dan’anace da Gambo suna k’ok’arin yaba gwarajensu domin su saka tsoro ko fargaba ko razana ga zukatan abokan hamayya.

KAMMALAWA


        Ba shakka Alhaji Muhammadu Gambo Fagada mawak’i ne na maza ba fand’ararre ko mai cin gashin kansa ba, musamman idan aka yi la’akari da bayanai da misalan da suka gabata. A cikin bayanan da aka kawo, ya bayyana zahiri cewa, kusan dukkan muhimman jigogin da ake da su a wak’ok’in maza an samu makamantansu a wak’ok’in Muhammadu Gambo, wanda suka had’a da zuga da bajinta da yabo da ta’addanci da sauransu da dama. Idan kuwa haka ne, wak’ok’in maza da wak’ok’in Gambo tamkar ‘Danjumma da ‘Danjummai ne ta fuskar jigogin da kowanensu yake d’auke da shi.

 

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/barazanar-zamani-kan-magungunan-hausawa-na-gargajiya/

 

MANAZARTA

Balarabe M.A. (2000).  Nazari  Kan Wak’ar Baka ta Hausa. Gaskiya  corporation

Zaria.

Gusau  S.M.  (1993).    Jagoran   Nazarin  Wak’ar  Baka.  Benchmark  publishers

Limited Kano.

Gusau S.M. (2008).Wak’ar Baka a K’asar Hausa: Yanaye-yanayensu da sigoginsu

Benchmark publishers limited, Kano.

K/Ganuwa S.L. (1989). Jigo da  Salon  Wak’ok’in  Maza :  ‘yan  tauri  da  ‘barayi.

Kundin digiri na farko, Jami’ar Usmanu  ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Mayyama U.H. (2001).  Jigon  Sata Cikin  Wasu  Rubutattun K’agaggun Labaran

Hausa.    Kundin   digiri   na   biyu,   Jami’ar   Usmanu   ‘Danfodiyo,

Sakkwato.

Mayyama U.H. (2008). Sata a zamantakewar Hausawa: Nazarin wak’ok’in ‘barayi

na  Muhammadu  Gambo  Fagada.  Kundin  digiri  na  uku,  Jami’ar

Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Suleman A. (2006). Take  da Kirari a Cikin Wak’ok’in  Garba  ‘Danwasa  Gummi.

Kundin digiri na farko, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Yahya  A.B.  (1996).  In  Praise  of   Thieves : An  Odd  Category in  Hausa Oral

Poetry. Takardar  da  aka  gabatar a taron  k’ara wa juna sani, sashen

koyar da harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sokoto.

Yahya A.B.  (1997).  Jigon  Nazarin  Wak’a. Fisbas  Media  Services,  Kaduna.

 www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments