Harshe Da Siyasar Canji A Arewacin Nijeriya

     DAGA

    Nazir Ibrahim Abbas
    Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sokoto
    Email: ibrahimabbasnazir@gmail.com  GSM: 08060431934

    Da

    Muhammad Mustapha Umar
    Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sokoto
    Email: mustaphahausa@yahoo.com  GSM: 08065466400

    Tsakure

    Harshe da siyasa muhimman abubuwa biyu ne da ke tafiya tare a cikin rayuwar al’umma. Harshe shi ne hanyar sadarwa da al’umma ke amfani da ita wajen bayyana tunaninsu da ra’ayoyinsu da duk wani abu da ke cikin zukatansu game da duniya. Siyasa kuwa ta danganci k’arfin iko na jagoranci da shugabancin jama’a da dukiyoyinsu, da tunaninsu da kuma d’abi’unsu. Wannan mak’ala za ta kalli tasirin harshen Hausa cikin al’umma da jami’iyyar adawa ta yi amfani da shi a wajen yak’in neman za’be da bayan babban za’ben shekara ta 2015 a arewacin Nijeriya. Binciken ya gudana ne a kan ra’in nazarin kalami a kimmiyar harshe.

    1.0     Gabatarwa


    Masana sun bayar da ma’anoni daban-daban na harshe Sapir kamar yadda Lyons (1981)[i] ya kawo, ya ce: "Harshe abu ne da ya danganci mutane, kuma hanya ce da sadarwa da bayyana buk’atu da sha’awa ta hanyar furta kalmomi". Bugu da k’ari Bloch & Trager a ruwaitowar Lyons sun ce; "Harshe hanya ce ta furta sautuka da manufar sadarwa tsakanin al’umma". Southworth da Chander (1974)[ii] kuwa sun ce; "Babu wata al’umma a duniya da ba ta da harshe. Harshe shi ke bayyana al’umma kuma shi ne hanyar sadarwar al’umma mai alamomi, ma fi tsari wanda ke da alak’a sosai da tunani da bisira". Yakasai (2012)[iii] ya kawo ma’anar harshe da; "Rai ko kuma zuciyar duk wani tunani da aiki na d’an Adam musamman dangane da abun da mutum ke ji game da kansa ko k’asarsa, ko addininsa ko kuma yadda shi kansa ya d’auki kansa". Fagge (2012)[iv] ya ce; "Harshe shi ne hanyar da mutane suka fi amfani da ita wajen sadarwa da ta fi tsari".

    Harshe yana da matuk’ar muhimmanci ga al’umma domin kuwa shi ne sadarwa, babu wani al’amari d’aya da ya shafi d’an Adam wanda babu harshe a cikinsa. Da harshe ne d’an Adam ke tunani da sadarwa ta hanyar magana ko ishara, ta harshe ne mutum ke bayyana ra’ayinsa da addininsa da sha’awarsa da fahimtarsa ga duk wani al’amari na duniya. Harshe shi ne babban abun da ya bambanta mutum da dabba, bugu da k’ari wani abu ne da ba a iya raba mutum da shi, tamkar jini da tsoka ne a jikin mutum.[v]

    Harshen mutum kuwa shi ke taimaka masa wajen bayyana sababbin tunane-tunane da fahimtar kalmomi da jumloli da kuma samun damar tsara magana da jera tunani da dangantaka kalmomi ko jumloli da ma’anoninsu a zahiri. Shi ke taimakawa wajen dangantaka sautuka da kalmomi da tattaunawa abubuwa da yanayoyi da har ma koyon al’adu da fahimtar sak’onni. Harshe mutum shi ke tafiyar da tunaninsa a cikin kowane al’amari da kuma bayyana masa duniyar da yake ciki ko fahimtar duniya.[vi]

    Wannan zai tabbatar muna cewa babu wani al’amari da mutum zai yi ba tare da amfani da harshensa ba. Siyasa kuwa a d’aya ‘bangare tamkar harshe, sak’e take a cikin al’umma, domin zaman mutane tare wuri d’aya da yanayin zamantakewa cikin al’umma ya sa dole ne a samu jagoranci da shugabanci tsakaninsu, samun shugabanci kuwa koyaushe yana tafiya ne tare gwagwarmaya ta neman mulki da jagorancin wanda da harshe ake yinsa. Wannan neman jagorancin al’umma shi ne siyasa. Wannan kuwa ya dad’e cikin Hausawa tun kafin zuwan tsarin siyasa ta Turawa ta tsayawa takara da neman goyon baya kamar yadda muke da ita a yanzu.

    Harshe da siyasa ke nan ba za su rabu ba domin da harshe ne ake k’ok’arin ko dai jawo hankali da ra’ayin mutane domin samun amincewarsu ga wani ko kuma yin suka domin kushe wani daga samun shugabanci ko jagorancin al’umma. Wannan takarda ta yi nazarin gudummuwar harshen Hausa wajen tabbatar da sauyin siyasa ko siyasar canji a za’ben sheakar ta 2015, a arewacin k’asar nan. Takardar za ta yi nazarin tasirin wasu kalamai da tattaunawa a tsakanin al’umma wand’anda babu ko shakka sun taimaka gaya wajen tabbatar da siyasar canji a arewacin k’asar nan inda harshen Hausa shi ne ya fi yawan al’umma da girma da aka fi amfani da shi tsakanin al’umma da kuma wajen yak’in neman za’be tun farkon fara siyasa a jamhuriya ta d’aya a k’asar nan.

    Harshen Hausa shi ne harshen huld’a a arewacin Nijeriya tun zamanin turawan mulkin mallaka. Harshen ya dad’e yana taka rawa a matsayin wanda ya fi yawan jama’a da samun gatar kayayyakin karatu da amfani da shi wajen koyarwa a makarantu da amfani da shi a gidajen rediyo na ciki da wajen k’asar nan. Bugu da k’ari an dad’e ana gudanar da ayyukan gwamnati a majalisun dokokin jihohi na arewacin k’asar nan da shi. Wannan ne ya sa dole ne ‘yan siyasa da ke neman shugabancin jama’a gudanar da yak’in neman za’bensu a cikin harshen Hausa a arewacin k’asar nan. Bayan tasirin harshen akwai kuma yawan al’umma masu jefa k’uri’a daga jihohi 19 na arewacin k’asar nan baya ga Hausawan da suka watsu a kowane sak’o da lungun k’asar. Ko a jihohin da ba Hausawa ba ne gaba d’aya a arewacin Nijeriya, harshen Hausa ya kasance shi ne harshen huld’a a tsakaninsu al’ummomin.

    Wannan takarda za ta kalli tasirin harshen Hausa wajen tabbatar da  canjin siyasa a arewacin Nijeriya. Kyautatuwar jagoranci kuwa wani muhimmin makami ne na samar da ci gaban al’umma a k’asar nan, musamman a arewacinta, la’akari da yadda al’amarin rashin tsaro da rashin tabbacin d’orewar had’in k’asar nan da barazanar wasu yankuna na watsewar k’asar, idan ba wata jam’iyya ta yi nasara ba daga wasu tsagerun yankuna da danniya da babakere suka yi kaka-gida a lokacin mulkin da ya gabata. Samun ci gaban da ya dace kuwa zai tabbata ne kawai idan mutane suka samu irin jagorancin da suke fata, wanda daga k’arshe ya tabbata, da ake fatar zai samar da ci gaban da duk ake buk’ata a cikin k’asar nan baki d’aya. An karkasa takardar cikin sassa kamar haka; gabatarwa da bayyana ra’in bincike da dabarun bincike sai taken sunaye da kalmomin da aka yi amfani da su wajen yak’in neman za’ben da kuma bayan kammala za’ben, bayan da aka samu nasara tare da bayanin irin tasirin da suka yi a cikin zukatan al’umma sai jawabin kammalawar aikin.

    https://www.amsoshi.com/2017/08/16/gudunmuwar-harshen-hausa-ga-siyasar-canji-a-arewacin-nijeriya/

    1.1     Ra’in Bincike


    Fahimtar cewa ba za a iya raba mutum da harshensa ba kuma duk wani abu da mutum zai yi ko ake buk’atar sanar da shi musamman ta jan ra’ayinsa da neman amincewarsa to da harshensa za a yi hakan. Wannan nazarin ya yi k’ok’arin amfani da fagen nazarin kalami (discourse analysis) wajen nazarin tasirin wasu kalaman Hausa na siyasa wajen tabbatar da siyasar canji a k’asar nan, domin fito da irin rawar da harshen Hausa ya taka a irin wannan muhallin. Harshe shi ne hanyar da ake iya nazarin al’umma da tsarinsu da sanin manufofinsu da yadda suke gudanar da al’amurransu da tunaninsu.

    Fagen nazarin kalamai (discourse analysis), fage ne dake nazarin huld’a da harshe tsakanin al’umma da yadda mutane ke tattaunawa a kan siyasa da wasu al’amurra na rayuwa da suka shafe su a maganganunsu na yau da kullum tare da kuma yin muhawara da bayyana ra’ayi ta amfani da harshe.[vii] Fagen nazarin kalaman yana k’ok’arin nazarin sakamakon da aka samu dalilin huld’a ta amfani da harshen. Wannan yana nuna cewa ana nazarin harshe ne daidai da manufar da ake son a cimma ta amfani ba wai nazartar tsarin nahawunsa kawai ba. Manufa ita ce sanin a kan wane dalili ne aka yi amfani da harshen? Wannan fage wani jigo ne wajen nazarin zamantakewar rayuwa cikin harshe. Saboda haka yake da alak’a da tarihi da ilimin halayyar d’anadam da ilimin rai. A tak’aice dai yana nazari na harshe a wani muhalli da yadda muhalli ko yanayin magana ke ba da ma’anar kalmomi, su kuma kalmomin su yi tasiri ga muhallin da aka yi maganar. A irin wannan hali ana kallon mai maganar da maganar da ya yi da muhallin da kuma wanda yake maganar da shi da tasirin maganar ga wanda aka yi wa ita.

    Ra’in kalamin magana, ke nan yana kulawa da huld’ar magana ta hanyar wasu bayyanannun abubuwan rayuwar al’umma. Masu magana ko rubutu suna amfani da harshe da sassan jikinsu da wasu abubuwa (na muhalli) da ke bayyane domin fito da abun da suke magana akansa. Masu saurare ko karatu kuwa suna mayar da hankali ga harshen da motsa sassan jiki na ishara da abubuwan zahiri da aka yi magana kansu (na muhalli) domin su fahimci abin da ake magana a kai yadda ake so ko akasin hakan. Da wannan muna iya cewa masu magana da rubutu suna k’ok’arin fito da hoton wani abu na rayuwa a bayyane domin  masu saurare ko karatu su fahimce shi. Wannan k’ok’arin yana iya yin nasara ko ya kasa fitowa da bayanan na zahiri wad’anda bayanannun abubuwa ne da ke iya sauyawa da lokaci a tarihi da zamantakewar al’umma.

    Wannan al’amari kuwa haka yake gudana tsakanin ‘yan siyasa da al’umma a koyaushe, k’ok’arin amfani da harshe suke yi domin fito da manufarsu da soke ko kushe abokan adawarsu a siyasance ta hanyar amfani da sunaye da nuna k’warewa ga harshe ta nuna alamcin adon harshe da makamantansu, daidai da irin muhallin da suke magana a cikinsa yadda zai yi tasiri a zukatan al’umma har ya zama wani abun tattaunawa da sharhi a kai. Kalaman da za mu yi nazari za a ga mafi yawa ‘ya’yan jam’iyyar siyasa da magoya bayansu ne suka k’irk’iro su domin fitowa da wani abu da zai yi matuk’ar tasiri a zukatan al’umma na cimma manufarsu ta samun nasarar za’be da kushe abokan adawa, da kuma nuna fin dacewa ko cancanta ga jagorancin jama’a, wanda ko shakka babu shi ne ya yi tasiri a zukatan al’umma da sha’awarsu ba ya ga ra’ayin da wata kila daman suna da shi ga samun nasarar canjin shugabancin siyasa da aka yi a k’asar nan.

    1.2     Dabarun Bincike


    An tattara bayanai da aka yi amfani da su a wannan binciken daga littafai da mujallu da aka samu daga d’akin karatu. Sauran bayanan misalan kalaman da aka yi amfani da su kuwa an tattara su ta hanyar sauraren zantukan mutane a tattaunawarsu ta yau da kullum da ta shafi siyasa, kafin za’be da lokacin za’be da bayan kammala za’be a jihohin Arewacin k’asar nan. Haka ma an kalli wasu kalmomin da wasu mawak’an siyasa suka yi amfani da su wad’anda suka yi tasiri a cikin zantukan al’umma da suka taimaka wajen tabbatar da canji a za’ben shekara ta 2015. Bugu da k’ari marubutan sun kuma yi amfani da masaniyar da suke da ita na wasu kalmomin da kasancewarsu Hausawa kuma mazauna wasu yankuna na Arewacin k’asar nan.      

    1.3     Harshe da Siyasa


    Akwai dangantaka mai k’arfin gaske tsakanin siyasa da harshe, domin kuwa babu wani tsarin siyasa ko mulki, kowane iri, wanda ba ya amfani da hanyar sadarwa ta baka ko rubutu wajen jawo hankalin jama’a ko fahimtar da wasu wani abu. An sani cewa wani lokaci akan yi amfani da k’arfi wajen biyar da mutane, amma dai duk da haka ba a ta’ba samun wani tsarin mulki ko siyasa wanda sam ba ya amfani da harshe ba. "Siyasa wata hanya ce ta amfani da ra’ayoyan jama’a, domin samar da kyakkyawan shugabanci tsakanin al’umma". Siyasa tana nufin nazarin yadda za a mulki k’asa a k’ark’ashin za’ba’b’bun wakilai a tutar jam’iyyu daban-daban.[viii]  Da wannan za mu fahimci cewa harshe shi ne hanyar sadarwa ta d’an’adam siyasa kuwa tana nufin tsarin shugabanci da jagorancin al’umma ta hanyar za’ba’b’bun shugabanni. Shugabanci da jagorancin al’umma kuwa ba zai yi yu ba sai an yi amfani da hanyar sadarwar al’umma wadda suka fahimta suka kuma aminta da ita. Dangantakar harshe da siyasa ta k’ud-da-k’ud ce, domin siyasar da harshe ake gudanar da ita, tun daga yak’in neman za’be har ya zuwa za’ben da kuma gudanar da mulki ko jagorancin al’umma.

    A tsarin kamfe na siyasa akwai dabarun sadarwa da jama’a na yak’in neman za’be da suka had’a da; k’ok’arin da d’antakara zai yi domin a san shi, a san sunansa da jam’iyyarsa, domin kar a za’bi wani a matsayinsa bisa kuskure daga nan sai gina ko tabbatar da tunani mai kyau a kansa da sunan nasa a cikin zukatan al’umma, da tabbatarwa jama’a da cewa matsalarsu tabbas, ita ce damuwarsa (wannan ne ke saka ‘yan takara su yi ta k’ok’arin tallar kansu da yayata manufofinsu a kafafen sadarwa na gidajen Rediyo da Talabijin da Jaridu) sai bayyana manufofin d’antakara da jam’iyya da suka shafi buk’atun al’umma wad’anda kuma suka sa’ba da na abokin adawa ta hanyar jawabai a yak’in neman za’be da halartar muhawurori a kafafen sadarwa domin yayata manufofi da yin suka. Akwai kuma fahimtar ‘yantakara da sanin bambancin mai takara da abokin adawarsa (wannan gagarumin aiki ne musamman ga wanda ba ya bisa mulki). A irin wannan mataki kuwa dole ne d’antakara ya yi suka da hujjoji na gaskiya, domin masu jefa k’uri’a ba za su yarda da hujjojin k’arya ba, za su aminta ne kawai da bayanan gaskiya da hujjoji masu ma’ana.

    Bugu da k’ari akwai kuma kariya daga soke-soken jam’iyyun adawa ta bayar da misali daga wani abu na d’antakar (wanda ake iya amfani da shi a matsayin makamin yak’in neman za’be na soke shi) a nan dole ne wanda aka soka ya mayar da martani cikin hikima kuma a kan lokaci, ba zai yi shiru ba domin yin shiru tamkar amincewa ne, da suka wadda za ta iya yi masa illa ga rasa jama’a da ke goyon bayansa, yana da wuya masu jefa k’uri’a su za’bi d’antakara in bai bi wad’annan matakan ba. Dukkan wad’annan matakan da harshe ake amfani wajen aiwatar da su. Wanda ya fi wani k’warewa ga harshe da iya magana da suka, sai a ga ya yi nasara kan abokin adawarsa na siyasa.

    Iya harshe da magana wani ingantaccen makami ne wajen samun nasara a cikin harakokin siyasa, wannan ne ya sa ake jawabai a wajen yak’in neman za’ben, a yi muhawarori a kafafen sadarwa na gidajen talabijin da rediyo da tattaunawa a mujallu da jaridu, kuma kowace jam’iyya tana k’ok’arin yad’a manufofinta da yayata ‘yantakararta a rubuce da magance da kuma alamce a fastocinta da na ‘yantakararta ta hanyar hotuna da alamomin jam’iyyu masu wata ma’ana (misali; tsintsiya da lema da zakara d.s) da taken kirarin jam’iyyun na jan hankali daban-daban, wanda wannan ko shakka babu ya kan yi tasiri sosai a zukatan al’umma da ke goyon bayansu.

    1.4     Harshe da Siyasar Canji a Arewacin Nijeriya


    A za’ben shekaru ta 2015, wanda a tarihin k’asar nan shi ne irinsa na farko da babbar jam’iyyar adawa mafi girma ta kayar da jam’iyyar da ke kan mulki wanda wannan mak’ala tana ganin harshen Hausa ya yi tasiri sosai a wajen yak’in neman za’ben a arewacin k’asar nan. Harshen ya kuma taimakawa jam’iyyar da d’antakakar ta suka yi nasara. Daga cikin dabarun da ‘yan jam’iyyar APC da magoya bayansu suka yi amfani da su akwai; kirari da adon harshe da k’irk’ira sunaye daban-daban na yabo ga d’antakararsu na shugaban k’asa da sunayen suka ga jam’iyyar dake kan mulki a lokacin da d’antakararta.

    An yayata wad’annan manufofin kuwa suka zama abubuwan batu da amincewa a cikin zukatan al’umma tun daga wancan lokacin har ya zuwa yau, wanda hakan tabbas ya taimaka gaya wajen tun’buke masu mulki da samun galaba a kansu. Wasu daga cikin kalaman da aka yi amfani da su su ne; sunayen yabo da sunayen suka da kirarin jam’iyyu da ‘yantakara da adon harshe. Duk wad’annan abubuwan sun faru a lokuta daban-daban na kafin za’be da lokacin yak’in neman za’be da kuma ma har bayan za’ben (wannan lokacin da muke ciki).

     

    1.4.1   Ire-iren Kalaman Siyasar Canji Kafin Za’ben 2015

    ‘Yan jam’iyyar APC da magoya bayansu sun lazimci yin amfani da wasu kalaman canji, musamman a lokacin yekuwar neman za’be, don yad’a manufar jam’iyyarsu da ‘yan takararsu, da kuma yin suka da kakkausar murya a kan salon tafiyar jam’iyya mai mulki. A wannan sashe za a nuna yadda  wad’annan kalamai suka ba da gudunmawa, wajen fad’akar da magoya baya da duk wani mai sha’awar canji muradu da ak’idar jam’iyyar adawa.

    1. APC sak ko canji sak: A za’bi jam’iyyar APC a dukkanin matakan za’bu’b’buka (daga shugaban k’asa har zuwa kansila)

    2. A saka, a tsare, a raka, a jira: Bayanin da mai girma shugaban k’asa Muhammadu Buhari ya rik’a amfani da shi lokacin yak’in neman za’be, don masu kad’a k’uri’a su d’auki matakin sa ido, don hanawa ko rage aringizon k’uri’u da ya zama ruwan dare a za’ben Nijeriya.[ix]

    3. ‘Yan lema: Sunan da aka bai wa magoya baya kuma ‘yan jam’iyyar PDP, wadda ke da alamar lema.

    4. Sai mun share su: Da’awar da ‘yan jam’iyyar APC ke yi na k’ok’arin canja gwamnati ko kar’be ta. Wato suna amfani da aikin alamar jam’iyyarsu ta tsintsiya wajen bayyana manufarsu.

    5. Mai malfa: Sunan da ‘yan jam’iyyar APC suke kiran tsohon shugaban k’asa Dr. Goodluck Ebele Jonathan, musamman saboda hular da yake yawan sawa ta yi canjarar da malfar Bahaushe, kuma ga alama sunan na suka ne.

    6. Kaduna sai mai rusau: Sunan da ake kiran d’an takarar gwamnan jahar Kaduna malam Nasiru Elrufa’i, musamma saboda ayyukan rushe gine-ginen da aka yi ba bisa k’a’ida ba, a lokacin da yake matsayin ministan birnin tarayya Abuja.

    7. Nijeriya sai mai gaskiya/ Sai mai gaskiya/ sai dogo d’an Daura/ sai baba Buhari: Sunan da aka rad’a wa d’an takarar shugaban k’asa Muhammadu Buhari, saboda a baya an san ya aikata abubuwa  cikin gaskiya da  rik’on amana.

    8. Buhari fiya-fiya kashe k’waro ko maganin k’wari: Fiya-fiya ruwan magani ne da ake amfani da shi don kasha k’wari, amma ‘yan siyasa da wasu jama’a na ambaton Muhammadu Buhari da suna, saboda tabbacinsu na cewa shi ne kad’ai zai iya ceto Nijeriya daga hannun ‘barayin gwamnati, wad’anda suka shigar da k’asa cikin wahalhalu tamkar yadda k’wari ke yi wa mutane da  tsirrai, da itace  tu’annuti ko lahani.

    9. Sai mai tsintsinya/Tsintsiya mai share datti/Tsintsiya mad’aurinki d’aya: Tsintsiya ita ce alamar jam’iyyar APC, saboda haka ne magoya bayanta ke nema mata farin jini domin ta ci za’be, musamman ganin had’akar jam’iyyu ta maja ta haifar da had’in kan ‘yan adawa, don samun sauk’i wajen tunkarar jam’iyya mai mulki ta PDP.



    1. Sai mai sallah: Suna ne da magoya bayan jam’iyyar APC (musulmai) ke yabon d’an      takara Muhammadu Buhari, don nuna d’arawa tsakaninsa da abokin hamayyarsa ta          fuskar addini. Akwai ma masu cewa naka sai naka,       ‘kuma hannunka bai ru’bewa ka         yanke shi ka yar’. Su ma ‘yan jam’iyyar PDP suna wasa nasu d’an takara da ‘sai         mai      hitsari tsaye’ ko ‘sai kahiri’ sai ka ji suna cewa ai siyasa ba addini ba ce.


    1.4.2   Ire-iren Kalaman Siyasar Canji Bayan Kafa Gwamnatin APC

    Bayan jam’iyyar APC ta yi nasarar kar’be madahun ikon shugabancin k’asa. Kalaman siyasar canji sun ci gaba da bunk’asa da yad’uwa, musamman a tsakanin magoya baya da ‘yan adawa da ma duk ‘yan k’asa masu sharhi kan al’amurran siyasa. A wannan sashe za a duba irin maganganun da ke bayyana ra’ayoyin jama’a kan tasirin canjin da aka yi, da kuma halin da k’asa ke ciki sakamakonsa. Ga kad’an daga cikin kalaman da aka kalato.

    1. Masu gudu su gudu[x]: Wannan gargad’i ne da aka samo daga wak’ar Dauda Kahutu             Rarara, wanda ke sanar da ‘barayin gwamnati cewa; Buhari ya ci za’be don haka duk        wanda ya san ya yi wata almundahana to, ya ranta cikin na kare kafin janaral ya rutsa da shi. Saboda haka ne ma ya sa ‘yan siyasa da jama’a suka rik’a amfani da wad’annan kalamai, wajen nuna goyon baya ko adawa. Sau da yawa za ka ji ‘yan jam’iyyar APC   na tsokanar abokan hamayyarsu na PDP  da cewa, ‘masu gudu su gudu’ wai in ka san ka yi sata ka gudu. Su ma ‘yan PDP na mayar da martani da cewa ai ‘masu gudu su gudu’ ya shafi kowa har da ‘yan APC, domin Buhari yana fad’a ne da azzalumai masu gurgunta k’asa da ake samu a cikin kowance jam’iyya.

    2. Bincike ake[xi]: Shi ma wannan kalami ya samo asali ne daga wak’ar Dauda Kahutu             Rarara ta kwana d’ari cikin mulkin Buhari. Daga wak’ar ko             amshinta jama’a suka d’auki hannu, inda suke amfani da ita wajen bayyana cewa, Buhari ya fara bin diddigin    abubuwan da suka gudana na rubda ciki da dukiyar k’asa da kuma matsalar cin hanci   da rashawa. Wannan kalami ya zama gama gari tsakanin magoya bayan da masu        adawa. ‘Yan APC kan zolayi ‘yan PDP da cewa, bincike ake yi, musamman ganin        binciken ya fi rutsawa da ‘yan tsohuwar gwamnati. Su kuma ‘yan adawa na dariyar             magoya bayan sabuwar gwamnati da cewa,   bincike ake yi har yanzu ba a gani a k’asa     ba, kuma ai binciken k’aik’ayi ne koma kan mashek’iya. Su ma sauran jama’a kan        rik’a     tunatar da junansu kan cewa, bincike ake yi saboda haka sai a rik’a sara ana duban             bakin   gatari. Kuma wasu mutane na danganta wannan kalami na ‘bincike ake’ da             cewa, komai fa ya tsaya cik sai an gama bincike.

    3. Lema ta yage: Wannan kalami an samo shi ne daga sunan wak’ar da wasu mawak’an Hausa suka yi wa jam’iyyar APC da Buhari. Lema ta yage na nufin an yi nasarar          kar’be mulki daga hannun jam’iyya mai alamar lema, kuma wannan kalami na kai-         komo tsakanin jama’a masu nuna goyon bayansu ga canjin da aka samu mai cike da         tarihi, da kuma nuna ‘barakar da jam’iyyar PDP ta samu.

    4. Buhariyya ko ‘Yar Buhari: Salon mulkin sabon shugaban k’asa na tsuke aljihun             gwamnati. Da rashin sa’ar da aka yi na hauhawar kayan masarufi         sanadiyar fad’uwar     d’anyen man fetur, wanda ya shafi tattalin arzikin k’asa. Saboda wad’annan dalilai, da             wahalar da k’asa ke ciki na rashin kud’i  da yunwar da wasu ke fama da ita, duk sun        ingiza mutane rik’a cewa, ana cikin Buhariyya ko ‘yar Buhari, musamman a harkar    cinikayya ko a sauran al’amurran al’umma na yau da kullun. Wani sashe na jama’a             kan kira Buhariyya da cewa, an d’unke aljihun ragga.

    5. ‘Dan’azumi: Saboda kwatantawar shugaba Buhari ya sa wasu ke yi masa kirari da           ‘Dan’azumi, ba ka ci ba ka bari a ci. Musammam ganin yadda ‘yan Nijeriya suka saba   da bushashar ci-mu-ci.

    6. Baba go slow ko go slow baba[xii]: Wannan lak’abi ne da ake kiran shugaba Buhari,             musamman ‘yan k’asa da suka k’osa ba su ga canjin nan take ba, da ma masu  ra’ayin       cewa, ta la’akari da yanayin da aka tarar da k’asa ciki sai a yi hak’uri, domin idan   dambu ya yi yawa ba ya jin mai. Wannan ne ma ya sa suka bayyana  Buhari da ‘ruwa            masu aiki sannu’, kuma suna ganin wannan salon mulki ne na bin abubuwa daki-daki,   domin gano bakin zare don daidaita al’amurra.

    7. Da tashin bam gwamma tashin dala: Bayan hawan shugaba Buhari ya gaji matsalar             k’ungiyar boko haram, kuma barazanar kai hare-hare ta ragu sosai.             Sai dai an sami             kariyar tattalin arziki, wanda ya haifar da tashin dala fiye da inda aka fito. Saboda             k’orafin ‘yan adawa da wasu ‘yan k’asa game da tashin dala, magoya bayan jam’iyyar    APC suka k’irk’iro kalami mai bayyana cewa, da tashin bam gwamma tashin           dala,[xiii] wato zaman lafiya ya fi zama d’an sarki. Su ma ‘yan kasuwa ba a bar su a       baya ba wajen yayata tashin dala, musamman idan aka yi maganar k’arin kud’in kayan   da suke sayarwa.


    Kammalawa


    Daga wad’annan kalamai an fahimci cewa, ‘yan siyasa kan tallata jam’iyyarsu ko d’an takara, ta hanyar yabo ko taken kirari wad’anda kan yi tasiri a zukatan masu saurare. Wato fad’ar za’ba’b’bun kalmomi masu dad’i ga gwanayensu, wad’anda suka aikata wasu kyawawan abubuwa masu k’ara  bayyana darajarsu na matuk’ar bak’anta wa ‘yan adawa rai, tare da faranta ran  magoya baya da k’ara musu k’warin guiwa. A siyasance duk lokacin da aka ambaci kalmar ‘sai’ to, alama ce ta nuna fifiko da darajar wani a kan wani ko wasu, fifikon kan fito k’arara ta hanyar ambaton abubuwa da yawa da suka bambanta wanda aka kambama da wanda aka nuna an fi ta fuskar manufa, ko ak’ida mai alfanu. Bayan canjin gwamnati an ga yadda harshe ya ba da gudunmawa wajen yad’a manufofin magoya baya da ‘yan adawa a kan lokacin canji da ake ciki, da kuma yadda suke amfani da kalamai daban-daban wajen ba shi fassara gwargwadon fahimta.

     

    https://www.amsoshi.com/2017/11/08/sakkwato-ce-tushen-hausa-ji-narambada-laluben-gudunmuwar-mawaka-kan-asalin-bahaushe-da-harshensa/

     

     

     

     

     

     

     

     

    Manazarta


    Abba, T.  2013. "Coinage And Neologism in Kano Politics" In Yalwa, L.D et al (eds). Studies in      Hausa Language, Literature And Culture. The First Hausa National Conference. Zaria:   Ahmadu Bello University Press Limited.

    Crystal, D. 2008. A Dictionary of Linguistics and Phonetic. Sixth Edition. UK:      Blackwell        Publishing.

     

    Fagge, U. U. 2012. Hausa Language and Linguistics. Zaria: Ahmadu Bello University,     Press Limited.

     

    Farinde, R.O & Ojo, J.O. 2005. Introduction to Sociolinguistics. Ibadan: Lektay    Publishers.

     

    Gee, P. J. 2014. An Introduction to Discourse Analysis Theory and Method. Fourth Edition.         London: Routledge.

     

    Kiyawa, H.A.  2013. "Gudunmawar Harshe a Harkokin Siyasa" In Yalwa, L.D et al (eds).   Studies in Hausa Language, Literature And Culture. The First Hausa National Conference.            Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

    Lyons, J. 1981. Language and Linguistics. United Kingdom: Cambridge University Press.

     

    Muhammad, D. (Ed) 1990. Hausa Metalangauge (K’amus na Ke’ba’b’bun             Kalmomi).       Ibadan: University Press.

     

    Ndimele, O.M. (Ed) 2001. Readings on Language. Port Harcourt. M&J Orbit        Communication Ltd.

     

    Sama’ila, S. 2011. "Language and Politics: A Discourse Analysis of Some Hausa Verbal Expressions in Contemporary Nigerian Politics".     In        Harshe Journal of African      Languages and Cultures. No. 5. Ahmadu Bello University, Zaria.

     

    Sani, S. 1998. "Political Language as a Source of Lexical Expansion: The Case of Hausa."           Unpublished PhD Dissertation, Indiana University.

     

    Southworth, C. F. & Chander, J. D. 1974. Foundations of Linguistics. New York: The Free          Press.

     

    USAID. 2014. Candidate Campaign Manual: A Practical Guide to Conducting Candidate             Campaings in Nigeria. International Republican Institute: Washigton.

     

    Yakasai, S.A. 2012. Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Kaduna: IBM Printers.

     

    Yakasai, M.G. 2013. "Adon Harshe a Fagen Dimokurad’iyya a Kano". In Yalwa, L.D et al (eds). Studies in Hausa Language, Literature And Culture. The First Hausa National Conference. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

    Yahaya, U. 2013. "Gudunmawar Harshe Wajen Inganta Dimokurad’iyya a             Nijeriya" In Yalwa,      L.D et al (eds). Studies in Hausa Language, Literature And Culture. The First Hausa National Conference. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.

    Yule, G. 1985. The Study of Langauge. New York: Cambridge Universty Press.

     

     

    [i] Lyons, J, “Language and Linguistics” Cambridge University Press, United Kingdom, 1981, shafi na 3.

    [ii] Southworth C.F, & Chander, J.D, “Foundations of Linguistics” The Free Press, New York, 1974, shafi na  2.

    [iii] Yakasai, S.A, “Jagoran Ilmin Walwalar Harshe” IBM Printers, Kaduna, 2012, shafi na 1-2.

    [iv] Fagge, U.U, “Hausa Language and Linguistics” Ahmadu Bello University Press Limited, Zaria, 2012, shafi na 1.

    [v] Ndimele O.M, “Readings on Language” M&J Orbit Communication Ltd, Port Harcourt, 2001, shafi na 3.

    [vi] Yule, G, “The Study of Langauge”Cambridge Universty Press, New York, 1985, shafi na 196.

     

    [vii] Gee, P.J, “An Introduction to Discourse Analysis Theory and Method: Forth Edition” Routledge, London, 2014, shafi na 24.

    [viii] Dubi lamba ta 3, shafi na 151-152

    [ix] Yakasai, M.G, “Adon Magana a Fagen Dimokurad’iyya a Kano” In Yelwa, L.D et al (eds), Studies in Hausa Language, Literature And Culture. The First Hausa National Conference, Ahmadu Bello University Press Limited, Zaria, 2013, shafi na 636.

    [x] Tasirin wannan kalami  ya haifar da fim na Hausa, wanda aka rad’a wa suna ‘masu gudu su gudu’.  A cikin shirin jaruman Hausa sun nuna hoton yanayin da Nijeriya ke ciki kafin za’be na bangar siyasa, da yadda ake siyasar kud’i, don a d’are mulki da kuma duk badak’alar da ta faru lokacin za’ben 2015, musamman a babban d’akin tattara k’uri’un za’be na k’asa.

    [xi] A cikin d’angayen wak’arsa ya sanar da cewa, ‘Bincike muke, za a yi maganin ‘barayi, Baba a bincike su sosai, kowa ta rutsa da shi a kwasai, za a yi maganin kiyasai, tsoho kar ka bar macuta.’

    [xii] Akwai kuma, masu kiran shugaban da Yawale mai canji, wato wai sun gaji da jiran gawon shanu, wai an yi canji amma har yanzu ba su fara cin gajiyarsa ba.

    [xiii] An samo wannan kalami ne daga kafar sadarwa ta fezbuk, kuma wad’annan hanyoyi na sadarwar zamani sun taimaka wajen wayar da kan jama’a da kuma yad’a harshe da siyasar canji, musamman lokacin yak’in neman za’be.
    www.amsoshi.com

    1 comment:

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.