Amsoshi

Ibrahim Abdullahi Sarkin SudanSashen Koyar da Harsunan Nijeriya,


Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.


E-main: ibrasskg@gmail.com


Lambar Waya: +2348036153050

Mak’alar da aka gabatar a taron k’ara wa juna sani na k’asa da k’asa a kan


K’alubalen koyar da harsunan Afrika wanda Association des Auters Nigeriens en Langues Nationales (ASAUNIL) ta shirya tare da had’in guiwar Nagerian Indigenous Languages Writers Association (NILWA) a Emir Sultan Venue, Niamey Janhoriyar Nijar daga ranar 19 zuwa 21 ga watan Fabrairu  2014


GABATARWA

Sauyawar da aka samu na al’amurran Hausawa a sakamakon kar’bar addinin musulunci ya daidaita yanayin rayuwarsu ta  fuskokin da dama. Suturar da suka saba sawa ta sauya. Irin abincin da suke ci ya inganta musamman ta fuskar fayyace haram. Mu’amalarsu ta kasuwanci da zamantakewa da fayyace hak’k’ok’in juna duk sun shiga zukatan mutane kuma sun yi tasiri ainun. Baya ga wad’annan kuma hatta da lafuzzan da aka yarda mutum ya furta shi ma addinin na musulunci da al’adar kunya sun k’arfafa shi ta yadda ya zama bak’on abu mutum ya bud’e baki ya yi ashar ko ya furta batsa. Duk wanda ya d’abi’antu da furta ire-iren wad’annan lafuzza sai a d’auke shi mutumin banza ko la’ananne.

 

A irin wannan rayuwa da ake ciki, sai ga shi an wayi gari wasu makad’an Hausa musamman wad’anda suke da birbishin Maguzanci a rayuwarsu sun bijire. Ba su damu su rink’a furta irin wad’annan kalmomi ba duk da kasancewar shi tsohon yayi. Mak’asudin wannan nazari shi ne fito da wannan matsala a fili musamman na irin k’alubalen da ake fuskanta wajen koyar da d’iyan wad’annan wak’ok’i ga d’aliban adabi.

https://www.amsoshi.com/2017/11/04/personification-hausa-proverbs/

2.0       WAIWAYE


Kafin bayyanar addinin musulunci da tasirinsa a rayuwar Hausawa, rayuwa ce da ba ta dogara ga wani tsari mai armashi ba dangane da abin da mutum zai furta. A rayuwa maguzanci, mutum na iya bud’e baki ya fad’i duk abin da ya ga dama muddin dai bai ci fuskar wani ko ya haddasa husuma a tsakanin mutane ba. Babu wani takunkumi wajen yin ashar ko fad’ar kalmomin batsa. Babu wani k’ask’anci ga babba don ya yi batsa ko ashar a gaban yara ko wad’anda ya kamata ya ji kunya. Haka shi ma yaro, kasancewar babba ko wani surukinsa a wuri ba dalili ba ne da zai kasa k’unduma zagi ko ashar ko kalaman batsa ba. Wannan wani babban reshe ne daga abin da aka kira maguzanci wanda kuma ake ganin ya munana rayuwa musamman ta Hausawan da ba musulmi ba (Maguzawa).[i]

 

Abu ne mai sauk’i a kasa bambance Bamaguje da Bahaushe (Musulmi) a wajen mu’amalar yau da kullum in ba lokacin salla ya yi ba. To amma da zarar aka ce kowanensu ya bud’e baki ya yi magana musamman wajen hira ko zance na raha, nan za a fahimci lafuzzan Bamaguje sun bambanta. Za a ji Bamaguje na luguden kalmomin batsa ko ashar ba tare da ya damu ba. Al’adar Maguzawa ta ba su dama ko ma ta k’arfafa ire-iren wad’annan lafuzza musamman idan mun d’auki abin da ke faruwa a wajen d’aurin aurensu a matsayin misali. Maguzawa suna amfani da ire-iren wad’annan lafuzzan wajen d’aura aure.

 

Ni Wane na d’aura auren Wane da Wance.

In ga d’an jar k’aniyar da zai raba.

 

Ni Wane na d’aura auren Wane da Wance

In ga d’an babban bura-uban da zai raba.

 

Ni Wane na d’aura auren Wane da Wance.

Ba d’an kutumar babakeren babban buran-uban

da zai raba wannan auren sai wanda ya kwana

da uwarsa. A nan duniya ba ta da wani miji in ba

Wane ba.”

 

Na d’aura auren nan d’amar.

In ga d’an durin uwar da zai kwance shi.

 

Na d’aura auren Wane da Wance

            Ba d’an jar durin uwar da zai kwance shi.

 

3.0       TANKA’DE DA RAIRAYA


Hak’ik’a wad’annan lafuzza in har an iya ambaton su a muhallin d’aurin aure cikin bainar jama’a, ba za su zama abin zargi ba idan sun fito a zantuttukan yau da kullum. Ga wanda yake musulmin Bahaushe, kuma ya tarbiyantu da ilimi da ladubba na addinin musulunci, haramun ne ya ambaci haka. Tun yara suna k’anana ake hani gare su da yin zagi ko furta kalmomin batsa. A duk lokacin da bakin wani ya kubce ya furta batsa ko ashar to kan masu sauraro yakan yi nauyi. Wani ya ji kamar ya nutse don kunya ko takaici. Idan mai fad’ar maganar da gangan ya yi, to tun daga wannan lokacin ya shiga cikin kundin marasa kunya na wannan al’umar. Za a rink’a kallonsa mutumin banza. Za a fara tsoron gardama da shi, ko ma mu’amala da shi don tsoron kada ya k’unduma wa mutum ashar. Ta fuskar jin kunyar furucin irin wad’annan lafuzza kuma (ga masu kyakkyawar tarbiyya) hatta da lafuzzan Kur’ani da ya yi kama da su ana jin kunya ambata. A wannan nazari an d’auki duk wani abu da za a  furta dangin ashar ko batsa a matsayin maguzanci .

 

4.0       MAGUZANTATTUN ‘DIYAN WAK’OK’IN HAUSA


Duk da kasancewar Hausawa (Musulmi) suna rayuwa a cikin al’umar da ta katange kanta daga munanan lafuzza, sai ga shi wasu makad’an Hausa ba su mayar da wannan abin kunya ba. Kai tsaye sukan bud’e baki amma a cikin wak’a su yi batsa ko ashar ba tare da an zarge su da yin abin assha ba. A wannan fasalin, za a kawo misalan ashar da batsa kamar yadda suke zuwa daga bakunan makad’an don kawai a tabbatar da dugadugan nazarin.

 

 • Ashar


Ashar na nufin muguwar magana ko zagi wadda ta sa’ba wa tarbiyar al’uma. Duk wata kalma da za a bud’e baki a furta da niyyar zagi, to ana kiran shi ashar. Wad’annan kalmomi ke’ba’b’bu ne duk da yake suna iya bambanta daga wuri zuwa wuri. Ga misalin wad’annan kalmomi ko lafuzza a bakin wasu makad’an Hausa.   

 • Mamman Shata a Wak’ar Gagarabad’au:


‘Dan k’undun durin uwa

Shadidi mazinaci

 

 • Gambu Dogo Mai Kalangu


Sai ya yi kwatakyas yah hwad’i zaune

Jab babban bura-ubanga

Sarki ya ji tsoro

Mi arranar yak’in Talakka.

 

 • Gambu Dogo Mai Kalangu


Mai shanun noma kaico kanka

Jab babban bura-ubanga

Ka ji kid’in yawo da zwari

Ana cigiyar banza da yohi

 

 • Umaru Sank’iran Gambu Dogo Mai Kalangu


Dogo ga kyau, ga kyauta, ga ’yab babbab bura’uban sata

 

-               Kassu Zurmi – Wak’ar Nomau Namagarya

Yac ce “Ina hita Maikassuwa,

                             Amma hwa ba da alheri ba,

 Bari ko an hana ni yanzu da rana,

Sai iskan sha biyun dare ya taso,

Sannan za ni kunna yab bura uba

Magarya sannan wada ko d’iyansu wasu ba su hita 

 

Wad’annan ’ya’yan wak’a kad’an kennan daga cikin d’imbin ire-irensu da suke d’auke da zagin da a al’adance ba a so a yi su ko a ji su ko ma a kusanta da mai yin su. Duk iyaye ko malamin da suka d’abi’antu da furta su, to ko shakka babu za a wayi gari yaran da ke kusa su fi shi iya k’unduma su. Idan kuwa a waje yaro ya koyo su, to iyaye sai sun yi da gaske kafin su fita k’wak’walwar yaro.

 

 • Batsa


Batsa na iya kasaancewa duk wata magana ta ‘batanci wadda ke da alak’a da furucin sunayen al’aura na zahiri ko kuma kalaman da suke nuni ga jima’i tsakanin mace da namiji. Akwai da yawa daga cikin makad’an Hausa da sukan yi wa d’iyan wak’ok’in nasu kwalliya da wad’annan kalmomi na batsa. Zai iya kasancewa sun yi haka ne don burge masu sauraro, amma ba don lalurar wak’a ba. To ko dai wane dalili ke gare su na wannan ‘batanci, birbishin maguzanci ne a ji irin wad’annan kalmomi daga mutum mai hankali. Misali:

 • ‘Dan’anace a wak’ar Shago


Na yarda don Gato aka aure,

In don daka ku bar ni in yi abuna

 

 • Mamman Shata – Wak’ar Gagarabadau


Taho nan kwanta ki bubbud’e k’afafu,

Ki bubbud’e k’afafu,

Ki lullumshe idanu

 

 • Sa’adu Bori (d’aya daga wak’ok’insa)


Ashe mata wayau suke mana,

Abin dad’i na can k’asan zani,

Mai hana duri Bura ubanta

 

 • Mamman Shata


In kin je kul ki ba da bado,

Yarinya in kin je kar ki ba da bado

-----------------------------------------

In ka ji kwaramniya d’aki,

Yarinya ta k’i ba da bado.

5.0       MATSALOLIN KOYAR DA MAGUZANTATTUN ‘DIYAN WAK’OK’I


 

Wad’annan ’yan misalai da suka gabata, sun tabbatar da samuwar tsarmin maguzantattun lafuzza a cikin wak’ok’in makad’an Hausa. Wak’ok’i makad’a kuwa suna daga cikin ginshik’an darussan koyarwa a adabin bakan Bahaushe. Idan har za a koyar da adabin musamman na wak’a ba da su ba, to lallai an bar gi’bi. Sannan kuma akwai bukatar a cikin irin wannan darussa a nuna illolinsu da kuma illolin koyar da su musamman don gudun yi wa tarbiyya zagon k’asa. A wannan fasali za a tunkari k’alubalen wad’annan wak’ok’i a azuzuwan adabi.

 

 • Ruguza Tarbiyya


Duk da yake ana cewa, zamani riga ne, sauraro ko kuma nazarin d’iyan wak’ok’in da ke k’umshe  da ashar ko batsa tamkar ruguza tarbiyar da aka yi wa yara ne a gida. A wasu gidajen an tarbiyantu da rashin sauraron irin wad’annan wak’ok’in. Zai iya zama abin sha’awa ga yara musamman wad’anda suka fara tashen balaga, su rink’a jin su. Rera su a cikin wak’a zai fi sauk’in shiga rai fiye da nauyin da za su iya d’auka a cikin zance. idan haka ya samu to an yaye tarbiyar da aka gina na lokaci mai tsawo. Kuma wannan ya zama wata kafa na gur’bata lafuzzan da za a ji yana fitowa a bakunansu musamman idan suna cikin sa’o’insu.

 

 • Zubewar Mutuncin Malami


Daga cikin abin da ya kamata a ce malami ya siffantu da shi musamman wanda ake d’ammahar yara su koya shi ne kyakkyawar lafazi. K’ok’arin koyar da ko kuma bayanin k’umshiyar wad’annan d’iyan wak’ok’in ba k’aramar illa take jawowa ba na kimar malami a idon d’alibi. Ko da ya kasance kayarwa ake yi, a duk lokacin da malami zai saki jiki wajen kawo misalan wad’annan wak’ok’i, za a fara yi masa kallon mara kunya, ko mara mutunci. Ba wani tsawatawa da malam zai yi na furucin ire-iren wad’annan kalmomi idan d’alibi ya zo da su ko da a cikin zance ne.

 

5.3       Zurfafa Bincike

A duk lokacin da aka yi wa d’alibi darasin da yake sha’awa, to kamar an ba shi kafa ne na k’ara zurfafa bincike wajen sanin wannan abu ko da kuwa a lullu’be aka zo da shi. Kada a ji mamakin idan malami ya bayar da misali d’aya na wad’annan d’iyan wak’ok’i, a  mayar masa da goma idan ya yi tambaya. Duk abin da yake da muni ko al’ada ta yi hani da shi ya fi saurin shiga zuciya da haddacewa. Samun tarin wad’annan lafuzza a zukatan matasa zai iya gurbata tunani na tabbatar da fad’ar mawak’i.

 NA’DEWA

Kalmomin ashar ko batsa in ba Bamaguje ba, ba Bahaushen da al’ada ta yaye wa lullu’bin yinsa kai tsaye a bainar jama’a. Duk da yake tun fil azal ana samun tsarmin wad’annan d’iyan wak’ok’i a gargajiyance kamar a cikin wak’ok’in gad’a da na da’be, amma fitowarsu a irin wannan muhalli, ba k’ank’anin abin tashin hankali ba ne. A can da a inda aka yi su a nan ake barinsu (a dandali ko wajen aikin da’be). Shigowar irin wad’annan wak’ok’i a muhallin da kowa zai iya cin karo da su, wata matsala ce da wannan mak’alar ta gano, kuma ta fahimci illarta ta ruguza wani sashe na tarbiyya a al’uma. Wak’ok’in da ke k’umshe da ashar da Batsa hak’ik’a an riga an yi su kuma sun shiga jama’a. To sai dai har yanzu akwai wata ’yar dama na sanin yadda za a yi nazarin su da bayanin su ga d’aliban adabi. Idan har malamai da d’alibai za su rik’a sara suna duban bakin gatari, to talala’biyar da ta ja makad’an suka rera su (wak’ok’in) ba za ta kayar da su ba. Hak’ik’a wannan nazarin tamkar hannunka-mai-sanda ne ga tunanin ke’bo  d’alibai da malamai daga komawa ga rayuwa ta maguzanci.

 

 • MANAZARTA


 

Abdullahi, I. S. S. 2008, ”Jiya Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar       Maguzawana Aure da Haihuwa da Mutuwa.” Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa Culture) Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

 

Abdullahi, I. S. S. 2008. “Fitattun ‘Dabi’un Maguzawa” Maiduguri Journal of Linguistics

and Literary Studies (MAJOLLS) Vol. X Department of Languages and Linguistics, University of Maiduguri.

 

Abdulkadir, M. F. 1988: “Culture and Linguistic Behaviour: A Sementic Study of Hausa

Insult words. Unpublished” M. A Dissertation, Dept. of English A. B. U. Zaria

 

Douglas, M. 1966: Purity and Danger: An Analysis of concepts of Pollution and Taboo.

London – Routledge and Kegan Paul.

 

‘Dangambo, A. 1984, Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar

Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company LTD

 

Garba, A. 1982, “Mammam Shata Da Wak’ok’insa.” Kundin Digiri na d’aya (B. A. Hausa)

Jami’ar Bayero, Kano

 

Gusau, S. M. 2008, Wak’ok’in Baka a K’asar Hausa Yanaye-Yanayensu da Sigoginsu

Kano:  Benchmark Publishing Limited

 

Gusau, S. M. 2009, Diwanin Wak’ok’in Baka Za’ba’b’bun Matanoni na Wak’ok’in Baka na

Hausa Kano: Century Reseach and Punlishing Limited

 

Usman, B. B. 1990, “A Sociolinguistic Study of Tabboos in Hausa” M. A. Hausa Thesis,

Bayero University, Kano

 

[i] Maguzanci na nufin halaye da ]abi’un Maguzawa wa]anda suke da ala}a da rayuwarsu ta gargajiya

kuma ba su da wani birbishi na addinin Musulunci. Don }arin bayani, dubi Abdullahi, I. S. S. (2008)”Jiya

Ba Yau Ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawana Aure da Haihuwa da Mutuwa.”

Kundin Digiri na Uku (Ph.D Hausa Culture) Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.