Amsoshi

DagaDr. Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan


Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,


Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.


e-mail: ibrasskg@gmail.com


Tel: 0803 6153 050


 


 

 GABATARWA

 

Daga cikin fa’idojin da ake samu na zaman mutane a wuri d’aya kuma su kasance al’uma d’aya shi ne samar wa kansu wad’ansu hanyoyi na rayuwa wad’anda suka aminta da shi a matsayin abin alfanu a gare su. Irin wannan tunani ne kan sa d’aid’aikun hanyoyin gudanar da rayuwa sukan bambanta tsakanin mutane. Abin da wasu suke d’auka da muhimmanci, ba zai kar’bu ba a wata al’umar, ba don rashin muhimmancisa ba, sai don kawai tunaninsu bai hango can ba. Gane fa’idar al’adar da al’uma ta ke’banta da ita da kuma rashin fa’idar ta ya dogara ne ga yadda aka sami damar baza ta a faifan nazari.

 

Mak’asudin wannan nazari, shi ne duban yadda Maguzawa suke gudanar da wata al’ada ta bayyana shigar ciki ga amarya. Maguzawa suna ba wannan al’ada muhimmanci ne saboda la’akari da irin kunyar da ke tattare da matakan samun cikin farko ga amarya. Wannan al’ada tamkar wata hanya ce ta yaye yanar kunya da take lullu’be bayyana wa amarya da sauran jama’a cewa, ta sami shigar ciki.  Haka kuma a tasu fahimtar, shigar cikin wani muhimmin mataki ne da ke nuna albarkar aure. Wannan ya sa aka tanadar masa wad’ansu al’adu na musamman a matsayin wani mataki a al’adar haihuwa a rayuwar tasu. A wannan nazari, za a kalli yadda Maguzawa suke aiwatar da wannan al’ada ta karan k’irji da kuma hikimomin da ke tattare da ita. An ke’be wannan nazari ne ga mutanen da ake Maguzawa da tunanin  cewa su ne Hausawa asali wad’anda akasarin al’adun Hausawa na gargajiya suka samo asali daga garesu.[i]

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/1267/

2.0       FASHIN BAK’I


Wannan fasali zai yi k’ok’arin yin sharhi ne a kan abin da ake kira Karan K’irji. Ga dukkan alamu dai duk kalmomin biyu Hausawa ne. Wato, ba aro su aka yi daga wasu harsunan ba. A nahawun Hausa, kara ko kare ko karewa kalma ce ta aikatau mai nufin killace ko yin katanga don asirta wani abu (K’amusun Hausa 2006:234). Kalmar k’irji kuwa suna ne na wani sashen jikin abu mai rai (musamman mutum) wanda ya yi iyaka da wuya ta sama da kuma ciki ta k’asa. Wannan sashe ne muhallin nono, kuma a nan ne k’asusuwan awazu/hak’ark’ari suka had’u. Had’a wad’annan kalmomi biyu ya nuna cewa, bisa ma’ana, sirrantawa ko katangewa ake d’ammahar a yi wa sashen da ake kira k’irji. Idan kuwa haka ne, to tambayoyin da za su tuzgo a nan su ne: A wannan al’ada, k’irjin wa ake karewa? Me ya sa ake so a kare k’irjin ba wani sashe na jiki ba? Wad’anne hikimomi ke tattare da wannan al’ada?

 

A yunk’urin lalubo bayanan da za su amsa wad’annan tambayoyin an fahimci cewa, jinsin mata na Maguzawa ake aiwatar wa wannan al’ada. Haka kuma ba a kan yi shi sai ga matar aure. Ita kuma matar auren, dole ta kasance amarya ce, ko a ce yarinyar da ta yi auren farko kuma ba ta ta’ba haihuwa ba. Har ila yau, ba a gudanar da wannan al’ada sai an yi la’akari da alamomin shigar cikin ga amarya.

 

Kafin matan gida (’yan’uwan ango da iyayensa) su fara zura ido don ganin alamomin samun juna biyu ga amarya, sukan so su san shin an ma fara saduwar aure tsakanin ango da amarya? Abu ne mawuyaci Maguzawa su yarda su bayyana saduwa a tsakanin ma’aurata. Al’adar kunya da hidimomin da ake gudanarwa da rana da tsarin muhallin da ake zaune, ba su ba da damar ango ya ke’banta da amarya da rana tsaka ba. Ma’aurata sukan yi amfani da damar lokacin kwanciya barci ne da dare kawai domin su d’ebe sha’awa a tsakaninsu. Sukan ji kunya matuk’a idan har suka bari wani ya riske su a cikin wannan yanayin. Haka su ma mutanen gida sukan nesanta da muhallin ango da amarya musamman a lokacin da ake d’ammahar su iya amfani da shi don d’ebe Sha’awa.

 

Akan sami tabbacin lallai ango ya kusanci amarya ne ta hanyar la’akari da sauyawar yanayin tafiyarta idan gari ya waye. Duk yadda amarya ta kai ga juriya, tsofaffi daga cikin matan sukan fahimci alamomin jin rauni a gaban mace musamman idan yarinya shataf aka auro. Wannan kan sa wata tsohuwa ta kusance ta, ta farsa mata gabanta da ruwan d’umi. Haka dai za a ta yi sannu a hankali har ta saba. Tun daga wannan lokacin ne manyan mata a gidan za su ta k’ok’arin kula da alamomin da suke sa ran su gani na sakamakon wad’annan saduwar.

 

3.0       ALAMOMIN SHIGAR CIKI


Yanayin tsarin jikin Maguzawa bai bambanta da na sauran al’umomi na duniya ba. Wannan ya sa ba wasu alamomi na daban Maguzawan suka ke’banta da su a matsayin alamomin shigar ciki ba. To sai dai fasahar kowace irin al’uma dangane da kowane lamari yana iya bambanta. A nasu tunanin, akwai wasu ’yan sauye-sauye da kuma halaye ko d’abi’u da sukan yi la’akari da su idan amarya ta sami shigar ciki. Wad’annan alamomi sun fi fitowa a fili ga macen da ba ta saba ba. Ita wadda ta saba, suna ganin tana iya ‘boye wasu lamurra ta yadda za a kasa tsinkayarsu kai tsaye.

 

Akan gane amarya ta sami shigar ciki ne idan aka ga ta faye yawan kukan ciwon ciki da zubar da yawu (miyau) da amai. Ga wadda ba ta saba ba, za ta shiga cikin damuwa da tunanin ko wani rashin lafiya ne. Sauran mata da ke lura da ita musamman tsofaffi, za su shiga murna  suna cewa, “lallai Wance ta sami shigar ciki.” Tabbacin haka yakan k’ara bayyana ne idan an lura da tana sauya kamanni, tana yin haske kuma tana k’ara k’iba. Haka ma za a ga ta fara za’ben abinci. Wato ta ce ba ta son wannan, ko ta fi son abu kaza, ko ba ta son jin warin abu kaza da dai sauransu. Wata alama kuma da Maguzawa ke la’akari da ita wajen gane mace ta sami shigar ciki ita ce, idan an ga kan nononta ya yi bak’i. Wannan abu ne mai sauk’i kowa ya lura da shi domin a kowane lokaci amarya da ma sauran matan gidan k’irazansu a bud’e suke. Suna d’aura zani ne a kwankwaso kawai. Duk wata alama da ake son gani a nonon mace musamman amarya ana iya lura da ita ba tare da an ta ’yan dabaru ba.

 

Ga matar da ba ta saba haihuwa ba, ‘batan wata, wato rashin ganin jinin al’ada a lokacin da ta saba gani ita ce alamar farko. Sauran jama’a ba za su lura cewa, ba ta ga jinin wata ba, saboda ba wani tanadi na musamman da al’adar  ta yi da za a gane ana al’ada kamar yadda mata Musulmi ke barin yin salla. Wasu amaren sukan gaya wa matan da suke kusa da su cewa, ba su ga jini  wannan watan ba. Su kuma sukan gargad’e su da kada su gaya wa kowa saboda abin kunya ne mace ta fito fili, ta bari a gane ba ta ga wata ba.

 


  • DABARUN KARAN K’IRJI
Bayan mutanen gida sun sami tabbacin amarya ta sami juna biyu, sai a fara shiryen-shiryen aiwatar da wannan al’ada ta Karan k’irji amma cikin sirri, ba tare da amaryar ta sani ba. Bambancin da ake samu a tsakanin muhallin Maguzawa daban-daban ya samar da dabarun da suka sa’ba wa juna na yadda ake aiwatar da ainihin wannan al’adar. Ga hud’u daga cikinsu.

 

4.1       ‘Daura Sabon Zani a Rufe K’irji


Idan alamomin da aka yi la’akari da su sun bayyanar da shigar ciki, matan gidan za su za’bi rana ta musamman da za a yi mata karan k’irji. Kafin wannan ranar, iyayen ango mata, za su tanadi sabon zani su ajiye. A ranar da za a yi karar k’irjin, za a shirya da d’aya daga cikin matan da ke da dangantaka da gidan kamar matar wan miji, ko wata k’anwar uban miji. Ita za a mik’a wa wannan zanin, ta yi ta kiwon hankalin amarya, tana cikin gudanar da lamurranta na gida, sai ta d’auko zanin ta zo ta bayanta ta d’aura mata a k’iji, ta fufe mata nono. Da amarya ta ga haka, za ta ji kunya ta fahimci an gane ta sami shigar ciki. Za ta rufe fuskarta da tafin hannuwanta, ta gudu zuwa d’akinta tana kuka.

 

Bayan wani d’an lokaci, sai a sami wad’ansu matan su shiga d’akin su rarrashe ta, su ba ta hak’uri. Tun daga wannan lokacin zanin zai kasance d’aure a k’irjinta. Ko da ta sake wani zanin, dole ta d’aura shi ya rufe mata nono har lokacin da ta haihu. Duk wanda ya shigo gidan ya ga k’irjinta a rufe zai fahimci an yi mata wannan al’adar ta karan k’irji, wanda ke nuna ta sami shigar ciki. Wannan zai sa a yi ta taya ta murna, ana mata fatar a sauke lafiya. Amarya za ta kasance cikin takunkumin sakin jiki a gidan har na kimanin kwana uku. Daga baya kuma ta fara gudanar da lamurra kamar yadda ta saba.

 


  • ‘Dad’d’aki
‘Dad’d’aki wani suna ne da kuma dabara da wasu Maguzawan suke amfani da ita a matsayin karan k’irji.[ii] A tasu al’adar, bayan an tabbatar da shigar ciki ga amarya, za a tanadi wani zani a ajiye. Za a had’a kai da wata tsohuwa, a ba ta zanin ta shammaci amarya ta d’aura mata shi a k’irji. Amarya na ganin an d’aura mata wannan zanin za ta gudu ta shige d’aki tana jin kunya. Haka dai za ta ci gaba da rufe k’irjin har sai ta haihu. Hikimar sa tsohuwa ta aiwatar da wannan al’adar yana da nasaba da tunanin kada kunyar da ke tsakaninta da matan gidan ya kau.

 


  • Amfani Da ‘Danyen Man Shanu
A maimakon zanin da ake d’aura wa amarya a k’irji, Maguzawan Gidan Gwarzo a k’asar Sayaya ta k’aramar hukumar Matazu cikin jihar Katsina d’anyen man shanu suke amfani da shi. Idan iyayen ango (mata) suka gama lura da bayyanar alamomin shigar ciki, za su tanadi d’anyen man shanu a asirce su ajiye. Za a sa rana, a shirya da wani k’anin angon ko taubashinsa wanda shi ake son ya aiwatar da wannan al’adar.

 

Wannan k’anin angon zai bari sai amarya ta saki jiki, ya lakato man shanun nan da hannunsa ya shafa mata a kan nonnanta. Da yin haka zai yi ta kansa domin za ta bi shi da duka. Duk abin da ta samu tana iya kwad’a masa cikin hushi. Daga nan sai ta shiga d’akinta ta d’auki wasu ‘yan kaya nata ta bar gidan da sunan an yi mata laifi ta yi yaji. A irin wannan yajin, ba ta komawa gidan iyayenta wai don kunya da gudun kada a ji sauk’in gane inda ta tafi a bi ta. Tana iya zuwa wurin wata ’yar’uwarta da ke aure a wani k’auyen na daban, ko wurin wasu dangin uwarta a wani wuri can da ba a ta’ba sa ran za ta tafi. A al’adance, shi wannan k’anin mijin da ya shafa mata man shanu a nono zai tafi biko. Idan ya gano inda take, zai ce ya biyo Wance. Mutanen gidan za su ce, ai matarku ce. Sai a yi mata magana, a rarrashe ta, ta shirya ta bi shi. Haka za su kamo hanya tare suna hira, ana ba’a irin wadda ke tsakanin k’anin miji da matar wa. Idan an kusa kawowa gida sai ta d’aure fuska kamar ba tare da shi suke ba, har su iso gida. Tun daga wannan lokacin ita ma za ta rink’a d’aura zani a k’irjinta har lokacin da ta haihu. Tunanin wad’annan Maguzawan dangane da shafa mata man shanu a nono shi ne a sanar da ita cewa, lokaci ya yi da al’ada ta tanada ta fara rufe su, kuma abokin wasa kad’ai zai iya yi mata wannan isharar a zauna lafiya.

 

4.4       Lullu’ba Zani A Kai


A al’adar Maguzawan Kaibaki ta k’asar Fago a Jihar Katsina, idan an ga alamar shigar cikin za a aika wata mata ta fad’o wa iyayen amarya a asirce. Su kuma bayan wani lokaci sai su d’inko wani farin zani su bayar a kawo. Ba za a bari ta san an kawo wannan zani ba. Sai an ga alamar cikin ya kai wata bakwai, za a sami wata rana a shammace ta tana zaune a d’auko wannan zanin a rufa mata. Sai ta fara kuka don kunya. Za ta shige d’akinta ta k’i fita har kwana uku saboda kunya. Bayan kwana ukun za ta fara fitowa tana d’aure da wannan zanin a k’irjinta. Ba za ta yi wa kowa magana ba sai a hankali ta fara sakin jiki kamar dai yadda ta yi a lokacin da take amarya.

 

5.0       DADDAGE


Karan k’irji shi ne abu na farko da yake bambanta matakan rayuwar Maguzawa. Idan aka d’auki aure a matsayin mataki na farko, to da wannan al’ada ake shiga mataki na biyu, wato haihuwa. Amarya tana cikin wani yanayi na amarci a gidan miji za a yi amfani da wannan al’adar a nuna mata ta shiga mataki na biyu na rayuwa (haihuwa). Karan k’irji tamkar wani mabud’i ne na shiga al’adun haihuwa. Wannan fasali zai kalli hikimomin da ke k’unshe a cikin wannan al’ada ta karan k’irji.

 

Al’adar ta karan k’irji wata hanya ce ta sanar da jama’a da ’yan’uwan amarya da na ango cewa, an sami shigar ciki. Ko da ba a gudanar da shi a gaban mutane ba, da zarar an gan ta da zani a d’aure a k’irji, to an fahimci cewa lallai ta sami ciki. Wannan sak’o yakan kwantar da hankalin duk wanda yake da dangantaka da auren, domin an sami albarkar da kowane aure yake so. Ta amfani da wannan sak’on ne za a fara duk shirye-shiryen da suka dace masu alak’a da haihuwa. Duk mai hakki zai fara tunanin hanyoyin sauke abin da ya rataya a wuyansa ta la’akari da wannan ishara da aka nuna masa.

 

A al’umar da ake ba haihuwa muhimmanci, kwanciyar hankalin kowane ango ne ya san ya auro matar da za ta haifar masa ’ya’ya. Sakamakon farko ga Maguzawa na d’awainiyar aure shi ne su ga mace ta sami shigar ciki. Wannan sak’on na al’adar karan k’irji abin farin ciki ne ga miji da kuma hannunka mai sanda na k’ok’orin yin tanadin abin da ya rataya a wuyansa. Haka su ma iyayen ma’auratan, wannan al’adar ke tabbatar musu da cewa, ’ya’yan da suka had’a aure, lafiya lau suke ta fuskar yad’a zuri’a.

 

Haka kuma wannan al’adar ita ke ba amarya damar dangin miji su d’auke mata hidimomin gida da al’ada ta rataya mata don renon cikin da tabbatar da nata lafiyar. Idan da za a bar yanayin nata a ‘boye, to za a sa ta cikin k’uncin fama da laulayin ciki da kuma aikace-aikacen gida da na gona har sai cikin ya bayyana.

 

Ganin irin kunyar da ke tattare da bayyana abin da ke faruwa tsakanin ma’aurata kafin a ce ciki ya shiga, abu ne mawuyaci a ce mace ta iya shaida wa ’yan’uwanta ga halin da take ciki. Wannan al’adar ta karan k’irji, ita ta yaye wannan yanar. A ‘bangaren ’yan kallon kuma, shi zai ba da damar mutane su yi ta tofa albarka da fatar alheri na abin da suka gani na k’aruwa. Maguzawa suna sane da fa’idojin da ke tattare da tofa yawun albarka daga mutane a kan abin alheri. Haka kuma sukan guji yin abin da mutane za su ta tofa yawun assha.

 

Al’adar karan k’irji ga Maguzawa wata dama ce ga amarya ta saki jiki ta tambayi duk abin da ya dace mai alak’a da haihuwa. Idan da an bar abin a duk’unk’une, to kunya za ta yi mata takunkumin kasa bayyana wa mutanen da ke kusa da ita halin da take ciki na damuwa, ko rashin lafiya ko kuma sanin makamar wasu sauye-sauye da ba ta saba gani ba. Al’adar karan k’irjin da aka riga aka gudanar ya bayyana wa jama’a halin da take ciki, ba sauran abin ‘boyewa. Wannan zai ba ta damar samun shawarwari da magunguna da fahimtar ladubban da al’ada ta tanada a kan kulawa da kanta da abin da take d’auke da shi.

 

A wannan al’ada ta karan k’irji, nonon mace shi ne muhimmin abin da ake rufewa daga ganin mutane. A al’adance, cikar nono tana da alak’a da shigar ciki. Haka kuma nono yana daga cikin abin da ke saurin jan hankali da ban sha’awa da motsa kwad’ayi ga wanda ya gani. Wannan al’ada ta rufe nonon mace a lokacin da aka fahimci ta sami ciki, wata kariya ce daga idanun miyagu. Maguzawa sun aminta da cewa, kwad’ayin maita yana iya matsawa idan an lura da cikar k’irjin mace. Barin shi a bud’e zai iya jefa ta cikin had’ari. Ko ba kamai an nuna cewa, mayu suna sha’awar mace mai ciki ballantana sun gan ta a tu’be.

 

Al’adar karan k’irji, wata dama ce ta k’arfafa wasannin barkwanci tsakanin amarya da dangin miji wanda hakan kan k’ara dank’on zumunci. Taubasan ango da k’anninsa maza da mata za su sami kwarjinin yin ba’a da wasanin raha a tsakaninsu da amarya. Ita kuma a nata ‘bangaren, shigar ciki da tabbatar da shi ta hanyar wannan al’adar yakan samar mata da kar’buwa ga dangin miji musamman wad’anda tun farko suke da adawa ga k’ulla auren.

 

6.0       NA’DEWA


Wannan nazarin ya fito da al’adar karan k’irji a fili musammasn ga wad’anda ba su san shi ba. Kamar yadda nazarin ya nuna, al’ada ce ta rufe k’irjin amaryar da aka ga alamar ta sami shigar ciki. Wannan al’ada kasancewarta matakin farko na al’adun haihuwar Maguzawa, sak’o ne ga amarya da sauran jama’a cewa, aure ya yi albarka, irin da aka shuka ya tsiro. Duk da yake wannan al’ada ba ta sami wata kafa a rayuwar Hausawa (musulmi) ba, fa’idojinta suna da yawan da ke tabbatar da Maguzawa mutane ne masu tsararren rayuwa mai la’akari da kare mutunci da ba kowa hakkinsa a cikin al’uma.

 

7.0       MANAZARTAAdamu, M.  (1976), “The Spread of Hausa Culture in West Africa 1700 – 1900” Savanna No 5 Vol. 1, A  Journal of the Environmental and Social Sciences.  Published at  Ahmadu Bello University, Zaria.

 

Akodu, A. (2001), Arts and Crafts of the Maguzawa and some Educational Implications. Gaskiya Corporation Limited. Zaria – Nigeria.

 

Alhassan, H. da Sauransu (1982), Zaman Hausawa

 

Charanchi, R. (1999), Katsina Dakin Kara: Tarihin Katsina Da Garuruwanta, Northern Nigerian Publishing Company Limited, Zariya.

 

Fletcher, D. C. (1929) “The Kai-na-Fara.” Extract from Re-assessment  Report on ’Yand’aka District, Katsina Emirate, Zaria Province. M. P. No K. 8833 National Archives and Monuments, Kaduna.

 

Greenberg, J. (1946) The Influence of Islam on a Sudanese Religion: Monographs of the American Ethnological Society. J. J. Augustin Publisher, New York.

 

Ibrahim, M. S. (1982), “Dangantakar Al’adu da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa”, Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Bayero, Kano.

 

Kado, A.A. (1987), “Kainafara Arnan Birchi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Sakkwato.

 

Krusius, P. (1915), “Maguzawa” Archiu, Anthropologies, NF Vol. XIV.

 

Lawal, A.T. (1986), “Al’adun Hausawa Jiya da Yau”, Kundin Digirin farko Jami’ar Sakkwato.

 

Madauci  I. da  wasu (1968) Hausa  Customs Northern Nigerian Publishing Company, Zaria.

 

Mairukubta, H. (1999) “Jego da Reno a K’asar Hausa: Tsokaci Kan Hausawan Kabi” Kundin digiri na  biyu, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

 

Safana, Y.B. (2001), “Maguzawan Lezumawa (Babban Kada) Gundumar Safana”, Kundin Digiri na farko, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

 

Sufi, A. H. (2001) “Hanyar Kiran Maguzawa Zuwa Ga Addinin Musulunci.” Mak’alar  da aka gabatar  a  taron Kwamitin Yad’a Addinin Musulunci na Jihar  Kano.

 

Travitt, L.  (1973) “Attitudes And Customs In Childbirth Amongst Hausa Women In Zaria  City,”  Savanna No 2 Vol. 2, A  Journal of the Environmental and Social Sciences Published at  Ahmadu Bello University, Zaria.

 

Tremearne, A. J.  N. (1913) Hausa Superstitions And Customs.  John Bale, Sons and Danielsson,  LTD Oxford.

 

Umar, M. B. (1980), Al’adun Haihuwa A K’asar Hausa. Hausa Publications Centre Zaria.

 

Yusuf, A. B. (1986), “Wasannin Maguzawan K’asar Katsina”, Kundin Digirin farko, Jami’ar Sakkwato.

[i] Maguzawa su ne Hausawan da ba Musulmi ba, masu gudanar da rayuwarsu ta hanyar bin tanadin da aka yi a al’adunsu da addininsu na gargajiya.

 

[ii] Maguzawan }auyen Gidan Bakwai a }asar Faskari cikin jihar Katsina su ke kiran wannan al’ada da [a]]aki